Halin ƙunci da rikcin Indiya da Pakistan ya jefa fararen hula

Wani Sojan  Indiya na sanya ido daga bayan wata katangar waya.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani sojan Indiya na sanya ido daga bayan wata katangar waya a Srinagar, babban birnin yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya

Mohammed Waheed na tsaka da yin bacci a gidansa a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin mulkin Pakistan da sanyin safiyar ranar Laraba wani abun fashewa ya girgiza gidansa.

"Kafin mu gane me ke faruwa, ƙarin wasu makamai masu linzami suka sake sauka, inda suka jefa mutane cikin firgici, da hautsini," kamar yadda ya shaida wa BBC, yana mai cewa ya zabura ya tashi daga kan gadon da yake kwance ya rugo waje tare da iyalansa da maƙwabtansa.

"Yara na ta koke-koke, mata na ta gudu don samun inda za su iya tsira ko fakewa."

Mista Waheed na mazaunin Muzaffarabad ne babban birnin Kashmir da ke ƙarashin ikon Pakistan. Ɗaya ne cikin wurarare uku da Indiya ta kai wa hari a ranar Laraba.

Sojojin Indiya sun ce sun kai harin ne maratani kan harin da aka kai yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikonta, inda ya yi sandiyar mutuwar mutum 26. Sun zargi sojojin ƴan tawayen Pakistan da kai harin, inda suka zargi gwamnatin Pakistan da goya musu baya, zargin da Pakistan ɗin ta sha musantawa.

BBC ta tattauna da wasu da suka shaida lamarin a yankin na Kashmir da ke tsakanin Indiya da Pakistan.

Pakistan ta ce fararen hula 26 aka halaka, yayin da mutum 35 suka ji raunuka sakamakon harin.

Sojojin Indiya sun ce aƙalla mutum 10 ne suka mutu sakamakon makaman atilare da Pakistan ta harba ɓangaren Indiya na yankin Kashmir.

'An halaka su suna hada shayi'

Ruby Kaur tana zaune a lardin Poonch na Indiya, wadda hukumomin yankin suka gano a cikin Indiyawan da aka kashe.

Kawunta Buava Singh ya shaida wa BBC cewar makami mai linzamin da aka harba kusa da gidanta da misalin ƙarfe 1:45, shi ne ya halaka ta nan take, sannan ya raunata ƴarta.

"Mijinta na fama da rashin lafiya, ta tashi ta hada masa shayi, a lokacin da bam ɗin ya sauka a kusa da gidan nasu," a cewarsa.

Ya ƙara da cewar harin makamai masu linzamin da aka kai da safiyar ranar Larabar abu ne "da ba mu taɓa gani ba". Singh ya ce babu wani wuri na buya a yankin, wanda hakan ya tilasta wa mazauna buya a gidajensu.

"Wani banagre na kwanson bam ɗin ya buge ta aka. ta zubar da jini sosai. mun garzaya ta da asibiti da ke kusa damu, anan aka tabbatar dma da cewar ta mutu," in ji Mr. Singh.

Shi ma wani mazaunin yankin na Poonch, ya ce ya ji ƙarar fashewar tsawon sao'i na daren ranar Laraba.

"Ya kasan ce yanayi na kaɗuwa a ɗaukacin birinin, sannan yankin na kusa da yankin da ake kula da shi," Dr Zamrood Mughal ya shaida mana ta waya.

"Mutane basu iya yin bacci ba, a ɗukacin daren. Mutane sun bar gidajen su, suna tserewa zauwa wajen tsira. wani makamin mai linzami da aka harbo, kusa da ofishin hukumar kula da gandun daji, ya lalata ofishin da sauran gine-gine da ke yankin.

Wani hoto na nuni da yadda masallacin Bilal ya rushe bayan kai harin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani ɓanagre na masallacin Bilal da ake iya gani ya lalace bayan harin da Indiya ta kai Muzaffarabad

'Fargabar abin da ka iya faruwa nan gaba'

Muhamamd Younis da ke zaune a yankin Kashmir na Pakistan, ya bayyana yadda makamai masu linzami huɗu da Indiya ta harba suka sauka a harabar ofhsin hukumar ilimi da ke Nangal Sahadan, inda ya lalata wani masallaci.

"Akwai wata makaranta da kwaleji ta yara, da wurin kwanan ɗalibai, da cibiyar kula da lafiya a wurin," in ji shi.

"Makaman masu linzami na farko an harbo su ne a jere, yayin da na hudu aka jinkirata harbo shi kamar mintuna biyar zuwa bakwai."

Yayin da ake dakon fara aikin ceto, mazauna yankin sun ce suna hasashen ƙaruwar ta'azzarar lamura, yayin da suke cikin kaɗuwar rashin sanin abin da zai faru nan gaba.

Shi ma wani takwaransa da ke zaune a yankin Shahnawaz da ke Muzaffarabad, ya ce shi da iyalansa yanzu, "na cikin mastanancin neman wuri mara haɗari don tsare rayukansu"

"Muna jiran mu ga abun da zai faru, amma yanzu muna cike da tsoro saboda yiwuwar ƙara ta'azara al'amarin."

Indiya ta nanata cewar matakin na ta na ranar Laraba, ta ce "tsararuru ne kuma iyakantatu, ba tare da ƙara ta'azara ba",

Mr. Waheed ya shidawa BBC cewar har yanzu ya kasa fahimtar dalialn da yasa aka kai harin kan masallacin nasu ba da ya haifar da asarar "gwammon maza da mata" unguwar tasu da ke Muzaffarabad.

"Abu ne mai wuyar fahimta,"in ji shi. "Masallaci ne kamar ko ina da ake sallah sau biyar a cikinsa . bamu taɓa ganin wani abun na zargi da ake aiktawa ba a cikinsa ba."

Delhi ta jaddad cewar harin da ta kai, ta kai shi ne kan gine-ginen da ta ke hasashen na ƴan ta'adda ne d suka zaɓa, "bayan wasu bayanan sirri da ta tattara".

Amma sai dai mazuan yankuanan da ke ƙarƙshin ikon Pakistan sun ce masallatansu da muhallanasu, na daga cikin wuraren da aka kai harin.

Mr. Waheed ya kasa fahimtar dalialn da yasa aka kai harin kan masallacin nasu ba da ya haifar da asarar "gwammon maza da mata" unguwar tasu da ke Muzaffarabad.

"Abu ne mai wuyar fahimta,"in ji shi. "Masallaci ne kamar ko ina da ake sallah sau biyar a cikinsa . bamu taɓa ganin wani abun na zargi da ake aiktawa ba a cikinsa ba..