Chelsea na tattaunawa da AC Milan kan Mike Maignan

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta fara tattaunawa da AC Milan domin neman sayen mai tsaron ragarta Mike Maignan.
Ƙungiyar ta Italiya na neman fam miliyan 25 ne domin barin ɗan wasan ya tafi, amma Chelsea ta ce ya yi tsada, don haka tana neman ragi.
Maignan shi ne mai tsaron ragar Faransa kuma ya buga mata wasanni 30 daga 2020 zuwa yanzu. Shi ne kuma golan da Faransa ta fi amfani da tun bayan da Hugu lloris ya yi ritaya a 2023.
BBC ta samu bayanan cewa ɗan wasan na da ra'ayin komawa Chelsea.
Chelsea dai ta jima tana neman mai tsaron ragar da za ta yi dace da.