Waiwaye: Yadda ambaliya ta kashe mutum sama da 100 a Neja da hana Sheikh Gumi aikin Hajji
Wannan maƙala ce da ke kawo muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Neja sun kai 151

Asalin hoton, Adamu Ngulde
Alkaluman waɗanda ambaliyar ruwa ta kashe a jihar Neja ya kai mutum 151, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa na jihar.
Masu aikin ceto sun ce sun gano gawawwaki da dama.
Jami'ai a yankin Mokwa wurin da lamarin ya faru, sun yi gargaɗin cewa ƙarin mutane na cikin barazana a birnin.
An shafe tsawon sa'o'i ana tafka mamakon ruwan sama a yankin ranar Laraba, inda ruwa ya tafi da gidaje aƙalla 50.
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya a kusan rabin jihohin ƙasar 36.
Sama da mutum 1,200 ne suka mutu sakamakon ambaliya a bara sannan sama da miliyan ɗaya suka ɗaiɗaita, a ambaliyar da ba a taɓa gani ba cikin gomman shekaru.
Sojoji sun ce sun hallaka ƴan ta'adda 60 a jihar Borno

Asalin hoton, Nigerian Army
Dakarun sojin Najeriya na Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan ta da ƙayar-baya sama da 60 a wani artabu da suka yi a jihar Borno.
Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar ranar Juma'a, ta ce dakarun sun samu nasarar kashe ƴan ta'ddan ne bayan bata-kashi da suka yi daddare a yankin Bita na jihar.
Sanarwar ta ce ƴan ta da ƙayar-bayan sun far wa sojojin birget 26 ne da misalin karfe 1:09 na asubahin yau Juma'a, inda dakarun Haɗin-Kai suka mayar da martani da hare-hare ta sama da kuma ƙasa kan ɓata-garin.
"Sojoji sun kaddamar da hare-haren sama da kuma ta ƙasa kan sansanonin ƴan ta da ƙayar baya a yankin Bita na jihar Borno da asubahin yau Juma'a, lamarin ya kai ga hallaka aƙalla 60 daga cikinsu," a cewar sanarwar sojojin.
Kotu ta yanke wa matashin da ya ƙona masallata a Kano hukuncin kisa

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne wata babbar kotun shari'ar musulunci da ke Kano ta yanke wa Shafi'u Abubakar, matashin nan da aka tuhuma da ƙona masallata hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun shi da aikata laifin kisan.
Al'amarin da ya faru ne a gari Gadan da ke ƙarƙashin Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano.
A ranar 15 ga watan Mayun 2024 ne matashin ya zuba fetur sannan ya cinna wa mutanen wuta yayin da suke yin sallar Asuba, lamarin da ya janyo da dama daga cikinsu suka kone sannan wasu suka mutu.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne sanadiyyar rikici kan rabon gado tsakaninsa da ƴan uwansa.
Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan Boko Haram, Abu Fatima

Asalin hoton, X/Defence HQ
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram wanda ake kira Amir Abu Fatima.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X, ta ce an samu nasarar kashe Abu Fatima ne a wani samame da dakarun Haɗin-Kai suka kai yankin Kukawa na jihar Borno.
Sojojin sun ce Abu Fatima na cikin mutanen da rundunar ke nema ruwa a jallo, inda ta ƙuduri aniyar bai wa duk wanda ya bayar da rahoton inda za a kama shi ladan naira miliyan 100.
"Abu Fatima ya samu munanan raunuka lokacin da ake ba ta-kashi kafin mutuwarsa. An kuma kashe mataimakinsa da wasu ƙwararru kan ababen fashewa da dama har ma da sauran ƴan ta'adda da suke tare da shi," in ji sanarwar.
Talauci da tashin farashi sun addabi talakan Najeriya - Buhari

Asalin hoton, Bashir Ahmad/Twitter
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu murnar cikar shekara biyu a kan karagar mulkin ƙasar.
A cikin wani saƙo da mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, da kuma ke ɗauke da sa hannunsa, Muhammadu Buhari ya roƙi al'umma da su ci gaba da ba gwamnatin jam'iyyar APC cikakken goyon baya.
Ya ce a daidai lokacin da jam'iyyarsu da kuma gwamnatin ke wannan bikin, ya dace 'yan Najeriya su san da cewa tsarin shugabanci abu ne da ke ci gaba da gudana.
Ya kuma ce sannu a hankali za a cimma nasara a sabbin tsare-tsaren gwamnati mai ci, idan an saka haƙuri domin ba abu ne da za cimma a dare ɗaya ba.
Saudiyya ta hana Gumi shiga ƙasarta domin aikin Hajjin bana

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun hana babban malamin addinnin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi shiga ƙasar domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sheikh Gumi wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnatin Saudiyya bayan ta ba shi bizar shiga ƙasar domin aikin Hajji amma kuma sai ba a ba shi damar shiga Madina domin fara aikin ibada ba.
"Bisa waɗansu dalilai saboda ra'ayi na kan siyasar duniya, hukumomi a Saudiyya ba sa son kasancewata a Hajji duk da sun ba ni biza," in ji Sheikh Gumi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ƙara da cewa "Ina godiya ga hukumomi a Najeriya waɗanda suka sha alwashin tuntuɓar hukumomin Saudiyya a kan wannan lamarin."
Fiye da mutum 10,000 sun mutu ƙarƙashin mulkin Tinubu - Amnesty International

Asalin hoton, Tinubu/X
Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan nan ya nuna cewa, cikin shekaru biyu da gwamnatin Tinubu ta hau mulki, an kashe aƙalla mutum 10,217 a hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihohi daban-daban.
Jihohin sun haɗa da Benue da Edo da Katsina da Kebbi da Plateau da Sokoto da Zamfara.
Jihar Benue ce ke da mafi yawan adadin mutanen da aka kashe – inda ya kai har mutum 6,896, sai Jihar Plateau da mutum 2,630.
Kotu ta ɗaure Murja Kunya wata shida

Asalin hoton, fb/Murja Kunya
Wata kotun tarayya da ke zama a Kano ta ɗaure matashiyar nan ƴar TikTok, Murja Kunya tsawon wata shida a gidan yari, bayan samun ta da laifin cin tozarta takardar kuɗi ta naira.
Alƙalin kotun mai shari'a Simone Amobeda ya ce kotun ta kama Murja da laifin watsa takardar naira da kuma taka ta, a wani lokaci cikin watan Disamban bara, laifin da ya karya tanadin sashi na 21 ƙaramin sashi na ɗaya na dokar nannam namkin Najeriya.
Kotun ta yankewa Murja Kunya hukuncin zaman gidan yari na wata shida, ko kuma zaɓin biyan tarar naira 50,000.
Kotun ta kuma umarci Murja ta zamo jakadiyar hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC da kuma babban bankin Najeriya CBN, ta hanyar wayar da kan jama'a game da daina cin mutumcin naira.
An kama mutane 41 kan zargin kashe DPO a Kano

Asalin hoton, FB/Abdullahi Haruna Kiyawa
Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan baturen ƴansanda na Rano, CSP Baba Ali.
Kwamishinan ƴansanda a jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce kisan jami'in nasu babban abin takaici da tashin hankali ne.
Kisan jami'in ya janyo suka daga ɓangarori da dama, musamman a lokacin da bidiyon mummunan al'amarin ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta.
A cikin sanarwar da rundunar, reshen jihar Kano ta fitar a yau Alhamis, kwamishinan ƴansandan ya ce rundunar tana yin duk abin da ya dace domin ganin an gurfanar da masu hannu a kisan jami'in nata da kuma tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata.