window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 01/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Aisha Babangida, da Umar Mikail

  1. Gwamnatin Neja na yunƙurin haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man fetur

    Gwamnan Neja Umaru Bago

    Asalin hoton, @HonBago

    Gwamnan jihar Neja da ke tsakiyar Neja ya nemi aikin haɗin gwiwa da matatar man fetur ta Dangote domin haƙowa da kuma hada-hadar ɗanyen mai da aka gano a Tekun Bida da ke jihar.

    Umar Bago ya bayyana aniyar gwamnatin tasa ne yayin wani jawabi da ya yi a bikin baje-kolin kasuwanci da aka gudanar a Minna babban birnin jihar ranar Lahadi.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa kamfanin na Dangote ne ya ɗauki nauyin bikin.

    Gwamnan ya siffanta albarkatun ɗanyen man da aka gano jihar na da shi a matsayin tikitin "cigaban tattalin arzikin Neja".

    NAN ya ruwaito cewa wani bincike da aka gudanar a 2023 ne ya gano rijiyoyin mai 17 da za a kasuwancinsa a jihar, inda aka ƙiyasata cewa za a iya kasuwancinsa na tsawon shekara 70.

  2. Rasha da Ukraine za su ci gaba da tattaunawar gaba da gaba

    Rasha da Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Rasha karkashin jagorancin babban jami'in gwamnati, Vladimir Medinsky, ta isa birnin Istanbul na Turkiyya domin gudanar da zagaye na biyu na tattaunar zaman lafiya da Ukraine a yau Litinnin.

    Bangarorin biyu sun tabbatar da ci gaba da ganawar duk da sabbin hare-haren bazata na ban mamaki da Ukraine ta kai kan jiragen yaƙin Rasha.

    Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov ne zai wakilce ta.

    Wakilin Amurka na musamman a wajen tattaunawar, Keith Kellogg, ya ce bangarorin biyu za su gabatar da takardun bayanai kan bukatunsu na tsagaita wuta.

    Alamu na nuna cewa kowanne ɓangare na da niyyar nuna sassautawa kan buƙatunsa.

  3. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Litinin.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Umar Mikail ne zai kawo rahotonnin bisa jagorancin Usman Minjibir.