Dole a yi bincike kan kisan Falasdinawa a wajen rabon tallafi — Antonio Guterres

Antonio Guterres

Babban sakatare a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga da a gudanar da cikakken bincike a kan kisan Falasdinawa a cibiyar da ake rabon kayan tallafi a Gaza.

Ganau sun rawaito cewa an bude musu wuta a yayin da suke jiran abinci daga cibiyar da ke Rafah inda gidauniyar nan da ke samun goyo bayan Amurka da Isra'ila ke rabon tallafi.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce asibinta ya karbi mutum 179 da suka samu rauni inda 21 daga cikinsu sun mutu.

Hukumar tsaro ta farin kayan Hamas ta ce mutum 31 ne suka rasa ransu.

A ranar Lahadi, 1 ga watan Yunin 2025, rundunar sojin Isra'ila ta musanta cewa dakarunta sun bude wa fararen hula wuta a kusa da kuma harabar inda ake rabon kayan tallafi tana mai cewa duk wani rahoto akan cewa sojojinta sun kashe mutane a wajen ba gaskiya bane

Gidauniyar ta ce ya kamata a rinka tabbatar da abu kafin a furta.

Isra'ila ta hana kafafan yada labarai ciki har da BBC shiga cikin Gaza abin da ya sa tabbatar da abubuwan da ke faruwa a Gazan zai yi matukar wuya.

Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar cikin wata sanarwa yace " Ya kadu da rahotannin da ke cewa an kashe tare da raunata Falasdinawa a yayin da suke jiran tallafi a Gaza."

Ya kara da cewa," Ina mai kira da gaggauta gudanar da cikakken bincike akan wannan lamari domin a gano ainihin wanda ya aikata wannan aika aika."

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta mayar wa da babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya kakkausan martani a wani sako da ta wallafa a shafinta na X inda ta soke shi tana mai cewa mai ya sa bai ambaci Hamas ba sai sojojin Isra'ila.

A jiya Litinin shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, ya shaida wa BBC cewa hanyar da ake bi wajen rabon kayan tallafi ba daidai ba ce kuma ba za a amince da ita ba.

Ya ce " Ina ganin abin da ake nunawa bai kamata ba ga fararen hula.Yanzu ace mutanen da ke matukar bukatar abinci da maganni kusan watanni uku wai sune zasu rinka gudu don karbar abincin sannan ga wulakanci kafin su samu");