window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

KAI TSAYE, Darajar Yamal ta kai £340m ga duk wadda za ta saye shi

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labaran wasanni a faɗin duniya na ranakun 31 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ƴanwasa 10 mafiya daraja a duniyar ƙwallon ƙafa

    Yamal

    Asalin hoton, Getty Images

    Matashin ɗanwasan Barcelona, Lamine Yamal ka iya kai darajar kusan fam miliyan 340, idan za a sayar da shi, a cewar wata ƙungiya a ƙasar Switzerland mai nazari kan darajar ƴan wasa.

    A wata ƙididdiga ta daban, cibiyar sanya idanu kan ƴanwasa ta CIES, ta ƙiyasta cewa ɗan wasan mai shekara 17 zai kai darajar euro miliyan 400 - kusan ninkin abin da aka sayar da Barcelona ta sayar da Neymar - euro miliyan 222 - ga PSG a 2017, mafi tsada a lokacin.

    Matashin ɗan Sifaniya ya kasance na biyar cikin jerin matasan ƴanƙwallo da suka haska a kakarsu ta farko a gasar La Liga, a lokacin yana da shekara 15 da wata tara.

    Ya zarta Messi- da ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau takwas - da ƙwallo 23 a daidai waɗannan shekaru.

    Ga jerin ƴan wasan 10 da suka fi daraja:

    1. Lamine Yamal (Barcelona) £340m.

    2. Erling Haaland (Man City) £200m.

    3. Jude Bellingham (Real Madrid) £197m.

    4. Kylian Mbappe (Real Madrid) £162m.

    5. Jamal Musiala (Bayern Munich) £130m.

    6. Pedri (Barcelona) £121m.

    7.Vinicius Junior (Real Madrid) £109.7m.

    8. Cole Palmer (Chelsea) £106.5m.

    9. Julian Alvarez (Atletico Madrid) £106m.

    10. Florian Wirtz (Bayer Leverkusen) £103m.

  2. Fulham ta sanar da korar William da Carlos Vinicius

    Fulham

    Asalin hoton, Getty Images

    Fulham ta sanar cewar Willian da Carlos Vinicius za su bar kungiyar bayan da yarjejeniyarsu za ta kare a karshen watan Yuni.

    Willian, wanda ya sake komawa Fulham a farkon shekarar nan ya buga wasa 79 tun bayan da ya fara buga mata tamaula a 2022 a karon farko.Shi kuwa Vinicius zai yi ban kwana da Fulham, bayan da suke su uku a gurbin da yake bugawa, idan ka hada da Raul Jimenez da Rodrigo Muniz.

    Fulham ta yi wa kyaftin dinta Tom Cairney tayin karin kwantiragi, wanda ake alakanta shi da zai koma Wrexham, wadda za ta buga Championship a badi.

    Sauran da aka yi wa tayin tsawaita kwantiragi a Fulham sun hada da Kenny Tete da matashi Luc De Fougerolles da Callum Osmand da kuma Lemar.

  3. Super Eagles

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaya daga cikin masu hannun jari a Crystal Palace, John Textor, wanda shi ke da ƙungiyar Faransa ta Lyon, na shirin sayar da kaso mai yawa na hannun jarinsa. (Mail)

    Mai tsaron raga a Ingila, Aaron Ramsdale ya tattauna kan yiwuwar tafiya West Ham daga Southampton. (Talksport)

    Ɗan wasan tsakiya a Croatia, Luka Modric mai shekara 39, ya amince ya koma AC Milan idan ya bar Real Madrid. (Gianluca di Marzio, via Football Italia)

  4. Fabregas ya mayar da hankali kan horar da Como

    Cesc Fabregas ya ce hankalinsa gabaki daya yana Como, bayan da ake alakanta shi da zai karbi aikin kociyan Inter Milan, sakamakon da Simone Inzaghi ya ajiye aikin bayan da Paris St Germain ta doke su 5-0 ranar Asabar ta lashe Champions Legue a Jamus.

    Kungiyoyi da dama na son zawarcin Febregas, tsohon dan wasan Arsenal da Barcelona da Chelsea, bayan da ya kare a mataki na 10 a teburin Serie A da Como a Serie A da aka kammala.

    Wasu rahotanni daga Italiya na cewa Inter za ta maye gurbin Inzaghi da Fabregas, domin tunkarar Club World Cup da za a yi a Amurka daga ranar 14 ga watan Yuni.

  5. Wasannin da za a buga ranar Alhamis

    UEFA Nations League karawar daf da karsheSpain da

    FIFA World Cup bangaren AsiaGroup A

    • Korea DPR da Kyrgyz Republic
    • Qatar da Iran
    • United Arab Emirates da Uzbekistan

    Group B

    • Iraq da South Korea
    • Kuwait da Palestine
    • Oman da Jordan

    Group C

    • Australia da Japan
    • Bahrain da Saudi Arabia
    • Indonesia da China PR

  6. Middlesbrough ta kori kociyanta Michael Carrick

    Carrick

    Asalin hoton, Getty Images

    Middlesbrough ta kori Michael Carrick, bayan kaka biyu da rabi yana jan ragama.

    Tsohon dan wasan tawagar Ingila, mai shekara 43 ya karbi aiki a kungiyar dake buga Championship a Oktoban 2022 a karon farko da ya fara aikin kociya.

    Ya ja ragamar kungiyar ta buga wasan cike gurbin shiga Premier League a 2022-23, wadda ba ta samu gurbin ba, daga nan ta kasa shiga cikin yan shidan farko a kaka biyu da ta wuce.

    Mataimakin Carrick, Jonathan Woodgate da dan uwansa Graeme Carrick duk sun bar kungiyar.

    Bayan da aka kori Carrick, kenan kungiya 17 daga 24 masu buga Championship sun sauya mai horar da tamaula tun daga Agustan bara.

  7. Sifaniya za ta kara da Faransa a wasan daf da karshe na Uefa Nations League

    Lamine Yamal

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Sifaniya ta yi atisaye ranar Laraba a sansaninta, Las Rozas ahead a shirin wasan daf da karshe da Faransa a UEFA Nations League.

    A yammaci ne Sifaniya za ta je Stuttgart inda koci, Luis de la Fuente da Pedri za su tattauna da yan jarida.

    Sifaniya da Faransa za su kece ranar Alhamis, domin samun wadda za ta buga wasan karshe a Uefa Nations League.

    Ranar Laraba za a fara wasan daf da karshe tsakanin Jamus da Portugal.

  8. Live Page

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai buga gaba a Brentford da Kamaru, Bryan Mbeumo, ɗan shekara 25 na fatan samun albashin £250,000 a kowanne mako - ninki har sau biyar kan abin da ake ba shi yanzu - idan ya koma Manchester United. (Times - subscription required)

    Inter Milan ta tuntubi kocin Como kan ko tsohon ɗan wasan tsakiya a Sifaniya, Cesc Fabregas zai maye gurbin mai horas da su Simone Inzaghi, da ya tafi. (Sky Sports Italia - in Italian)

    Chelsea tayi tuntuba kan ɗan wasan Faransa mai shekara 29, Mike Maignan, wanda yake da sauran kwantiragin shekara guda a AC Milan. (Talksport)

  9. Tottenham za ta sayar da Son idan an taya da tsoka

    Son Hueng min

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta ce za ta iya sayar da Son Heung-min ga duk kungiyar da ta yi tayi mai tsoka.

    Ana alanta son da kungiyar Saudiyya, wadan da suka taya shi da tsoka a kaka biyu da ta wuce, wanda ya zabi taka leda karkashin sabon koci Ange Postecoglou.

    A watan jiya kyaftin Son ya ja ragamar Tottenham ta lashe Europa League, bayan cin Manchester United 1-0 a Sifaniya.Ana ta tantama kan makomar Son, wanda zai shiga kakar karshe a yarjejeniya da Tottenham.

    A watan Yuli Son zai cika shekara 33 da haihuwa, wanda ke fama da jinya a kakar da ta wuce, amma Tottenham ta ce tana jiran tayi mai tsoka.

    Tottenham na shirin ziyara Koriya ta Kudu, domin yin atisayen tunkarar kakar badi, karo na uku a kaka hudu da kungiyar da ke buga Premier ke zuwa kasar.

    Son, wanda ya je buga wa kasarsa tamaula ya ci kwallo 11 a Tottenham a kakar da ta wuce, wannan shi ne karon farko da bai zura kwallaye ba da yawa a raga tun bayan da ya koma kungiyar da taka leda.

    Bayan son da ake tantama kan makomarsa, haka shima koci, Ange Postecoglou na fuskantar matsi, bayan da Tottenham ta kare a kaka mafi muni a tarihi a Premier League.

  10. Jorginho da Tierney suna daga cikin 20 da Arsenal ta kora

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Jorginho da Kieran Tierney za su bar Arsenal, bayan da kwantiraginsu ya kare ranar 30 ga watan Yuni, kamar yadda Gunners ta fitar da sunayen yan wasan da ta kora.

    Jorginho dan wasan tawagar Italiya, wanda ke daf da rattaba hannu a Flamengo ta Brazil, ya koma Emirates daga Chelsea a Janairu 2023, wanda ya yi mata wasa 79.

    Shi kuwa Tierney dan kwallon tawagar Scotland, ya koma Arsenal daga Celtic kaka shida da ta wuce, ya buga wasa 170 daga baya ya je aro a Real Sociedad a kakar 2023-24.

    Bayan da ya koma Emirates ya buga wasa 13 a Premier League, zai sake komawa Celtic.

    Shima yarjejeniyar Thomas Partey za ta kare a karshen watan Yuni, amma Arsenal na tattaunawa da shi don tsawaita zamansa a Emirates.

    Shi kuwa Raheem Sterling, wanda ya buga wasannin aro 28 a Arsenal, zai sake komawa Chelsea da taka leda.

    Cikin wadanda Arsenal ta kora har da matasan kungiyar yan kasa da shekara 18 da 21 da wasu daga matan dake yiwa kungiyar wasanni.

  11. Messi ya yi atisaye a tawagar Argentina

    Lionel Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Lionel Messi ya yi atisaye a tawagar Argentina, wadda ke shirin buga wasan neman shiga gasar kofin duniya da Chile.

    Argentina mai rike da kofin duniya karkashin koci, Lionel Scaloni, za ta fuskanci wasa biyu masu zafi a shirin da take na kare kofinta a Amurka da Mexico da Canada a 2024

    Argentina za ta fafata da Chile a Santigo ranar Alhamis daga nan ta karbi bakuncin Colombia a Buenos Aires a Monumental ranar 10 ga watan Yuni.

    Argentina ce ta daya a rukunin Kudancin Amurka da maki 31 a wasa 14 da cin wasa 10 da canjaras daya aka doke ta uku daga ciki.

  12. Cagliari ta kori kociyanta, Davide Nicola

    Davide Nicola

    Asalin hoton, Getty Images

    Cagliari ta sallami kociyanta, Davide Nicola wanda ya hana kungiyar barin Serie A a kakar da aka kammala kamar yadda kungiyar ta sanar ranar Laraba.

    Nicola ya karbi aiki a cikin watan Yuli, bayan maye gurbin Claudio Ranieri, ya kuma sa hannu kan yarjejeniyar kaka biyu da ta kare a mataki na 15 a kasan teburin Serie A da tazarar maki biyar tsakani da yan karshen teburi.

    Nicola ya yi suna wajen ceto kungiya daga faduwa daga gasa, cikinsu har da Empoli da Salernitana da Torino da kuma Genoa dukkansu kungiyoyin Italiya.

  13. Hueng Son Min

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan gaba a Tottenham, Son Heung-min mai shekara 32 ya kasance wanda ƙungiyoyin Saudiyya ke rubibi a yanzu. (Telegraph)

    Mai buga gefe a Manchester United, Jadon Sancho na iya komawa Saudiyya sakamakon yadda ƙungiyoyi irinsu Al-Hilal da Al-Ittihad da Al-Nassr ke zawarcin matashin mai shekara 25 daga Ingila. (Mirror)

    Ɗan wasan tsakiya a Real Sociedad, Martin Zubimendi mai shekara 26 na nuna rashin tabbas kan tafiyarsa Arsenal, inda ɗan wasan na Sifaniya ke duba zaɓin da yake da shi. (Radio Nacional de Espana, via Metro)

  14. Alcaraz ya kai daf da karshe a French Open

    Mai rike da kofin French Open, Carlos Alcaraz ya kai zagayen daf da karshe, sakamakon da ya yi waje da Tommy Paul a gasar ta Roland Garros.

    Dan kasar Sifaniya ya kai zagayen gaba ne a cikin minti 53 a fafatawar da suka yi a birnin Paris.

    An kuma yi waje da Paul a zagayen kwata fainal, bayan da aka doke shi da ci 6-0 6-1 6-4 victory.

    Alcaraz zai fafata da mai shekara 23, Lorenzo Musetti a zagayen daf da karshe.

    Alcaraz

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Ina Luca Modric zai koma da taka leda?

    Luca Modric

    Asalin hoton, Getty Images

    Yarjejeniyar Luka Modric za ta karkare a Real Madrid a karshen watan Yuni.

    Dan wasan tawagar Crotia ya taka rawar gani a kungiyar Sifaniya, shi ne kan gaba a yawan lashe kofuna a Real Madrid.

    Tun bayan da Real Madrid ta dauki dan wasan daga Tottenham ya zama kashin bayan kungiyar, mai kyautar Ballon d'Or mai taka leda a daga tsakiya.

    Real Madrid, wadda ta yi ta biyu a teburin La Liga a kakar da ta kare za ta buga Club World Cup a Amurka - ko Modric zai buga mata wasannin.

    Za a fara Club World Cup daga 14 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.

    Wasu rahotannin na cewar kyaftin din Real Madrid zai koma taka leda a gasar Serie A a kakar badi.

  16. Manchester City ta sayi Reijders daga AC Milan

    AC Milan

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City ta amince za ta biya AC Milan (£46.3m) domin sayen dan wasan tawagar Netherlands, Tijjani Reijnders.

    Mai shekara 26, zai saka hannu kan yaejejeniyar kaka biyar a kungiyar Etihad.

    City na fatan kammala cinikin, domin Reijders ya samu buga mata Club World Cup da za a fara ranar 14 ga watan Yuni a Amurka.

    Idan har ya koma Etihad, kungiyar za ta magance gurbin da Mateo Kovacic ke buga wa, wanda ya ji rauni ba zai samu zuwa Amurka ba.

    Watakila Kevin de Bruyne ya bi Manchester City Club World Cup, duk da ana alakanta shi da Napoli, wadda ta lashe Serie A a kakar da aka kammala.

  17. Watakila Chelsea ta dauki Gittens

    Jamie Gittens

    Asalin hoton, Getty Images

    Guardian ta bayar da rahoton cewar Chelsea na duba yadda za ta dauki dan wasan Borussia Dortmund, Jamie Gittens.

    Gittens ya taka leda a makarantar horar tamaula ta Chelsea da Reading da Manchester da kuma Borussia Dortmund.

    Mai shekara 20 mai taka leda a tawagar Ingila ta matasa yan kasa da shekara 21 zai kai £50m.

    Gittens ya ci kwallo 12 a dukkan karawar da ya yi wa Dortmund a 2024-25

  18. Inter Milan da Simone Inzaghi sun raba gari a tsakaninsu

    Inzaghi

    Asalin hoton, Getty Images

    Inter Milan da Simone Inzaghi sun raba gari a tsakaninsu, bayan da kungiyar Italiya ta sha kashi a wasan karshe a Champions League da Paris St Germain ta lashe kofin a karon farko a tarihi.

    Mai shekara 49, wanda ya karbi aiki a 2021, ana alakanta shi da zai koma horar da tamaula a babbar gasar tamaula ta Saudiyya da Al-Hilal.

    Inzaghi ya lashe Serie A da Coppa Italia biyu da Supercoppa Italia uku a kungiyar ta san Siro.

    Sau biyu yana kai Inter wasan karshe a Champions League, inda ya sha kashi a hannun Manchester City da ci 1-0 a 2022-23 da wanda PSG ta dura musu 5-0 ranar Asabar.

    Inzaghi ya bar Inter, wadda za ta buga Club World Cup da za a fara a Amurka daga 14 ga watan Yuni da kungiya 32 za su kece raini a karon farko.

    Haka itama Al-Hilal za ta fafata a Club Worl Cup.

  19. Ko kungiyar Serie A za ta yi zawarcin Rasmus Hojlund

    Rasmus Hojlund

    Asalin hoton, Getty Images

    Gazzetta dello Sports ta ce watakila Inter Milan za ta nemi a bata aron mai shekara 22, Rasmus Hojlund daga Manchester United.

    Dan wasan tawagar Denmark ya koma Old Trafford daga Atalanta mai buga Serie A kan £72m a Agustan 2023.

  20. Wasu rahotanni na cewar Mitrovic zai koma buga Premier

    Mitrovic

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu rahotannin na cewar watakila Manchester United da Everton da West Ham za su yi zawarcin Aleksandar Mitrovic.

    Tsohon dan wasan Fulham mai shekara, 30, ya ci kwallo 68 a wasa 79 tun bayan da ya koma Saudiyya da taka leda.

    Al-Hilal ta amince za ta sayar da Mitrovic ko kuma ta bayar da aronsa.