Abin da ya sa India ke son alaƙa da Taliban

Asalin hoton, MEA India
- Marubuci, Soutik Biswas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, India correspondent
- Twitter,
Yunkurin India na baya-bayan nan na neman kulla alaka da gwamnatin Afghanistan ta Taliban na nuna alamar yadda India ta dawo daga rakiya ta rungumi kaddara kan yadda al'amuran siyasar yankin suke a zahiri.
Wannan kuwa na kasancewa ne bayan sama da shekara uku da India ta gamu da gagarumin cikas a fannin dabaru da diflomasiyya lokacin da Taliban ta kama Kabul.
Jarin da ta yi shekara ashirin tana zubawa a gwamnatin dumukuradiyya ta Afghanistan ta hanyar horad da sojoji da bayar da tallafin karatu da yin manyan gine-gine kamar na sabuwar majalisar dokokin Afghanistan da India ta yi nan da nan suka tsaya.
Haka kuma fadawar kasar hannun Taliban ta bude hanya ga sauran abokan hamayyar India na yankin musamman Pakistan da China, wanda hakan ya kawar da tasirin da India take da shi a kasar da kuma sake taso da wata sabuwar fargabar tsaro.
To amma duk da wannan, a makon da ya gabata alamu suka nuna sauyi a kan haka, inda ministan harkokin wajen India Vikram Misri ya gana da mukaddashin ministan harkokin wajen Taliban Amir Khan Muttaqi a Dubai - wannan ita ce wata babbar ganawa ta diflomasiyya tsakanin kasashen tun bayan da Taliban ta karbe iko da kasar.
Gwamnatin Taliban ta nuna sha'awarta ga karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki da India, inda ta bayyana alaka da India a matsayin mai matukar muhimmanci a yankin da kuma tattalin arziki.
Rahotanni sun ce tattaunawar ta mayar da hankali ne a kan fadada alakar kasuwanci da kuma amfana da tashar jirgin ruwa ta Chabahar, wadda India take ginawa domin kauce wa tashoshin jirgin ruwa na Karachi da Gwadar na Pakistan.
To yaya muhimmancin wannan ganawa yake? A yanzu dai India ta amince da gwamnatin Afghanistan da Taliban ta kafa bayan hambarar da zababbiyar gwamnati - wanda wannan daman shi ne abin da Taliban ke nema daga kasashen duniya tun bayan da suka dawo kan mulki, kamar yadda Micheal Kugelman na cibiyar masana ta Wilson Center ta Amurka ya bayyana wa BBC.

Asalin hoton, AFP
Tun bayan da Taliban ta sake dawowa kan mulki a Afghanistan, kasashe na daukar matakai da dabaru daban-daban kan mu'amulla da gwamnatin - inda suke sara suna duba bakin gatari kan alaka da ita tare kuma da lura da batun kare hakkin dan'Adam da tsaro.
Misali China ta yi nisa a wannan fanni inda ta kai ga kulla alaka ta sosai da gwamnatin Taliban din ta Afghanistan, da har tana da jakada a kasar.
Babu wata kasa da a hukumance ta amince da gwamnatin Taliban, to amma kuma kasashe wajen arba'in akalla suna da wata 'yar alakar diflomasiyya ko kuma wata alaka da ita.
Wannan ne ya sa kwararru irin su tsohon jakadan India a Afghanistan Jayant Parasad ke dari-dari a kan matakin na India na zawarcin Taliban.
A tsawon shekara uku da ta gabata, ya ce India na alaka da Taliban ta hanyar jami'in diflomasiyya na waje.
India ta rufe ofisoshin jakadancinta a Afghanistan a lokacin yakin basasa a shekarun 1990 kuma ta sake bude su a 2002 bayan yakin ya kare.
Jami'in ya ce ba sa son ganin wannan zaman nesa-nesa ya ci gaba sun fi son ganin an samu yaukakar dangantaka a tsakanin kasashen.
India tana da tarihin alaka da Afghanistan, kamar yadda ministan harkokin waje S Jaishankar ya gaya wa majalisar dokoki a 2023.
India ta zuba jarin sama da dala biliyan uku a ayyuka sama da 500 a Afghanistan, wadanda suka hada da tituna da samar da wutar lantarki da madatsun ruwa da asibitoci.
Haka kuma kasar ta horad da hafsoshin sojin Afghanistan da bai wa dubban dalibai gurbin karatu tare da gina wa kasar sabuwar majalisar dokoki.
Wannan ya nuna alamu na alaka mai dorewa a tsakanin kasashen ba tare da la'akari da wace wane salon shugabanci ko mulki ake da shi a Afghanistan din ba - Mulukiyya ne ko Kwaminishanci ko kuma masu ikirarin bin shari'ar Musulunci ne - kamar yadda jaridar Indian Express ta bayyana.
Wani abu kuma shi ne yayin da ake samun tabarbarewar dangantaka tsakanin Afghanistan da Pakistan sai kuma alaka ke kara kulluwa tsakanin Afghanistan din da India.
Gwamnatin Pakistan na zargin cewa 'yan Taliban masu tsattsauran ra'ayi da ke kasarta (TTP) suna tsara hare-hare ne daga cikin Afghanistan.
Wannan ne ma ya sa Pakistan kan kai hare-hare wani lokaci kan wadanda take zargi 'yan Taliban din ne har cikin Afghanistan abin da yake sa Afghanistan din na cewa Pakistan ta keta haddin 'yancinta na kasa mai ikon kanta.

Asalin hoton, AFP
Wannan ya kawo matukar raguwar alaka tun bayan da Taliban ta sake karbe iko da kasar a 2021, lokacin da ya wani babban jami'in hukumar leken asiri na Pakistan ya kasance daga cikin bakin kasashen waje da suka yi maraba tare da ganawa da gwamnatin ta Taliban.
A lokacin mutane da dama na kallon faduwar gwamnatin dumukuradiyya da komawar Taliban a matsayin koma-baya da India.
Batun Pakistan ba shi ne kadai ke sa India zawarcin gwamnatin Taliban ta Afghanistan ba, akwai wasu abubuwan da ke sa India hakan.
Misali India na neman karfafa sadarwa da samun kutsawa yankin tsakiyar Asiya- abin da ba za ta iya yi ba kai tsaye ta kasa saboda kin amincewa Pakistan.
Kwararru sun ce Afghanistan hanya ce da India za ta iya cimma wannan buri ta hanyar alaka da Iran ta hanyar tashar jirgin ruwa ta Chabahar.

Asalin hoton, Getty Images
A fili take cewa matakin India na baya-bayan nan na neman kulla kyakkywar alaka da gwamnatin Taliban ta Afghanistan na kara wannan manufa ne.
Hakan kuma na kare barazanar 'yanta'adda ga India da zurfafa mua'mulla da Iran da Asiya ts Tsakiya inda Indiyar ke samun karin farin jini daga al'ummar Afghanistan ta hanyar bai wa kasar taimako da kuma adawa da Pakistan wadda ke fama.
Mece ce kuma illar alakar Indiya da gwamnatin Taliban ta Afghanistan?
Matsalar ita ce ita kanta Taliban - domin muna magana ne a kan gwamnati ko kungiya mai tayar da hankali da kuma mugunta wadda ke neman kasashen duniya da hukumomi su kulla alaka da kuma amincewa da ita - ciki har da kungiyoyin ta'addanci na Pakistan -wadda ba wani abu gagarumi da ta yi wajen sauya kanta daga yadda aka santa a shekarun 1990, in ji Mista Kugelman.
Watakila India za ta so ta yi alaka ta nesa-nesa da Taliban, to amma ba lalle ba ne ita Taliban kuma ta yi dari-dari da mu'amulla da India, domin tana ganin India ba kanwar lasa ba ce.
Wannan haka yake to amma maganar ita ce, za a iya yarda da Taliban? Wannan ita ce tambayar da za ke zuciyar India, yayin da sannu a hankali take neman kulla alaka da Taliban din.
Mista Prasad dai ba ya ganin wata illa a kokarin da Indiya ke yi na kulla alaka da Taliban ta Afghanistan, duk da damuwar da ake nunawa a kan yadda Taliban ke yi wa mata.
To amma ana ganin alakar Taliban din da kasashe da hukumomin duniya ka iya sa ta sassauta a kan wasu manufofinta - misali dawo da mata cikin harkokin gwamnati da dawo da 'yancinsu na samun ilimi da aiki da kuma damawa da su a siyasa.