window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

KAI TSAYE, Darajar Yamal ta kai £340m ga duk wadda za ta saye shi

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labaran wasanni a faɗin duniya na ranakun 31 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Real Madrid ce mafi daraja tsakanin ƙungiyoyin tamaula a duniya

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Real Madrid mai buga La Liga ita ce kan gaba mafi daraja tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon kafa a duniya karo na huɗu a jere in ji mujallar Forbes.

    Real ce ta farko da ta samu sama da dala biliyan ɗaya a kakar tamaula, wadda ta ce ta samu ƙudin shiga da ya kai $1.13 billion a 2023-24 kamar yadda mujallar ta wallafa a shafinta ranar Juma'a.

    Manchester United ce ta uku mai $6.6 billion bayan samun ƙudin shiga $834 million a 2023-24 duk da kalubalen da ta fuskanta, wadda ta kare a mataki na takwas da lashe FA Cup.

    Barcelona ce ta uku mai $5.65 billion, sai Liverpool ta huɗu da kuma Manchester City ta biyar.

    Fobes ta bayyana ƙungiyoyin Premier League shida daga 10 farko har da Arsenal da Tottenham da Chelsea da Bayern Munich da kuma Paris St Germain.

  2. Monaco

    Asalin hoton, Monaco

  3. Djokovic zai buga French Open a lokacin da ake Champions League wasan karshe

    Novak Djokovic

    Asalin hoton, Getty Images

    Novak Djokovic, wanda ke fatan lashe Grand Slam na 25 jimilla, zai buga wasan zagayen gaba a French League a lokacin da ake wasan karshe tsakanin Paris St Germain da Inter Milan a Champions League.

    Haka ma wasu ƴan wasa mata daga Amurka za su yi wasanninsu ranar ta Asabar daga ciki har da Coco Gauff da Jessica Pegula da Madison Keys da kuma Sofia Kenin masu fatan kai wa zagayen ƴan 16 har da Hailey Baptiste.

    Djokovic zai fafata da mai shekara 23, Filip Misolic a daren Asabar a filin Philippe Chatrier.

    Paris Saint-Germain na fatan lashe Champions League a karon farko, inda za ta fuskanci Inter mai uku a tarihi a fafatawar da za su yi a Jamus.

  4. Man United ce ta biyu mafi daraja duk da kalubalen da take fuskanta

    Man United

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ce ta biyu mafi daraja tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon kafa a duniya, duk da kalubalen da ta fuskanta, Yayin da Real Madrid ce ta farko.

    Mujallar Forbes ta bayyana United mai darajar $6.6bn (£4.9bn), wadda ta samu ƙuɗin shiga $834m (£620m) a kakar 2023-24.

    Kamar yadda Forbes ta ayyana, United ta samu karin kaso 1 cikin 100 duk da kammala kakar 2023/24 a mataki na takwas a teburin Premier League da kasa samun gurbin shiga Champions League.

    Sai dai United ta ɗauki FA Cup a kakar, amma ta kare a mataki na 15 a teburin Premier League a kakar da aka kammala, sannan Tottenham ta doke ta 1-0 ta lashe Europa League a Sifaniya.

    Kenan ƙungiyar da Ruben Amorim ke jan ragama, ba za ta shiga gasar zakarun Turai ba a baɗi.

    Duk da kasa taka rawar gani da bashin £1bn da faɗuwa ribar kasuwanci £113.2m a kakar 2023-24, har yanzu United tana sawun gaba tsakanin ƙungiyoyin dake da daraja a fannin wasanni.

  5. NFF

    Asalin hoton, Super Eagles

  6. Heitinga ya kusan zama kociyan Ajax

    Heitinga

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta tabbatar da cewar John Heitinga ya bar Anfield, domin ya je ya karɓi aikin horar da Ajax.

    Mai shekara 41 tsohon ɗan wasan Ajax da Everton wanda mataimaki ne ga kociyan Liverpool, Arne Slot, ya bar wadda ta lashe kofin Premier League bayan kaka daya a Anfield.

    Tsohon ɗan wasan tawagar Netherlands ya fara taka leda daga makarantar Ajax, zai maye gurbin sco Farioli wanda ya ɓarar da maki tara ya kasa lashe Eredivise kofin da abokiyar hamayya PSV Eindhoven ta ɗauka.

    Wannan labarin na zuwa ne bayan da Pep Lijnders, wanda ya yi mataimaki karkashin Jurgen Klopp ya amince zai koma aiki tare da Pep Guardiola a Manchester City.

  7. PSG

    Asalin hoton, PSG twitter

  8. Fraser da Reguilon za su bar Tottenham

    Tottenham

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta sanar cewar Fraser Forster da Sergio Reguilon suna daga cikin ƴan wasan da za su bar ƙungiyar.

    Reguilon, wanda ya koma Tottenham a 2020, ya kasa taka rawar gani da ta kai an bayar da shi aro ga Atletico Madrid da Manchester United da kuma Brentford - daga nan ya buga wa Tottenham karawa huɗu a Premier League a kakar da ta kare.

    Haka kuma mai tsare raga, Alfie Whiteman da Forster za su bar Tottenham, yayin da Timo Werner zai koma RB Leipzig, bayan wasannin aro da ya yi a Tottenham.

    Sai dai Tottenham ba ta sanar da sunan Ben Davies ba daga waɗanda ta ce za ta rabu da su ba.

  9. Sinner ya kai zagaye na huɗu a French Open

    Sinner

    Asalin hoton, Getty Images

    Jannik Sinner ya doke Jiri Lehecka ranar Asabar a gasar a Roland Garros ya kai zagaye na huɗu a wasannin da ake yi a birnin Paris.

    Ɗan kasar Italiya ya kai zagayen gaba ne da cin 6-0, 6-1, 6-2.

    Kenan mai shekara 23, zai buga karawar gaba da Andrey Rublev a fafatawar zagayen ƴan 16.

  10. Tsohon damben gargaji: Shagon Mada ya buge Kanin Emi

    Bayanan bidiyo, Damben da Shagon Mada ya buge Shamsu Kanin Emi
  11. West Brom za ta ɗauki Ryan Mason tsohon kociyan Tottenham

    Mason

    Asalin hoton, Getty Images

    West Bromwich Albion tana tattaunawa da tsohon kociyan Tottenham, Ryan Mason.

    Wasu majiya da suka sanar da BBC sun ce Mason, wanda yake aiki tare da Ange Postecoglou a Tottenham, shi ne kan gaba da ƙungiyar ke son ɗauka domin maye gurbin Tony Mowbray, wanda ta kora a cikin watan Afirilu.

    Yarjejeniyar Mason a Tottenham za ta kare a karshen watan Yuni.

  12. Wa zai lashe Champions League: PSG ko Inter

    Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Asabar za a buga wasan karshe a Champions League tsakanin Paris St Geramin da Inter Milan a Allianz Arena a Jamus.

    Kungiyar Italiya za ta yi karawar karshe a gasar zakarun Turai ta Champions League ko European Cup karo na bakwai, bayan da take da uku a hannu.

    Rabon da ta kai zagayen karshe tun 2023, inda Manchester City ta lashe kofin.

    Ita kuwa ta Faransa za ta kara a wasan karshe karo na biyu, bayan da Bayern Munich ta lashe kofin a kanta a 2020.

    Idan har PSG ta yi nasara za ta zama ta biyu a Faransa mai Champions League bayan Olympic Marseille

    Haka kuma PSG na fatan lamusa kofi uku a jere a karon farko, bayan da ta lashe Ligue 1 da Coupe de a kakar da ta kare ta bana.

    Kungiyar Faransa na sa ran ɗaukar kofin nan, bayan da Lionel Messi da Neymar da Kylian Mbappe wanda ya koma Real Madrid suka kasa lashe mata shi.

    Gasar Champions League ce ta rage a bana, bayan da Tottenham ta lashe Euopa League da kuma Chelsea da ta dauki Conference League ranar Laraba – daga nan a shiga Club World Cup a watan gobe

  13. Andreeva ta kai zagayen ƴan 16 a French Open

    Mirra Andreeva

    Asalin hoton, Getty Images

    Matashiya ƴar kasar Rasha, Mirra Andreeva ta kai zagayen ƴan 16 a gasar ƙwallon tennis ta French Open ranar Asabar, bayan da ta yi waje da Yulia Putintseva.

    Mai shekara 18 da haihuwa ta kai zagayen gaba ne da cin 6-3, 6-1 a cikin minti 78.

    Za ta buga wasan gaba ne da Daria Kasatkina, domin neman gurbin kwata fainals.

    Kasatkina, mai shekara 28, tana buga gasar ta Roland Garros karo na 10, ta kuma kai daf da karshe a 2022.

    Andreeva na fatan yin abin kirki a wasannin Roland Garros, koda yake har yanzu fitatciyar ƴar wasa Sabalenka da mai rike da kofin, Iga Swiatek suna cikin gasar.

  14. Tottenham za ta kammala cinikin Danso da zarar an buɗe kasuwar cinikin ƴan wasa

    Danso

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham za ta kammala sayen mai tsaron baya, Kevin Danso da zarar an buɗe kasuwar cinikin ƴan wasa ranar Lahadi.

    Mai buga Premier League ta ɗauki aron Danso daga Lens ta Faransa a watan Fabrairu, za kuma ta saye shi kan £21m.

    Mai shekara 26 ya buga wasa 10 a Premier League a kakar da aka kammala, ya canji ɗan ƙwallo a wasan karshe da Tottenham ta lashe Europa League bayan doke Manchester United a Sifaniya.

    Ƙwantiragin Sergio Reguilon da Fraser Forster da Alfie Whiteman zai kare a Tottenham a watan gobe.

    Yayin da take fatan mallakar Pierre-Emile Hojbjerg, wanda ya buga mata wasannin aro daga Marseille.

    Shi kuwa ɗan wasan tawagar Jamus, Timo Werner, mai shekara 29 zai koma ƙungiyarsa RB Leipzig, bayan wasannin aro.

    Har yanzu ba a fayyace makomar koci, Ange Postecoglou ba, bayan da Tottenham ta kare kakar bana a mataki mafi muni a tarihinta.

  15. Labaran da jaridu kan wallafa kan cinikin ƴan wasa, Daga jarida

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta fara tattaunawa kan siyan Benjamin Sesko, Manchester United na shirin tayin Kobbie Mainoo koda Bruno Fernandes ya bar kungiyar, Al-Hilal na iya zawarcin Cristiano Ronaldo.

    Arsenal ta fara tattaunawa da RB Leipzig a kokarinta na sayen dan wasan gaban kasar Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21, wanda ake neman sama da Yuro miliyan 80 (£67.4m) a kansa. (Sky )

    Har yanzu kofar Manchester United a bude take don karbar tayi kan dan wasan Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, koda kuwa dan wasan tsakiya kuma dan kasar Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 30, ya bar Old Trafford. (I Paper)

    Ana kuma sa ran kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya za ta nada kocin Inter Milan Simone Inzaghi a matsayin sabon kocinta bayan wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Asabar. (Sky Sports)

  16. Watakila Fernandes ya bar Man United

    Fernandes

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila Bruno Fernandes ya bar Manchester United a makon gobe, domin karɓar tayi mai tsoka da Al Hilal ta Saudiya ta yi masa.

    Wakilan ɗan wasan tawagar Portugal sun ce za su ci gaba da tattaunawa da Al Hilal, domin ya koma ƙungiyar da wuri, wadda za ta buga Club World Cup a watan Yuni.

    Ƙyaftin ɗin United na taka rawar gani a ƙungiyar kuma koci Ruben Amorim ya ce yana fatan zai ci gaba da aiki tare da ɗan ƙwallon

    Manchester United ba ta ce komai ba kan lamarin.

  17. Jama'a barkanmu da wannan lokacin

    Sunana Mohammed Abdu zan gabatar da muku da sharhi da bayanan wasanni daga ranar Asabar 31 zuwa 7 ga watan Yunin 2025.

    Za kuke iya bauyar da gudunmuwarku a lokacin da ake gabatar da shirin kai tsaye a BBCHausa Facebook ko kuma a X.