Ko Tinubu na son mayar da Najeriya mai bin tsarin jam'iyya ɗaya ne?

Tinubu

Asalin hoton, Onanuga/X

Komawar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori jam'iyyar APC a tsakiyar makon da ya gabata ya sa masana kimiyyar siyasa da wasu daga ɓangaren hamayya fara tuhumar shugaba Bola Tinubu da yunƙurin mayar da Najeriya kan tsarin jam'iyya ɗaya.

Bugu da ƙari, sauya sheƙar da tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya na PDP, Dr Ifeanyi Okowa zuwa jam'iyyar mai mulki da kuma iƙrarin da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya yi cewa zai bai wa Bola Tinubu goyon baya, sun ƙara sanya fargabar tattara masu hamayya a ƙarƙashin jam'iyya guda.

Hakan ne kuma ya sa mai magana da yawun gwamnatin, Bayo Onanuga ya mayar da martanin cewa "ƙarya ce da shaci-faɗi irin na ƴan siyasa".

A shafinsa na X, Bayo Onanuga ya ce "shure-shure ne da masu hamayya ke yi sakamakon gaza cimma haɗaka a tsakaninsu."

Me hakan ke nufi?

Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen jami'a ya ce duk da irin wawason da jam'iyya mai mulki ta APC ke yi a yanzu haka ba ya nuna cewa jam'iyyar ka iya zama jam'iyya ɗaya tilo a Najeriya.

"Duba da cewa har yanzu ana jin motsin sauran jam'iyyun na hamayya da ma ƙoƙarin haɗa da masu hamayyar ke yi na nuna cewa ba a ɗauki hanyar komawa tsarin jam'iyya ɗaya a ƙasar ba.

Har yanzu jam'iyyar APC ba ta yi shekarun da jam'iyyar PDP mai hamayya ta yi a baya ba tana mulki. PDP ta kwashe shekaru 16 kuma ƴan jam'iyyar sun ta yin iƙrarin cewa ba za su bar wata jam'iyya ta yi mulki ba. Amma bayan haɗaka da abokan hamayya suka yi daga ko'ina sai ga shi sun kayar da ita. To ita ma APC hakan ka iya faruwa a kanta." In ji Malam Kabiru Sufi.

To sai dai Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja ya ce nan gaba idan ba a yi taka tsan-tsan ba Najeriya za ta iya komawa ƙasa mai jam'iyya ɗaya.

"Wannan gagarumin koma-baya ne ga ga ɓangaren adawa, kuma koma-baya ne ga tsarin dimokuraɗiyya saboda hakan na ƙara wa jam'iyya mai mulki ƙarfi, kuma dimokraɗiyya ba ta ƙarko sai da jam'iyyun adawa masu ƙarfi," in ji Farfesa Kari.

Farfesa Kari ya ce illar mamaye masu hamayya da mayar da su ƙarƙashin jam'iyya mai mulki ita ce "za a kai yanayin da gwamnati mai mulki za ta rinƙa gudanar da duk abubuwan da take son yi ba tare da masu hamayya sun taka mata burki ba."

Shi ma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa , ya ce a yanzu babu wata hamayya da ta rage a fagen siyasar Najeriya.

A tattaunawarsa da BBC ya ce 'yan siyasar ƙasar su ne ke hamayya da kansu da cutar juna game da neman muƙamai ba tare da sun anfana wa talakawa wani abu ba.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa duk wannan sauya sheƙa da 'yan siyasar na ɓangaren hamayya ke yi suna tafiya jam'iyya mai mulki ba don su amfanin talaka suke yi ba, face don kansu suke yi, saboda haka ya ce siyasar hamayya ta matu a ƙasar a yanzu - babu aƙida.

Mene ne tsarin jam'iyya ɗaya?

Tsarin jam'iyya ɗaya na nufin wani tsarin mulki wanda jam'iyya mai mulki ke da ƙarfin faɗa a ji, inda sauran jam'iyyun ke fuskantar barazanar haramtawa ko kuma rashin ƙarfin shiga a fafata da su a zaɓe.

"Tsari ne da ya yarda da zaman jam'iyya ɗaya a ƙasa: ita ce jam'iyyar da aka sani a gwamnatance. Ita ce jam'iyya guda ɗaya da ke shiga zaɓe. Ita ce kuma jam'iyyar da idan har kana son riƙe wani muƙami to sai ka kasance a cikinta.

A gwamnatance ba a yarda da duk wata jam'iyya ba bayan wannan. Wani lokaci ma kasancewar jam'iyyun kan zama laifi." In ji Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano.

Sai dai Malam Kabiru Sufi ya ce yawancin ƙasashen da aka samun irin wannan tsari na farawa ne da tsarin da aka sani na jam'iyyu guda biyu ko fiye da haka.

"Yau da gobe sai a samu jam'iyya guda ɗaya ta fi ƙarfin kowa har ta kai ga an sauya tsarin mulkin ƙasa da zai haramta wasu jam'iyyun."

Mece ce mafita?

Farfesa Kari ya ce: "'Yan'adawa su yi gagarumin yunƙuri domin ganin hakan bai ci gaba da faruwa ba, kuma su ma su fara zawarcin manyan 'yansiyasa daga APC ganin cewa ita ma jam'iyyar mai mulki tana fuskantar korafe-korafe da rashin gamsuwa da yadda abubuwa ke wakana."

"Ina da tabbas cewa ƴan Najeriya za su yi baƙin ciki idan har ba su da wani zaɓi sai jam'iyyar APC a zaɓen 2027," in ji Farfesa Kari.

Tuni tsohon Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya fara aikin zawarcin manyan 'yan adawa a jam'iyyarsa ta SDP, wadda ya koma a watan Maris bayan ya bar APC.

Tsohon ɗantakarar shugabancin ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa yana tattaunawa da sauran 'yan adawa domin yin haɗaka, amma PDP ta ce ba ta cikin tattaunawar.