Majalisar dokokin Senegal ta amince da gurfanar da tsoffin ministocin ƙasar biyar a gaban kotu
Majalisar dokokin Senegal ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da gurfanar da tsoffin ministocin ƙasar biyar gaban wata kotu ta musamman don fuskantar tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa.
Ana zarginsu da yin almubazzaranci da kuɗaɗen da aka ware domin yaƙi da cutar ta Covid-19 daga shekarar 2020 zuwa 2021.
'Yan adawar sun yi Allah wadai da tuhumar da ake yi wa ministocin.
Ministocin biyar sun yi aiki a tsohuwar gwamnatin tsohon Shugaba Macky Sall - wanda shugaba mai ci Bassirou Diomaye Faye ya kayar.