Karanta yadda BBC ke aiki don karfafa aminci da fadin gaskiya a labaran intanet

Masu bibiyar BBC a Burtaniya da sauran kasashen duniya na ganinta a matsayin kafa mai samar da amintattun labarai. Shafinmu na intanet, kamar talabijin din mu da tashoshinmu na rediyo ya kasance mai gaskiya da rashin nuna bambanci da dogaro da kai da adalci.

Ka'idojinmu na aikin jarida sun ce: "Duk abin da muke yi ya ta'allaka ne kan amincewar da masu bibiyarmu ke da ita kan shirye-shiryenmu. Muna da 'yanci kuma ba ma nuna wariya kuma mun tsayar da gaskiya. Mun mayar da hankali wajen kaiwa kololuwar fitar da gaskiya da kin nuna bambanci kuma mun dage wajen kaucewa yaudarar masu bibiyarmu, walau a sane ko a cikin rashin sani.

"Jajircewarmu kan rashin nuna bambanci ita ce ginshikin dangantakar nan ta amincewa. A duka shirye-shiryenmu, za mu duba ko wane labara bil hakki da gaskiya. Za mu duba dukkan bayanai masu muhimmanci bisa adalci da gaskiya."

Mun san cewa gane sahihan labarai a intanet na iya zama abu mai rikitarwa. Mun kuma san cewa masu bibiyar labarai na so su kara fahimtar yadda BBC ke samar da labarai.

Saboda wadannan dalilai, BBC NEWS ta ke kara matsa kaimi wajen yin bayani kan irin bayanan da kuke karantawa ko kallo a shafinmu na intanet, da kuma wurin wadanda da inda bayanan ke fitowa sannan yadda ake tsara labara ya fito yadda yake. Ta yin haka, za mu taimaka maka ka gane abinda ya sa za a iya amincewa da BBC News.

Haka kuma, muna shirya wadannan bayanan na irin labaran da za a iya amincewa da su ta yadda za su dace da na'urori, ma'ana ana iya tsinto su ta hanyar lalubowa a intanet da shafukan sada zumunta da muhawara, ta hanyar taimaka masu gane kafofin yada labaran da suka kamata.

YADDA YA KAMATA A YI AIKI A DAKIN TATTARA LABARAI

BBC ta dade tana da dokokinta na aikin jarida da ake bi wajen tsara duka shirye-shiryenmu, wadanda kuma ke sa 'yan jaridarmu a hanya. Mun jere duka bangarori masu muhimmanci na dokokinmu a wannan shafi, don saukake maku yadda muke aiki da su a ofisoshinmu

Manufa: Manufar BBC it ace ta yi aiki don biyan bukatar al'uma, biya wa duka masu bibiyarta bukata ta hanyar samar da sahihan labarai masu inganci da ke sanarwa da ilimintarwa da nishadantarwa. Cikakkun bayanai na BBC Charter.

Tsarin Mallaka da Kudade: Muna da 'yanci don haka babu wasu daga wajen da ke mana kutse da zai iya yi wa gaskiyarmu a aikin jarida zagon kasa. Masu bibiyarmu su sani cewa matakan da muke dauka basu da alaka da siyasa ko matsin lambar kasuwanci ko ra'ayin wani mutum. Za ku iya samun Karin bayani kan yadda BBC News ke samun kudinta, a Burtaniya da kasashen waje a cikin BBC Charter on the independence of the BBC.

Ranar da aka kafa: An kafa BBC ranar 18 ga watan Oktobar 1922. Karanta Karin bayani kan tarihin BBC.

Manufar Da'a: Dokokin BBC na Aikin Jarida sun zayyano yadda za a nuna da'a a aikin da kuma ahnyoyin da ya kamata a bi wajen nuna da'a a duka shirye-shiryenmu.

Karin bayani:

Manufarmu kan daukar ma'aikata masu bambanci a jinsi da launin fata da addini: Karanta Karin bayani kan mayar da hankali da BBC ta yi kan daukar ma'aikata daga dukkan jinsi da asali da launin fata da kabila da addini a BBC Charter.

Rahoto kan daukar ma'aikata masu bambanci a jinsi da launin fata da addini: Fahimci yadda BBC NEWS ke aiki tukuru don kara yawan ma'aikata daban-daban a wannan Rahoton kan bayanin daidaito.

Gyare-gyare: BBC ta mayar da hankali kan cimma gaskiya. Ana iya samun manufofinta da suka shafi gyare-gyare a wannan bangaren na Dokokinmu na Aikin Jarida.

Dole ne Shirye-shiryenmu su zama suna da majiya, bisa shaidu masu karfi da aka tabbatar sahihai ne, kuma aka bayyana su karara yadda za a fahimta. Dole mu zama masu gaskiya kana abin da ba mu sani ba kuma mu guji jita-jita. Idan har muna zargi ko muna da bayanan da ba za mu iya tabbatarwa ba, lallai ne mu bayana hakan karara.

A shirye muke mu amshi laifin kuskure idan muka yi kuma mu yi koyi da kuskurenmu.

Idan aka gyara wani kuskure a wani labari a shafinmu na intanet tun bayan wallafa shi, za mu sa bayani a karshen labarin don alamta wa mai karatu cewa an yi gyara a labarin tare da ranar da aka yi gyaran. Idan aka samu karamin kuskure wanda ba zai taba muhimman abubuwan da ke cikin labarin ba (misali ba a rubuta suna daidai ba), za a yi gyara ba tare da an sa alama a karshen labarin ba.

Labarin da aka wallafa zai kasance a cikin kundin labaranmu a shafin intanet har abada, sai dai idan dama can an wallafa labarin ne don takaitaccen lokaci. Akwai lokutan da saboda umarnin kotu ko kuma tsaron lafiyar/rayuwar wasu, ko kuma kauce wa ka'idojin aiki da ba za a iya gyara labarin ba sai dai a cire shi gaba daya

Karin Bayani:

Dokokin Tantancewa/Bin-Diddigi: Manufar BBC ta tsage gaskiya da tantancewa na rubuce a Dokokin Aikin Jarida kan Tsage Gaskiya.

Majiyoyin da basu da suna: Manufar BBC da dokokinta kan amfani da majiyoyin da ba a sani ba ko wadanda bas u da suna na zayyane a cikin Dokokin Aikin Jarida.

Karin Bayani:

Kawo Korafin da za a iya yin wani abu a kansa: Tsarin BBC na korafe-korafe na cikin Tsarin BBC kan Korafe-Korafe.

Shugabanci: Ka san manyan tawagogin da ke tafi da bangaren labarai: Majalisar BBC News.

KWAREWAR 'YAN JARIDA

Labaran da ake wallafawa a BBC News wadanda 'yan jaridar ne da kansu suka bibiyi asalin labarin, na zuwa da sunan dan jaridar da ya rubuta labarin, kamar yadda ake yi wa labaran da 'yan jaridar da ke kwarewa a wani bangare suka rubuta.

Labarai na bai daya, wadanda ke da bayanai daga bangarori da dama ciki har da kamfanonin dillancin labarai, da bangaren BBC Newsgathering mai tattaro labarai da bangaren watsa shirye-shirye na BBC ko kuma wanda ma'aikatan BBC da dama suka sa hannu a cikinsa, ba su daukar sunan wadanda suka rubuta shi.

TRABE-RABEN AIKI

BBC News na banbance yin rahoto kan bayanan gaskiya da bayyana ra'ayi. Muna amfani da alamomi shidda da nau'ra ke iya karantawa:

  • Labarai- Aikin jarida da ya dogara kan sahihan bayanai, wadanda wakilinmu ya duba kuma ya tantance, ko kuma wadanda majiyoyi masu karfi suka bayar
  • Sharhi- Sau da yawa shirye-shiryenmu sun dogara ne kan ilimin wani kwararre, zai iya kasancewa ma'aikacin BBC ko kuma daga wajem don taimakawa wajen fahimtar bayanai masu rikitarwa
  • Zaburar da masu bibiyarmu - Labara da ke zaburar da masu bibiyarmu su amsa mana tambaya ko su tofa albarkacin bakinsu
  • Masu Fahimtarwa - Labarai da za su zayyana da bayanai masu sahihanci filla-fill, a saukakakkiyar hanya kan wani batu
  • Ra'ayi - BBC News ba ta nuna fiffiko ga wani bangare kuma ba ta ba da ra'ayinta kan labarai, amma wani lokaci, mu kan wallafa ra'ayoyin kwararru daga waje, inda suke bayar da shawarwari bisa yadda suka fahimci bayanan da suka shafi labari.
  • Bita - Labarin da ya dogara kan yadda aka tantance ko kuma aka duba wani taro, ko zane da sauransu, da ya kunshi ra'ayin wani da ya halarci taron ko ya tantance zanen.

MAJIYOYI

Ya kamata shirye-shiryenmu su zama suna da majiyoyi da suka dogara da shaidu masu karfi, kuma wadanda aka gwada sosai sannan a gabatar da su da yare mai saukin fahimta. Muna kokarin zama masu gaskiya kana bin da ba mu da masaniya a kai don gujewa zargi.

A lokutan da BBC News ta dogara kan majiya daya kan wani bangare mai muhimmanci na shirye-shiryenta, za mu dage wajen ambatar sunan majiyar inda zai yiwu. Sau da yawa muna Ambato rahotannin da aka fitar a hukumance da alkaluma da sauran majiyoyin bayanai, don ba ku damar gane bayanan da muke kawo maku rahoto a kai.

Duk lokacin da ya dace, muna Ambato wasu shafukan intanet masu muhimmanci da ke da karin bayani.

TSARIN LABARAI

Ga labaran da suke da rikitarwa, kamar labaran binciken kwakwaf ko labaran da suka kunshi alkaluma da dama, za mu taimaka maku ku fahimci yadda muka gudanar da aikin ta hanyar nuna maku bayanan bayan fage da kuma bayyana wasu yarjejeniyoyi da zato ko wasu tsare-tsaren da muka bi muka rubuta labarin- misali, tsarin da muka bi muka rubuta labarin; yawan mutanen da muka yi bincike a kansu; wakilci; bambanci tsakanin sakamakon bincikenmu da ainihin yadda abin yake a zahiri; yadda muka tattara bayanai; muhimmancin inda muka gudanar da b da lokutan da muka tattara bayananmu.