window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Labaran abubuwan da ke faruwa dangane da wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labaran wasanni a faɗin duniya na ranakun 31 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Swiatek ta kai kwata fainal a French Open bayan doke Rybakina

    Iga Swiatek

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai rike da French Open, Iga Swiatek ta doke Elena Rybakina ta kai zagayen kwata fainal a gasar da ake yi a birnin Paris.

    Ƴar kasar Poland ta yi nasarar cin 1-6 6-3 7-5.

    Wannan shi ne wasa na 25 a jere da Swiatek ta lashe a jere a French Open, wadda ke fatan ɗaukar kofin karo na biyar a cikin kaka biyar.

    Swiatek za ta fuskanci Elina Svitolina a zagayen kwata fainals, wadda ta yi waje da Jasmine Paolini.

  2. Lewandowski na ci gaba da taka rawar gani a Barcelona

    Robert Lewandowski

    Asalin hoton, Getty Images

    Robert Lewandowski yana taka rawar gani a Barcelona, duk da cewar yana da shekara 36 a ƙungiyar.

    A kakar da aka kammala ya ci ƙwallo 42 a wasa 52 a dukkan fafatawa.

    A kakarsa ta farko a Barcelona a 2022/23, Lewandowski ya ci ƙwallo 33 a karawa 46.

    Sai kuma a kaka ta biyu wato a 2023/24, ya zura ƙwallo 26 a raga a karawa 49.

  3. Club Worl Cup

    Asalin hoton, One Footbal Twitter

  4. Thibaut Courtois zai yi jinya in ji Real Madrid

    Thibaut Courtois

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Real Madrid ta sanar a shafinta na Intanet cewar mai tsaron ragarta, Thibaut Courtois ya ji rauni.

    Sai dai ƙungiyar ta Sifaniya ba ta fayyace kwanakin da zai yi jinya ba da ranar da zai koma taka leda.Wannan raunin da Courtois ya ji koma baya ne ga Real Madrid, wadda za ta buga Club World Cup da za a fara ranar 14 ga watan Yuni a Amurka tsakanin ƙungiya 32 a karon farko a tarihi.

  5. An fitar da ƴan wasa 11 fitattu na Champions League

    Uefa

    Asalin hoton, Uefa Twitter

    Ranar Asabar aka kammala Champions League, bayan da Paris St Germain ta lashe kofin, sakamakon da ta doke Inter Milan 5-0 a Jamus.

    Ranar Lahadi hukumar ƙwallon kafar Turai, Uefa ta sanar da fitattun ƴan wasa 11 na Champions League, inda bakwai daga ciki daga PSG suke.

    Fitattun ƴan wasan Champions League:

    Mai tsare raga: Gianluigi Donnarumma (PSG)

    Masu tsare baya: Achraf Hakimi (PSG), Marquinhos (PSG), Alessandro Bastoni (Inter), Nuno Mendes (PSG)

    Masu buga tsakiya: Vitinha (PSG), Declan Rice (Arsenal)

    Masu cin ƙwallaye: Lamine Yamal (Barcelona), Desire Doue (PSG), Ousmane Dembele (PSG), Raphinha (Barcelona)

  6. Arnold zai buga wa Real Madrid Club World Cup

    Arnold

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta kammala ɗaukar Trent Alexander-Arnold daga Liverpool a karshen mako, kuma ɗan wasan tawagar Ingila zai buga wa Real Madrid Club World Cup da za a fara a Amurka daga 14 ga watan Yuni.

    Karon farko da za a buga tsakanin ƙungiya 32 a tarihi

    .

  7. Dembele ne fitatcen ɗan wasan Champions League - Uefa

    Dembele

    Asalin hoton, Uefa

    Ɗan ƙwallon Paris St Germain, Ousmane Dembele shi ne ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan wasan Champions League kamar yadda UEFA ta sanar ranar lahadi.

    Ranar Asabar PSG ta lashe Champions League, bayan doke Inter Milan 5-0 a Allianz Arena a Jamus.

    Dembele mai shekara 28 ya ci ƙwallo takwas a gasar zakarun Turai ta bana.

    Koda yake Dembele bai ci ƙwallo ba a wasan da PSG ta ɗura 5-0 a ragar Inter, amma ya taka rawar gani a fafatawar.

    Haka kuma matashin ɗan wasan PSG mai shekara 19, Desire Doue, shi ne ya lashe ƙyautar matashin da ba kamarsa a ƙwazo a Champions League.

  8. An samu ƙungiya ta karshe da ta samu gurbin Club World Cup

    Fifa Club World Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Los Angeles FC ita ce ƙungiya ta 32 da za ta buga Club World Cup da za a yi a Amurka a cikin watan Yuni.

    Ranar Asabar ta doke Club America ta Mexico 2-1, kenan za ta karɓi kusan $10-million ladan shiga gasar.

    LAFC tana rukuni ɗaya da Chelsea mai buga Premier League a wasannin Club World Cup da za a fara ranar 14 ga watan Yuni a kammala ranar 13 ga watan Yuli a birnin New York.

    Sauran dake rukuni na huɗu da LAFC har da Flamengo ta Brazil da kuma ES Tunis ta Tunisia.

    Duk kungiyar da za ta buga Club World Cup za ta samu ladan $9.55, sannan wadda ta ci wasa za ta karɓi $2 million.

    Duk wadda ta lashe kofin za a bata sama da $100 million.

  9. An buɗe kasuwar cinikin ƴan wasa ranar Lahadi

    Cunha

    Asalin hoton, Getty Images

    An buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo daga ranar Lahadi, inda za a yi kwana 10 ana hada-hada.

    An kuma yi hakan ne domin bai wa kungiyoyi damar yin cefane, domin taka rawar gani a Club World Cup da za a yi a Amurka a cikin watan nan.

    Daga cikin ƙungiyoyin Ingila da za su wakilce ta a wasannin da Amurka za ta shirya har da Manchester City da Chelsea.

    Kuma kada a bai wa City da Chelsea dama su kaɗai an amince sauran ƙungiyoyi su yi cefane idan suna bukata har da masu buga EPL.

    Za a rufe kasuwar ranar Talata 10 ga watan Yuni.

    Za kuma a sake buɗe kasuwar nan gaba, domin shirin tunkarar fara kakar bana.

    Ana sa ran fara gasar Premier League daga 16 ga watan Agusta.

    Manchester United ta ɗauki Matheus Cunha daga Wolverhampton.

  10. Rodrygo

    Asalin hoton, Getty Images

    Danwasan gaban Brazil Rodrygo, mai shekara 24, ya shaida wa Real Madrid cewa yana son ci gaba da zama a kungiyar duk da sha'awar da kungiyoyin Premier daban-daban ke nunawa kansa. (Marca Spanish)

    Manchester City za ta gabatar da tayin farko kan danwasan tsakiya na Lyon da Faransa Rayan Cherki, mai shekara 21 a wannan makon. (Fabrizio Romano)

    Danwasan Liverpool dan kasar Holland Cody Gakpo, mai shekara 26, da kuma dan kasar Japan Kaoru Mitoma na Brighton, mai shekara 28, suma suna cikin jerin wadanda Bayern Munich ke son dauka. (Christian Falk)

  11. Tottenham

    Asalin hoton, Tottenham Twitter

  12. Damben Ilele da Shagon Audun Tunga a Maraba

    Bayanan bidiyo, Damben Ilele da Shagon Audun Tunga a Maraba
  13. Sama da mutun 500 yan sanda suka kama a lokacin da ake bikin lashe Champions League a Faransa - an kuma bayar da rahoton mutuwar mutum biyu da 192 da suka ji rauni a ci gaba da murna da aka yi ranar Lahadi.

    A daren Asabar aka barke da murna da sowa a biranen Faransa har zuwa Lahadi, bayan da Paris St Germain a karonta na farko a tarihi ta lashe Champions League da caskara Inter Milan 5-0 a Allianz Arena filin Bayern Munich a Jamus.

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ta sanar a ranar Lahadi cewar ana tsare da mutum 559 har da 491 da aka kama a birnin Fari, kenan ana tsare da 320 a caji ofis kuma 254 daga ciki a birnin Paris.

  14. Djokovic zai fafata da Norrie a zagaye na huɗu a French Open

    Djokovic

    Asalin hoton, Getty Images

    Novak Djokovic ya doke Filip Misolic in straight ya kai zagaye na huɗu a French Open zai kuma fuskanci Cameron Norrie a zagayen gaba.

    Djokovic ya yi nasara da cin 6-3 6-4 6-2 a wasan da karawar karshe a Champions League ta ɗauke hankalin ƴan kallo, inda PSG ta yi murnar lashe kofin a karon farko, bayan doke Inter Milan 5-0 a Jamus.

  15. Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona za ta karfafa neman da take yi wa danwasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford mai shekara 27 ne idan bata cimma matsaya da dan wasan Colombia Luis Diaz, mai shekara 28 na Liverpool ba. (Mundo Deportivo)

    Tottenham na duba yiwuwar rike danwasan gaban Faransa Mathys Tel, mai shekara 20 a matsayin dan wasanta na din din din daga Bayern Munich. (Sky Sports)

    Kocin Fulham Marco Silva ne ke kan gaba wajen neman zama sabon kocin Juventus (Sky Italy)

  16. Labarai da dumi-dumi, Man United ta ɗauki Cunha daga Wolves kan £62.5m

    Cunha

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta kulla yarjejeniya da Wolves domin sayen Matheus Cunha kan £62.5m.

    Tun farko United ta amince za ta biya ƙunshin yarjejeniyar ɗan wasan mai shekara 26 ɗan ƙwallon tawagar Brazil

    Tsohon ɗan wasan Atletico Madrid, zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar a Old Trafford da cewar za a iya tsawata masa wata 12 da zarar ya yi abin kirki.

    Tuni aka kammala auna koshin lafiyar Cunha a shirin da yake na komawa United da taka leda.

    Sai dai yarjejeniya za a kammalata ne da zarar Cunha ya gama buga wa Brazil karawar neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi ranar Juma'a.

    Cunha ya koma taka leda a Molineux a 2023 daga Atletico Madrid, bayan da ya fara daga wasannin aro.

    .

  17. Sinner ya kai zagaye na huɗu a French Open

    Sinner

    Asalin hoton, Getty Images

    Jannik Sinner ya doke Jiri Lehecka ya kai zagaye na huɗu a French Open

    Ɗan kasar Italiya ya yi nasara cikin awa ɗaya da minti 35 da cin 6-0 6-1 6-2.

    Kawo yanzu Sinner ya ci wasa 11 a jere.

  18. Mutum biyu sun mutu yayin bikin lashe Champions League a Faransa

    PSG

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum biyu sun mutum ana kuma tsare da mutanen da aka kama a birnin Paris a lokacin da magoya baya ke bikin murna lashe Champions League da Paris St Germain ta yi ranar Asabar bayan doke Inter Milan 5-0 a Jamus.

    Kamar yadda ma'aikatar dake kula da harkokin cikin gida ta sanar an kashe wani matakshi mai shekara 17, an kuma bugawa wani mutum wuka a kirji ranar Asabar.

    Haka kuma an bayar da rahoton wata mota ta buge wani mutum a kan karamin babur, wanda ya mutu nan take.

    Magoya baya da yawa ne suka kunna abubuwan tartsatsin wuta a yayin biki, an fasa gilasen motoci da yawa a birnin na Faransa.

    psg

    Asalin hoton, Reuters

  19. Man United ta kusan kammala cinikin Cunha kan £62.5m

    Cunha

    Asalin hoton, Getty Images

    Matheus Cunha ya je Manchester United a karshen mako, domin kammala yarjejeniyar komawa taka leda a Old Trafford kan £62.5m daga Wolverhampton.

    A makon jiya aka auna koshin lafiyar Cunha, ɗan wasan tawagar Brazil

    An ɗauki hoton ɗan wasan a lokacin da zai bar otal ɗin Lowry a Manchester ranar Lahadi da safe

    Ya kuma je Brazil, domin buga wasan neman shiga gasar kofin duniya da Ecuador ranar Juma'a, shi ne wasan farko da sabon koci, Carlo Ancelotti zai fara jan ragama.

    Idan har ba a ci karo da matsala ba, Cunha ne zai zama na farko da Ruben Amorim ya ɗauka kan fara kaka mai zuwa.

    Cunha ya ci ƙwallo 33 a wasa 76 a Wolves tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Atletico Madrid a Janairun 2023, wanda ya fara daga wasannin aro.

    A kuma kakar ce Wolves ta sayi Cunha kan 40m euros (£35m).

    Manchester United ta kare kakar da aka kammala a mataki na 15 da maki iri ɗaya da na Wolves.

  20. Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United na sha'awar sayen danwasan tsakiya na Portugal da Sporting Pedro Goncalves, mai shekara 26, a matsayin wanda zai maye gurbin Bruno Fernandes, mai shekara 30, idan ya koma Saudiyya a bazara. (Sunday Mirror)

    Bayern Munich na sha'awar sayen danwasan tsakiya na Ingila da Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 26. (Football Insider)

    Crystal Palace na son Eze ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da su duk da sha'awar da sauran kungiyoyin Premier kamar Arsenal da Tottenham da kuma Manchester City ke nunawa kansa. (The I)