Nick Kyrgios ba zai buga Wimbledon Open ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan kasar Australiya, Nick Kyrgios ya ce ba zai buga gasar Wimbledon ba, bayan da ya ci karo da rauni, sakamakon fama rauni da ya yi.
Kyrgios, wanda Novak Djokic ya doke shi a 2022 a wasan karshe a gasar da ake yi a All England Club, bai buga tennis da yawa ba a kaka biyun da ta wuce, sakamakon raunin tsintsiyar hannu, wanda ke bukatar tiyata.
A watan Maris a Miami, mai shekara 30 ya lashe kofi a karon farko tun bayan 2022 – daga nan ya sanar ba zai iya buga French Open ba da ake tata burza a birnin Paris.