Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin da muke kawo muku.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
A madadin abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 01/06/2025.
Usman Minjibir, Aisha Babangida, da Umar Mikail
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin da muke kawo muku.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
A madadin abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Asalin hoton, Getty Images
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce akwai yiwuwar shugaba Trump da takwaransa na China za su tattauna ta wayar tarho a wannan mako game da batutuwan kasuwanci.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rajin jituwa tsakanin ƙasashen biyu game da kasuwanci.
Ma'aikatar kasuwanci China ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar kasuwancin da aka cimma a watan da ya gabata.
A makon da ya gabata Mista Trump ya zargi Beijing da karya yarjejeniyar.
Sakatare Janar na MDD ya bayyana rashin jin daɗinsa game da rahoton mutuwar aƙalla Falasdinawa 30, a kusa da wata cibiyar rabon kayan agaji da Amurka ke goyon baya a dudancinci Gaza.
Antonio Guterres ya yi kiran gudanar da bincike mai zaman kansa tare da hukunta waɗanda aka samu da hannu a lamarin.
Jami'an jinya sun bai wa waɗanda suka samu raunin harbin bindiga magani, sai dai Isra'il da ƙungiyar agajin sun ƙaryata faruwar al'amarin.
Isra'ila ba ta yiwa jawabin Mista Guterres martani ba.
Jami'an lafiya a Gaza, sun ce an samu rahoton mutuwar wasu Falasɗinawa 3 a ranar Litinin da safe amma dakarun Isra'ila sun musanta rahoton.
Asalin hoton, EPA
Rasha ta gabatar da jadawalin buƙatunta kafin ta amince da tsagaita wuta a yaƙin da take yi da Ukraine.
A wata ganawar kai-tsaye tsakanin wakilan ƙasashen biyu da aka yi a birnin Instanbul na ƙasar Turkiyya, Moscow ta ce sharuɗɗan sun ƙunshi hana Ukraine shiga ƙungiyar tsaro ta Nato, da kuma hana ta mallakar makamin nukiliya, da taƙaita yawan dakarun sojin ƙasar, sannan kuma a kuma ɗage takunkuman da aka sanya wa Rasha.
Haka kuma sharuɗɗan sun hada da janyewar dakarun Ukraine daga yankuna huɗu da Rasha ke iko da su.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa a Ukraine ya zargi Rasha da son a ci gaba da yaƙi.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce yana sa rai shugaba Trump ya sanya wa Rasha takunkumi, bayan ganawa kai-tsaye karo na biyu, tsakanin Ukraine da Rasha da aka gudanar a Turkiyya, ba ta yi nasara ba.
Bangarorin biyu sun amince da musayar fursunonin yaƙi tsakaninsu da kuma mayar da gawarwakin sojijin da suka mutu.
Asalin hoton, NAHCON
Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON ta bayyana cewa ƴan ƙasar 2,717 ne suka kasa samun damar zuwa aikin Hajjin 2025 sakamakon biya a ƙurarren lokaci.
Cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce duk da gazawar hukumarsu ta samun amincewa daga hukumomin Saudiyya na ƙara wa'adin rufe rajistar bizar ta samu biza 13,217 ga kamfanonin yawon buɗe ido daga cikin maniyyata 14,158 da suka yi wa rijista.
Hukumar ta NAHCON ta nemi afuwar mutanen da lamarin ya shafa, tana mai cewa zuwa Hajji kira ne na ubangiji.
Tana mai bayar da shawara ga maniyyata da su riƙa biyan kuɗinsu a kan lokaci domin kauce wa .
Hukumomin Saudiyya ta ware wa Najeriya kujeru 95,000 a aikin hajjin bana
Asalin hoton, Getty Images
Mummanar ambaliyar da ta auka wa garin Mokwa a jihar Neja ta haddasa mummunar asarar rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa.
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi na fargabar cewa adadin waɗanda da suka mutu a iftila'in na kai wa 700, yayin da fiye da mutum 3,000 suka rasa muhallansu.
Ƙungiyar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross ta ce ana ci gaba da aikin neman mutanen da ba a gani ba a tazara mai nisa daga garin Mokwa inda lamarin ya fau.
Asalin hoton, Getty Images
An samu gagarumar ƙaruwar alƙaluman waɗanda suka mutu bayan da aka samo gawarwaki masu yawa daga tazarar kkilomita 10 daga garin.
Kimanin gidaje 250 suka rushe, yayain da manyan gadoji biyu suka ɓalle, kamar yadda Ibrahim Audu Husseini, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ya shaida wa AFP.
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya na bayyana cewa fiye da mutum 25 aka hallaka a hare-haren da aka kai wasu ƙananan hukumomin jihar yayin da wasu da dama suka jikkata.
An kai hare-haren ne a kauyukan Ankpali da Naka a jihar da ke fama da rikicin da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa tsakanin makiyaya da manoma.
A harin farko a safiyar Lahadi, akalla mutum 14 aka kashe a ƙauyen Ankpali da ke ƙaramar hukumar Apa, a cewar shugaban karamar hukumar Adam Ochega kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Mista Ochega ya kuma yi gargaɗin cewa ana ci gaba da samun barazanar wasu hare-haren a yankin.
An sake kai wani harin a yammacin ranar Lahadin, inda aka kashe aƙalla mutum 16, tare da jikkata da dama a ƙauyen Naka da ke karamar Gwer ta Yamma.
Wata mazauniyar yankin ta shaida wa BBC cewa suna zaune a gida da misalin ƙarfe 7:00 na yamma sai ga mutanen sun shigo garinmu sun harbi kan kowa da kowa.
''Kuma sun ci gaba da harbe-harbe har ƙarfe 1:00 na dare, kuma bayan zuwan jami'an tsaro sun guda, bayan guduwarsu an tattaro gawa 16''. a cewarta.
Rahotanni na bayyana cewa ko a watan da ya gabata ma, mutum 44 aka kashe cikin kwana huɗu a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma.
Zuwa yanzu dai ba a san makasudin kai hare-haren ba, sai dai shugaban karamar hukumar Gwer ta yamma Ormin Victor a tattaunawarsa da AFP, ya zargi fulani makiyaya da kai hare haren.
Sai dai a gefe guda kuma makiyaya a yankin na zargin cewa ana kai musu hare-hare tare da ƙwace musu filaye da kuma sanya wa dabbobinsu guba.
Ƴansandan jihar sun tabbatar wa kamfanin dillancin labaran na AFP cewa an kai hare-haren, sai dai ba su faɗi adadin mutanen da abin ya ritsa da su ba.
Jihar ta Benue da ke tsakiyar Najeriya dai na fama da irin waɗannan hare-hare da na ramuwar gayya sakamakon rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, inda rahoton baya bayan nan na ƙungiyar Amnesty Internationa ya nuna cewa akalla mutum 6,800 aka kashe a jihar cikin shekara biyu.
Asalin hoton, Getty Images
Jakadan Trump a Syria ya ce Amurka na goyon bayan shirin da sabuwar gwamnatin Damascus ke yi na ɗaukar dubban tsoffin mayaƙa masu iƙirarin jihadi aiki a rundunar sojin Syria.
Jami'an ma'aikatar tsaron ƙasar na cewa mutum 3,500 galibi ƴanƙabilar Uyghurs daga China da yankin tsakiyar Asia za su shiga sabuwar rundunar sojin.
Jakadan Amurka, Thomas Barrac, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ''yana da kyau a ɗauki mayaƙan, waɗanda ke biyayya ga sabuwar gwamnatin, domin su taimaka wajen ciyar da ƙasar gaba, maimakon ware su.
Dagewar da Amurka ta yi na ƙin ɗaukar ƴan ƙasashen waje a sabbin hukumomin sun canza a watan da ya gabata, bayan da shugaba Trump ya gana da shugaban ƙasar Syria, Ahmed al-Sharaa a Saudiyya.
Asalin hoton, AFP
Masu iƙirarin jihadi sun sake kai hari kan sansanonin soji da filin jirgin saman Timbuktu da ke arewacin Mali.
Mazauna birnin mai ɗimbin tarihi sun ce sun ji ƙarar harbe-harbe da abubuwan fashewa.
Ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai harin.
Rundunar sojin Mali ta ce ta samu narasar daƙile harin tare da kashe mayaƙan ƙungiyar 13.
Harin na Timbuktu na zuwa ne kwana guda bayan masu iƙirarin jihadi sun ƙwace iko da sansanin soji da ke Boulkessi da ke tsakiyar ƙasar, inda rahotonni suka ce sun kashe sojoji 30.
Masana na ganin cewa hare-haren alamu ne da ke nuna samun taɓarɓarewar tsaro a Mali da makwabtanta.
Asalin hoton, AFP
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta ce akwai yiwuwar a fuskanci ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, musamman na arewa ta tsakiyar ƙasar.
NiMet ta bayyana haka ne a cikin hasashen yanayi da ta yi na wannan wata na Yunin 2025, wanda ya kama a ranar Lahadin da ta gabata.
Rahoton na zuwa ne yayin da ƙasar ke ci gaba da jimamin wata mummunar ambaliyar ruwa da aka samu a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar ƙasar, wadda ake kyautata zaton ta yi sanadin rayuka sama da 500.
NiMet ta ce duk da cewa yanzu ne damina ke kankama a yankin arewacin ƙasar, amma "ana hasashen samun marka-markan ruwan sama a cikin ƙanƙanin lokaci a wasu jihohin arewacin ƙasar, musamman Nasarawa, Filato, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi da kuma yankin Babban birnin tarayya (Abuja).
"Wannan zai iya haifar da ambaliyar ruwa a wuraren da suke cikin haɗari," in ji rahoton na NiMet.
Daga nan sai rahoton ya buƙaci mutane su kasance a ankare tare da bibiyar bayanan da take fitarwa a kai a kai.
Haka nan NiMet ta buƙaci hukumomin da ke kula da madatsun ruwa su sanya ido sosai tare da lura da cikowar ruwa a madatsun.
Rahoton ya ce jihohin kudancin ƙasar da kuma na arewa ta tsakiyar ƙasar za su samu ruwan sama mai ƙarfi da iska a kai a kai.
Duk da haka NiMet ɗin ta ce jihohin Kwara, Kogi, Niger, Nasarawa, Benue, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Edo, Delta da kuma Abuja ba za su samu ruwan sama mai yawa kamar yadda suka saba samu ba.
Wanda hakan ya sanya hukumar ta bai wa manoma shawarar su yi amfani da ilimi da kuma ƙwarewa wajen harkokin noma.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Juma'a da Liitnin masu zuwa a matsayin ranakun hutu ga ma'aikatan ƙasar domin bikin Babbar Sallah.
Ranakun za su dace da 6 da kuma 9 ga watan Yuni da muke ciki.
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, yana mai taya al'ummar Musulmi murnar zagayowar bikin.
A ranar Juma'a 6 ga watan Yuni ne Musulmi za su gudanar da Idin Babbar Sallar, wanda ya ƙunshi yanka dabbobin layya.
Asalin hoton, Getty Images
Wata ƙungiya mai alaƙa da al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai hari kan sansanin sojin Mali a garin Boulikessi.
Rahotonni na cewa an kashe sojoji fiye da 30 a harin, amma hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.
A ranar Litinin ne ƙungiyar Jama'a Nusrat ul-Islam wa al-Muslimin (JNIM) ta ce ta kai wa garin Timbuktu mai ɗimbin tarihi hari.
Wata sanarwa da rundunar sojin Mali ta fitar ranar Lahadi game da harin ta ce "ta mayar da gagarumin martani" kafin dakarunta "su janye", abin da ke nufin ƙwace iko da sansanin.
"Dakaru da yawa sun fafata, wasu ma har suka rasa rayukansu, domin kare ƙasar Mali," a cewar sanarwar.
Wata majiya a yankin ta faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa JNIM ta illata mutane da dama kuma ta "tarwatsa sansanin".
Asalin hoton, Reuters
Bayan kammala tattaunawar tsagaita wuta, Ministan Tsaro na Ukraine ya ce sun karɓi daftarin buƙatun Rasha, wanda za su ɗauki lokaci domin tsettsefewa.
"Ya tabbatar cewa ɓangarorin biyu sun amince su "yi musayar fursunonin da suka ji munanan rauni, ko marasa lafiya 'yan shekarun 18 zuwa 25".
Kazalika, ya ce za kuma a yi musayar gawar dakaru a tsakaninsu.
Umerov ya kuma ce sun tattauna yiwuwar ganawa tsakanin Zelensky da Putin, wanda zai iya haɗawa da Shugaba Trump a ƙarshen watan nan.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan da muke samu a yanzu na nuna cewa tawagar wakilan Ukraine ta fice daga farfajiyar tattaunawa da ta Rasha bayan kammala ganawar.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro Rustem Umerov ta isa birnin Istanbul na Turkiyya ne domin ganawa da wakilan Rasha da zimmar kawo ƙarshen yaƙin da suke gwabzawa.
Asalin hoton, @NigerianNavy
Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa sun yi kaɗan wajen tabbatar da tsaron gaɓar ruwan ƙasar da kuma daƙile satar man fetur.
Da yake magana ta kafar talabijin ta Channels TV a yau Litinin, Vice iral Emmanuel Ogalla ya ce jimillar dakarun rundunar tasa ba su 30,000 da ɗoriya ba.
Sai dai ya ƙara da cewa mahukunta sun ƙara yawan adadin mutanen da suke ɗauka duk shekara domin cike giɓin.
"Za ku sha mamaki idan kuka ji cewa dakarun rundunar sojin ruwa ba su wuce 30,000 da ɗoriya ba," in ji shi.
"Amma kuma muna da gaɓar ruwa mai girman kashi ɗaya cikin uku na faɗin ƙasar Najeriya baki ɗaya. Muhimmin abu dai shi ne muna ƙoƙarin ƙara yawan dakarun."
Asalin hoton, AFP
Mutane da dama sun mutu, wasu da dama kuma sun jikkata bayan da sojojin Sudan suka kai hari da jirage marasa matuƙi a kasuwar garin Al-Koma da ke jihar Darfur ta Arewa, in ji rahoton Sudan Tribune.
Wata ƙungiya ta fararen hula a yankin, mai suna Al-Koma Emergency Room, ta ce aƙalla mutum 89 ne suka mutu a harin da jirgin maras matuƙin sojoji ya kai.
Shaidu sun ce sun ga wani jirgi maras matuƙi yana shawagi a sararin sama kafin ya harba kusan rokoki uku a kasuwar da ke cike da jama'a.
Harin ya jawo mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da kuma tashin gobara a wuraren kasuwar.
Garin Al-Koma yana ƙarƙashin ikon dakarun RSF, kuma sojoji sun taba kai masa hari a baya inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama na zargin sojojin Sudan da kai hare-hare ba tare da la’akari da fararen hula ba a yankunan da RSF ke iko da su.
Sai dai sojojin na Sudan na cewa sukan kai hari ne kawai kan sansanonin RSF, kuma suna zargin dakarun RSF da ɓoye kansu a cikin unguwannin jama’a.
Asalin hoton, @PoliceNG/X
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami'anta sun samu nasarar ceto yara 12 da aka yi safararsu a Jihar Abia tare da ƙwato makamai da alburusai da dama a Jihar Kogi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.
"A Jihar Abia, jami’anmu sun kama mutum biyu bisa zargin gudanar da gidan yara marayu ba bisa ƙa'ida ba a cikin gidansu dake kan titin Ikot Ekpene, Aba inda aka gano yara 12 daga tsakanin watanni shida zuwa shekaru 14 a cikin gidan." in ji sanarwar
Bincike dai ya nuna cewa an yi safarar yaran ne daga ƙauyuka daban-daban a yankin Arochukwu.
"An miƙa yaran da aka ceto ga ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Abia domin kula da su." sanarwar ta ƙara da cewa.
"Masu laifin kuma na hannun hukuma suna fuskantar tambayoyi, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike." rundunar ta ƙar da cewa.
A wani samame kuma ta daban a Jihar Kogi, jami’an ‘yan sanda sun ce sun daƙile wata mota ɗauke da makama da alburusai da dama.
"Ana zargin wannan makamai da alaka da wani fashi da makami da aka yi kwanan nan a wajen saida man fetur a Kabba." in ji sanarwa.
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Egbetokun ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu lura da tsaro, kada su ba yara ga mutanen da ba su sani ba, tare da gaggauta kai rahoton duk wata motsi ko mutum da ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Asalin hoton, AFP
Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya da haɗa baki da Faransa da China da Amurka wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a ƙasarsa.
A cikin wani jawabi na awa uku da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na Radio-Télévision du Niger (RTN) a ƙarshen mako, Tchiani ya yi magana da harshen Hausa, Zabarma da Faransanci, inda ya zargi Najeriya da Jamhuriyar Benin da Faransa da China da Aljeriya da Amurka da kokarin dagula ko cutar Nijar da sauran ƙasashen da ke cikin ƙawancen AES.
Wannan shi ne karo na biyu da Tchiani ke zargin Najeriya a yayin wata hira da ya yi ta ranar Kirsimeti a bara, inda ya ce Faransa na haɗa baki da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin tafkin Chadi domin lalata tsaron Nijar, tare da sanin Najeriya.
Tchiani ya ƙara da cewa an gudanar da wata ganawa a ɓoye a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a watan Disamba na shekarar 2024 domin tsara yadda za a afka wa Nijar.
Haka zalika, Tchiani ya ce a watan Janairu 2025, wakilan Benin da Côte d’Ivoire da wasu ƙasashen Yammacin Afirka sun sake haɗuwa a Abuja domin sake nazarin dabarunsu na cutar da Nijar, amma suka gamu da cikas bayan shirin ya ci tura.
Waɗannan zarge-zargen sun biyo bayan hare-haren da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya suka kai a yankunan Tahoua da Dosso, inda aka kashe sama da sojoji 100, lamarin da ya tayar da hankalin jama’ar Nijar.
Tuni gwamnatin Najeriya ta mayar da martani dangane da wannan sabon zargi, inda ta karyata iƙirarin gaba daya tare da bayyana shi a matsayin maras tushe ko makama.
Masu fashin baƙi dai na alaƙanta irin waɗannan zarge-zarge da shugaban sojin ya yi da ƙoƙarin wanke kansa da kuma burge al'ummarsa.
Asalin hoton, EPA
Ƙungiyar likitoci ta duniya MSF ta ce mutanen da take bai wa kulawa a sansanin raba kayan agajin da Amurka ke goyon-baya a Gaza sun ba da labarin yadda sojojin Isra'ila ke yi musu ruwan wuta.
Sun ce ana harbin su ta kowanne ɓangare kama daga jirage marasa matuka da helikwafta,da jiragen ruwa, da tankokin yaƙi.
Wakiliyar BBC ta ce bayanan da ƙungiyar MSF ta fitar sun ci karo da wadanda Isra'ila ke bayarwa cewa ba ta harbi kan fararen hula da ke zuwa karbar abinci a Gaza.
Wani mutum da MSF ta tattauna da shi ya bayar da labarin yadda ake cewa su zo su karbi abinci, amma sai a ɓuge da harbi kan mai tsautsayi.
Ƙungiyar ta ce wannan salon raba tallafin na tattare da mugun haɗari da cutarwa.
Asalin hoton, Reuters
Wani hari da jirgi naras matuƙi ya kai ya yi sanadiyyar kashe gomman mutane tare da raunata wasu da dama a jihar Arewacin Darfur da ke Sudan.
Jaridar Sudan Tribune ta ruwaito cewa sojojin gwamnatin Sudan ne suka kai harin kan wata kasuwa da ke garin Al-Koma a jiya Asabar.
Rahoton jaridar ya ambato ƙungiyar Al-Koma Emergency Room mai fafutika kare haƙƙi na cewa "an kashe aƙalla mutum 89 a harin da jirgin rundunar sojin Sudan ya kai".
Ya kuma ambato hukumomi a yankin na cewa "an ga wani jirgi maras matuƙi na shawagi kafin harin kusan nisan mil uku daga kasuwar ta Al-Koma mai cike da fararen hula."
"Harin ya jawo kashe mutane da yawa, da raunata wasu, sannan ya haddasa tashin gobara a sassan kasuwar da dama," in ji rahoton.