window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Labaran abubuwan da ke faruwa dangane da wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labaran wasanni a faɗin duniya na ranakun 31 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Inter na son Inzaghi ya ci gaba da koci bayan kasa cin Champions League

    Inzaghi

    Asalin hoton, Getty Images

    Inter Milan na fatan Simone Inzaghi zai ci gaba da horar da ita, duk da kasa daukar Champions League, in ji shugaban kungiyar Giuseppe Marotta.

    An caccaki kwazon kungiyar kan yadda Paris St Germain ta caskara Inter 5-0 a wasan karshe a babbar gasar tamaula ta Turai da suka yi a Munich.

    Inzaghi wanda ya karbi aikin horar da Inter a 2021, ana ta alakanta shi da aiki a gasar tamaula ta Saudiyya a Al Hilal, sai dai shugaban ya ce yana sa ran zai gi gaba da zama da su.

    Inzaghi ya dauki Serie A daya da Coppa Italia biyu a kaka hudun da ya yi a Inter.

    Kungiyar Italiya ta doke Bayern Munich da Barcelona a hanyar da ta kai wasan karshe, kuma karo na biyu da ta kai karawar karshe a kaka uku, bayan da Manchester City ta yi nasara a kanta 1-0 a 2023 a Instanbul.

    Rashin nasarar da Inter ta yi a hannun PSG na nufin ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi ba, wadda ta yi ta biyu a kofin da Napoli ta lashe.

    Haka kuma Inter ta yi rashin nasara a hannun AC Milan a zagayen daf da karshe a Coppa Italiya.

  2. PSG 5-0 Inter Milan

    PSG

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Wa Tottenham za ta fuskanta a Uefa Super Cup, PSG ko Inter?, PSG da Inter Milan

    Tottenham za ta buga Champions League a baɗi, bayan da ta ci Manchester United ta lashe Europa League a Sifaniya.

    A ranar ta Asabar, Tottenham za ta san wadda za ta fuskanta a Uefa Super Cup na 2025 - gasar da ake yi tsakanin mai Champions League da wadda take da Europa League.

    Za a buga Uefa Super Cup a Udinese a Italiya ranar 13 ga watan Agusta.

  5. A ina Mbappe zai kalli wasan PSG da Inter?, PSG da Inter Milan

    Kylian Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    2 ga watan Yuni 2024: Kylian Mbappe ya saka hannu kan yarjejeniyar buga wa Real Madrid tamaula, bayan kaka bakwai a PSG ba tare da lashe kofin zakarun Turai ba.

    16 ga watan Afirilu 2025: Ranar da Arsenal ta fitar da Real Madrid mai rike da kofi daga Champions League na kakar nan.

    31 ga watan Mayu 2025: Ranar da PSG tsohuwar ƙungiyar Mbappe ta kai zagayen karshe a Champions League.

  6. Ko PSG za ta ɗauki Champions League ranar Asabar, PSG da Inter Milan

    Ƴan wasa fitattu da yawa sun buga wa Paris St German tamaula, amma sun kasa ɗauakr mata Champions League da ya haɗa da Kylian Mbappe da Neymar da Lionel Messi da George Weah da Ronaldinho da David Beckham da Zlatan Ibrahimovic da sauransu.

    Shin ko Luis Enrique zai ɗaukarwa PSG Champions League?

    Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

    Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

    Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Yadda ƙungiyoyin za su fara da ƴan wasa 11, PSG da Inter Milan

    PSG starting XI: Donnarumma, Hakimi, Marquinhos, Pacho, Mendes, Ruiz, Neves Vitinha, Dembele, Doue, Kvaratskhelia.

    Inter Milan starting XI: Sommer, Dumfries, Pavard, Acerbi, Bastoni, Barella, Calhanoglu, Mkhitaryan, Dimarco, Martinez, Thuram.

  8. Filin Allianz Arena ya fara ɗaukar harami, PSG da Inter Milan

    Allianz Arena

    Asalin hoton, BBC Sport

  9. Kimanin magoya bayan Inter Milan 40,000 ne suka je Munich, PSG v Inter Milan

    Ticket

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu rahotannin na cewa kimanin magoya bayan Inter 40,000 ne suka je Munich, domin ganin wasan karshen.

    To sai Uefa ta bai wa kowacce ƙungiya tikiti 18,000 - kenan wasu da yawa ba za su samu damar shiga sitadiya ba.

  10. Wasu na neman tikiti ruwa a jallo, PSG da Inter Milan

    Ticket

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya baya sun halarci filin wasa na Bayern Munich, inda za a buga wasan karshe a Champions League, sai dai wasu na neman tikitin da za su saya.

    Wani ɗan kallon ya ce zai bayar da Yuro 2,000 duk tiket ɗaya domin ya samu kallon karawar.

  11. Champs

    Asalin hoton, Reuters

    Champs

    Asalin hoton, Reuters

    Champs

    Asalin hoton, Reuters

  12. Dubban magoya baya sun fara hallara a Munich don kallon wasan karshe na Champions League

    Munich

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban masoya kwallon kafa ne suka fara hallara a filin wasa na Munich domin kallon wasan karshe na gasar Zakarun Turai.

    Parist St-Germain ta Faransa za ta fafata da Inter Milan ta Italiya, inda kowannensu ke ƙoƙarin ganin ya lashe kofin.

    PSG ba ta taɓa lashe kofin ba a tarihinta duk da kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen ƴan wasa a shekarun da suka gabata - Inter Milan ta lashe gasar har sau uku.

    Ana sa ran mutum 70,000 ne za su kasance a filin wasan Munich Allianz Arena, inda miliyoyi kuma daga sassan duniya za su kalli wasa a gidajen talbijin.

    Munich

    Asalin hoton, Getty Images

    Munich

    Asalin hoton, Getty Images

  13. AC Milan ta sake ɗaukar Massimiliano Allegri kociyanta

    Allegri

    Asalin hoton, Getty Images

    AC Milan ta sake ɗaukar Massimiliano Allegri a matakin kociyanta.

    Mai shekara 57 ya horar da mai buga Serie A daga Yunin 2010 zuwa Janairun 2014.

    Allegri ya maye gurbin Sergio Conceicao, wanda aka kora ranar Alhamis, duk da wata shida ya yi a kan mukamin.

    Milan ta kasa taka rawar da ya kamata a 2024/25, wadda ta kare a mataki na takwas, haka kuma ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Bologna a Coppa Italia, kenan ba za ta buga gasar zakarun Turai ba a baɗi.

    Rabon da Milan ta lashe Serie A tun bayan na 19 da ta ɗauka a 2021/22 karkashin kociya, Stefano Pioli.

    Allegri ya ɗauki Scudetto a kakarsa ta farko a Milan a 2010-11 - kofin farko a ƙungiyar tun bayan 2004 - daga nan kuma ta kore shi.

    Daga nan ya koma Juventus ya dunga lashe kofin tun daga 2014 zuwa 2019, wanda ya ci Serie A karo biyar a jere.

    Allegri ya horar da Aglianese da SPAL da Grosseto da Sassuolo da kuma Cagliari.

  14. European Cups

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa

    Anthony

    Asalin hoton, Getty Images

    Al-Hilal na tattaunawa da AC Milan kan cinikin dan wasan baya na kasar Faransa Theo Hernandez, mai shekara 27, wanda ke kan gaba cikin cikin yan wasan da kungiyoyi ke marari a gasar Saudi Pro League a bazara. (Fabrizio Romano)

    Jami'ai daga Real Betis za su gana da takwarorinsu na Manchester United a mako mai zuwa don tattaunawa kan makomar dan wasan Brazil Antony mai shekaru 26 da yiyuwar kungiyar Red aljannu ba za ta sake barin shi a matsayin aro ba. (Marca Espanya)

    Dan wasan gaban Faransa, Christopher Nkunku, zai bar Chelsea a bazarar nan, yayin da Tottenham ta yi bincike kan yiwuwar siyan dan wasan mai shekaru 27. (Talksport)

  16. Wasan da Ramadan ya buge Autan 'Yar Biyat, Manu ya doke Dogon Sama'ila

    Bayanan bidiyo, Ramadan ya buge Autan 'Yar Biyat, Manu ya doke Dogon Sama'ila
  17. , Paris St Germain da Inter Milan

    Birnin Paris ya ɗauki harami kan wasan karshe a Champions League tsakanin Paris St Germain da Inter Milan ranar Asabar, inda shaguna suke taka-tsantsan, an raba jami'an tsaro a lokacin da magoya bayan PSG ke ta murna.

    Duk da cewar a Jamus za a buga wasan, amma da zarar PSG ta lashe kofin, murnar da za a yi a birnin ka iya komawa ta tashin hankali, hakan ya sa aka tura ƴan sanda 5,400 domin kula da doka da oda.

    Ana kuma sa ran magoya bayan PSG za su taru a wurare da yawa domin kallon wasan a babban alluna da za a tanada a birnin Paris har da Parc des Princes.

    Tuni jami'an tsaro sun hana ajiye mota a kan titi - wannan shi ne karo na biyu da PSG ta kai wasan karshe a Champions League, kofin da ba ta taɓa ɗauka ba, Inter tana da uku a tarihi.

  18. Gasperini ya bar aikin horar da Atalanta mai buga Serie A

    Gian Piero Gasperini

    Asalin hoton, Getty Images

    Gian Piero Gasperini ya bar aikin horar da Atalanta, wanda ya yi ban kwana da ƙungiyar ranar Asabar.

    Ba a yi mamaki ba da ya ajiye aikin, domin tun cikin watan Fabrairu ya sanar cewar ba zai tsawaita yarjejeniyarsa ba da Atalanta, wadda za ta kare a karshen watan Yuni.

    Mai shekara 67 ya saka Atlanta cikin manyan ƙungiyoyin Serie A har da gasar zakarun Turai, wanda ya lashe Europa League a 2024.

    Wasu rahotanni daga Italiya na cewar Gasperini zai je ya karɓi aikin kociyan AS Roma ma, sakamakon da Claudio Ranieri ya yi ritaya bayan kammala kakar bana.

  19. Roma

    Asalin hoton, Fabrizio Romano twitter

  20. Amurka na son yin haɗakar shirya gasar kofin duniya ta mata a 2031

    Women World Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka na son yin haɗaka da Mexico, domin gudanar da gasar cin kofin duniya na mata a 2031.

    ESPN ta bayar da rahoton cewar hukumar ƙwallon kafa ta Mexico ta tabbatar da hakan.

    Tun farko Fifa ta sanar cewar Amurka ce ke takarar shirya gasar 2031, wadda tawaga 48 za ta kece raini a karon farko.

    Tun farko Amurka da Mexico sun so shirya wasannin 2027 daga baya suka janye, domin tsara yadda za su karɓi bakuncin gasar 2031.

    Za a buga gasar cin kofin duniya ta mata a 2027 a Brazil

    Za a fafata a gasar kofin duniya ta maza a 2026 a Amurka da Mexico da kuma Canada.

    Biranen da za a gudanar da wasanni daga 16 guda 11 daga Amurka suka, inda za a fara bikin buɗe gasar a filin MetLife Stadium a New Jersey.