window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

KAI TSAYE, Labaran abubuwan da ke faruwa dangane da wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labaran wasanni a faɗin duniya na ranakun 31 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Alcaraz ya kai daf da karshe a French Open

    Mai rike da kofin French Open, Carlos Alcaraz ya kai zagayen daf da karshe, sakamakon da ya yi waje da Tommy Paul a gasar ta Roland Garros.

    Dan kasar Sifaniya ya kai zagayen gaba ne a cikin minti 53 a fafatawar da suka yi a birnin Paris.

    An kuma yi waje da Paul a zagayen kwata fainal, bayan da aka doke shi da ci 6-0 6-1 6-4 victory.

    Alcaraz zai fafata da mai shekara 23, Lorenzo Musetti a zagayen daf da karshe.

    Alcaraz

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Ina Luca Modric zai koma da taka leda?

    Luca Modric

    Asalin hoton, Getty Images

    Yarjejeniyar Luka Modric za ta karkare a Real Madrid a karshen watan Yuni.

    Dan wasan tawagar Crotia ya taka rawar gani a kungiyar Sifaniya, shi ne kan gaba a yawan lashe kofuna a Real Madrid.

    Tun bayan da Real Madrid ta dauki dan wasan daga Tottenham ya zama kashin bayan kungiyar, mai kyautar Ballon d'Or mai taka leda a daga tsakiya.

    Real Madrid, wadda ta yi ta biyu a teburin La Liga a kakar da ta kare za ta buga Club World Cup a Amurka - ko Modric zai buga mata wasannin.

    Za a fara Club World Cup daga 14 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.

    Wasu rahotannin na cewar kyaftin din Real Madrid zai koma taka leda a gasar Serie A a kakar badi.

  3. Manchester City ta sayi Reijders daga AC Milan

    AC Milan

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City ta amince za ta biya AC Milan (£46.3m) domin sayen dan wasan tawagar Netherlands, Tijjani Reijnders.

    Mai shekara 26, zai saka hannu kan yaejejeniyar kaka biyar a kungiyar Etihad.

    City na fatan kammala cinikin, domin Reijders ya samu buga mata Club World Cup da za a fara ranar 14 ga watan Yuni a Amurka.

    Idan har ya koma Etihad, kungiyar za ta magance gurbin da Mateo Kovacic ke buga wa, wanda ya ji rauni ba zai samu zuwa Amurka ba.

    Watakila Kevin de Bruyne ya bi Manchester City Club World Cup, duk da ana alakanta shi da Napoli, wadda ta lashe Serie A a kakar da aka kammala.

  4. Watakila Chelsea ta dauki Gittens

    Jamie Gittens

    Asalin hoton, Getty Images

    Guardian ta bayar da rahoton cewar Chelsea na duba yadda za ta dauki dan wasan Borussia Dortmund, Jamie Gittens.

    Gittens ya taka leda a makarantar horar tamaula ta Chelsea da Reading da Manchester da kuma Borussia Dortmund.

    Mai shekara 20 mai taka leda a tawagar Ingila ta matasa yan kasa da shekara 21 zai kai £50m.

    Gittens ya ci kwallo 12 a dukkan karawar da ya yi wa Dortmund a 2024-25

  5. Inter Milan da Simone Inzaghi sun raba gari a tsakaninsu

    Inzaghi

    Asalin hoton, Getty Images

    Inter Milan da Simone Inzaghi sun raba gari a tsakaninsu, bayan da kungiyar Italiya ta sha kashi a wasan karshe a Champions League da Paris St Germain ta lashe kofin a karon farko a tarihi.

    Mai shekara 49, wanda ya karbi aiki a 2021, ana alakanta shi da zai koma horar da tamaula a babbar gasar tamaula ta Saudiyya da Al-Hilal.

    Inzaghi ya lashe Serie A da Coppa Italia biyu da Supercoppa Italia uku a kungiyar ta san Siro.

    Sau biyu yana kai Inter wasan karshe a Champions League, inda ya sha kashi a hannun Manchester City da ci 1-0 a 2022-23 da wanda PSG ta dura musu 5-0 ranar Asabar.

    Inzaghi ya bar Inter, wadda za ta buga Club World Cup da za a fara a Amurka daga 14 ga watan Yuni da kungiya 32 za su kece raini a karon farko.

    Haka itama Al-Hilal za ta fafata a Club Worl Cup.

  6. Ko kungiyar Serie A za ta yi zawarcin Rasmus Hojlund

    Rasmus Hojlund

    Asalin hoton, Getty Images

    Gazzetta dello Sports ta ce watakila Inter Milan za ta nemi a bata aron mai shekara 22, Rasmus Hojlund daga Manchester United.

    Dan wasan tawagar Denmark ya koma Old Trafford daga Atalanta mai buga Serie A kan £72m a Agustan 2023.

  7. Wasu rahotanni na cewar Mitrovic zai koma buga Premier

    Mitrovic

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu rahotannin na cewar watakila Manchester United da Everton da West Ham za su yi zawarcin Aleksandar Mitrovic.

    Tsohon dan wasan Fulham mai shekara, 30, ya ci kwallo 68 a wasa 79 tun bayan da ya koma Saudiyya da taka leda.

    Al-Hilal ta amince za ta sayar da Mitrovic ko kuma ta bayar da aronsa.

  8. Barcelona ta fara tuntubar Liverpool kan Diaz

    Luiz Diaz

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta fara tuntubar Liverpool kan daukar Luis Diaz wanda kungiyoyin Saudiyya ke son zawarci dan wasan tawagar Colombia in ji Sky Sports.

    A rahoton ya bayyana Barcelona ke son sayen Diaz, wanda take ganin da rawar da zai taka mata a badi.

    Diaz ya ci kwallo 16 a dukkan fafatawa a Liverpool a 2024-25, har da 13 a Premier League da ta kai Liverpool ta lashe kofin kakar da ta kare na 20 jimilla.

  9. Su waye ke son sayen Mbeumo bayan Man United?

    Mbeumo

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle da Arsenal da kuma Tottenham suna daga cikin wadanda ake cewar suna son sayen dan wasan Mbeumo daga Brentford.

    Wasu rahotannin na cewar dan wasan ya bukaci duk mai son sayensa sai ya linka albashinsa uku da ya karbar £45,000 a duk mako a Brentford.

  10. Chelsea na farautar ɗan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20, Jamie Gittens, wanda ake kiyasata kudinsa kan £50m. (Guardian)

    Manchester City na dab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan AC Milan da Netherlands, Tijjani Reijnders mai shekara 26. (Football Italia)

    Everton da Manchester United da West Ham na farautar ɗan wasan Serbia, Aleksandar Mitrovic, wanda Al-Hilal ke shirin rabuwa da shi. (Talksport)

    Brighton na bibbiyar ɗan wasan Sheffield United, Ollie Arblaster mai shekara 21. (Teamtalk, external)

    Tsohon ɗan wasan Arsenal da Ingila, mai shekara 33, Jack Wilshere, na gab da zama koci a ƙungiyar League One ta Plymouth Argyle. (Sun)

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Ban san me zai faru a makonni masu zuwa ba Kerkez

    Milos Kerkez

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana alakanta Liverpool da dan wasa, Milos Kerkez mai taka leda a Bournemouth.

    Wasu jaridun sun wallafa cewar Liverpool na son sayen matashi Kerkez mai shekara 21, wanda zai kai £40m daga Bournemouth.

  12. Mark Flekken ya koma Bayern Leverkusen

    Mark Flaken

    Asalin hoton, Getty Images

    Brentford ta tabbatar cewar mai tsaron ragarta Mark Flekken ya koma Bayer Leverkusen kan yarjejeniyar da za ta kare zuwa karshen kakar 2028.

    Ya bar buga gasar Premier League, bayan wasa 77 a Brentford a dukkan fafatawa.

  13. Robert Lewandowski

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta soma tattaunawa da ɗan wasan Liverpool, Luis Diaz mai shekara 28, sai dai yana samun tayi daga Saudiyya. (Florian Plettenberg)

    Chelsea na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasa daga Everton, Jarrad Branthwaite mai shekara 22, yayin da Tottenham ke kalubalantarta. (Teamtalk)

    Ɗan wasan tsakiya Jobe Bellingham ya zaɓi tafiya tsohuwar ƙungiyar kaninsa, Borussia Dortmund a maimakon Eintracht Frankfurt da RB Leipzig. (Bild - in German)

  14. West Brom ta dauki Ryan Mason kociyanta

    Mason

    Asalin hoton, Getty Images

    West Brom ta sanar da nada Ryan Mason a matakin sabon kociyanta.

    Wadda take buga Championship ta kori Tony Mowbray ranar 21 ga watan Afirilu daga nan ta fara tattaunawa da Mason, mai shekara 33, wanda ya koma Hawthorns kan yarjejeniyar kaka uku.

    Hakan ya kawo karshen kaka bakwai a Tottenham, wanda ya fara tun daga makarantar koyon tamaular kungiyar ya kuma buga mata wasa 70.

  15. Chelsea ta dauki Essugo kan £18m daga Sporting

    Essugo

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta sanar da daukar Dario Essugo kan £18m daga Sporting.

    Tun cikin watan Maris aka cimma yarjejeniya daga ciki har da Geovany Quenda da zai koma Stamford Bridge a kakar 2025-26.

    Essugo, mai shekara 20, ya buga wasannin aro a kungiyar La Liga Las Palmas a kakar da aka kammala.

    Matashin zai bi Chelsea buga Club World Cup, wanda zai ke jiran ko-ta-kwana duk lokacin da Moises Caicedo ya samu matsala.

  16. Rawar da Sancho ya taka a Chelsea

    Sancho

    Asalin hoton, Getty Images

    Jadon Sancho ya ci kwallo biyar ya bayar da 10 aka zura a raga a wasannin aro 42 da ya buga a Chelsea.

    Sai dai kwallo daya ya ci ya bayar da daya aka zura a raga a Premier League tun da aka shiga sabuwar shekara.

    Amma mai shekara 25 ya ci kwallo a wasan karshe da Chelsea ta doke Real Betis ta lashe Conference League.

    Ya kuma buga dukkan wasannin Conference tun daga zagaye na biyu har karawar karshen.

  17. Mbeumo na son komawa Man United

    Bryan Mbeumo

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila Bryan Mbeumo ya koma Manchester United, bayan da wasu rahotannin ke cewar dan wasan na son komawa Old Trafford da taka leda.

    David Ornstein na Atletic ya bayar da rahoton cewar dan wasan tawagar Kamaru, wanda ya ci kwallo 20 a Premier League ya fi son komawa United fiye da duk masu zawarcinsa har da Tottenham.

    Ana cewa United za ta fara zawarcin dan wasan mai shekara 25, domin buga mata kakar nan gaba.

    Tuni dai United ta amince za ta daiki Matheus Cunha daga Wolverhampton.

  18. Dortmund na fatan sayen kanin Bellingham

    Jobe Bellingham

    Asalin hoton, PA Media

    Borussia Dortmund tana da tabbaci ita ce za ta dauki dan wasan Sunderland, Jobe Bellingham.

    Matashin mai shekara 19, kungiyoyi da yawa na son sayen shi, bayan da ya bayar da gudunmuwar da Sunderland ta samu gurbin komawa buga Premier League a kakar da za mu shiga.

    Har yanzu Dortmunda ba ta fara tattaunawa ba da Sunderland, amma ana sa ran Bellingham zai bi sawun yayansa, wanda ya taka leda a kungiyar da ke buga Bundesliga.

    Dortmund ta kare a mataki na hudu a teburin Bundesliga a kakar da ta wuce, kenan za ta buga Champions League a badi.

    Dortmund ta dauki Jude Bellingham daga Birmingham City a 2020 – ya buga mata wasa 132 a kaka uku da lashe German Cup tare da Erling Haaland da kuma Jadon Sancho a 2021.

    Daga nan ya koma Real Madrid da taka leda a 2023.

    A watan jiya aka bayyana Jobe Bellingham a matakin dan wasan da ba kamarsa a Championship – kyautar da Bellingham ya lashe kaka biyar da ta wuce.

  19. Me ya sa aka bude kasuwar cinikin yan wasa a watan Yuni?

    An bude kasuwar cinikin yan wasa ranar 1 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan.

    Za kuma a sake yin hada-hada tsakanin ranar Litinin 16 ga watan Yuni zuwa Litinin 1 ga watan Satumba.

    Fifa ta amince da bude kasuwa a farkon watan Yuni, domin bai wa kungiyoyin da za su buga Club World Cup su samu damar kara karfi, ko sa taka rawar ganin da ta dace.

    Kungiya 32 ne za su buga Club World Cup da za a fara daga 14 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli a Amurka.

    Manchester City ce mai rike da kofin tun kan a sauya fasalin wasannin.

  20. Nick Kyrgios ba zai buga Wimbledon Open ba

    Nick Kyrgios

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan kasar Australiya, Nick Kyrgios ya ce ba zai buga gasar Wimbledon ba, bayan da ya ci karo da rauni, sakamakon fama rauni da ya yi.

    Kyrgios, wanda Novak Djokic ya doke shi a 2022 a wasan karshe a gasar da ake yi a All England Club, bai buga tennis da yawa ba a kaka biyun da ta wuce, sakamakon raunin tsintsiyar hannu, wanda ke bukatar tiyata.

    A watan Maris a Miami, mai shekara 30 ya lashe kofi a karon farko tun bayan 2022 – daga nan ya sanar ba zai iya buga French Open ba da ake tata burza a birnin Paris.