Mece ce gwamnatin ƴan hamayya da APC ke son kafawa a Kano, ko za ta yi tasiri?

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta soki batun na ƴan adawa tare da bayyana shi a matsayin abin da ya saɓa wa doka

Asalin hoton, facebook/Abba Kabir Yusuf

Bayanan hoto, Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta soki batun na ƴan adawa tare da bayyana shi a matsayin abin da ya saɓa wa doka

Fagen siyasar jihar Kano ya sake ɗaukar zafi bayan da jam'iyyar APC mai adawa a jihar ta sanar da batun kafa gwamnatin ƴan'adawa domin 'sanya ido kan ayyukan gwamnatin jihar mai ci ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf.

Wannan dai wani tsari ne da ba a saba gani ba a Najeriya, kuma tuni batun ya haifar da kumfar baki tsakanin ƴan siyasa a jihar.

Kano ce jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya kuma siyasarta na ɗaukar hankali a kowane lokaci.

An tafka adawa sosai a manyan zaɓukan ƙasa guda biyu da suka gabata, inda a shekarar 2023 Abba Kabir ya samu nasarar zama gwamna da ƙyar da jiɓin goshi, bayan kayar da jam'iyyar APC mai mulki a wancan lokacin, lamarin da aka riƙa tafka shar'a a kai har zuwa kotun ƙoli.

Ita ce jiha ɗaya tilo da ke ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, wadda tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Kwankwaso ke jagoranta.

Me ƴan hamayya suka ce?

A ƙarshen mako ne wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Kano suka sanar da ƙudurin nasu na kafa gwamnatin je ka na yi ka, wadda a turance ake kira 'shadow government'.

A wani taron manema labarai da suka gudanar, ƙungiyar ta wasu ƴaƴan jam'iyyar APC a jihar ta Kano ƙarƙashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ta ce za ta tura mambobinta zuwa ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar Kano domin lura da ayyukan da ake gudanarwa.

Ƙungiyar ta ce za ta yi hakan ne domin ta samu damar yin "suka mai nagarta" domin zaburar da gwamnati ta yi abin da ya kamata.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa "wannan tsari ana amfani da shi a Birtaniya, inda jam'iyyar hamayya ke samar da gwamnatin je ka na yi ka domin sanya wa gwamnati mai ci ido.

"Za mu yi irin haka a Kano ta hanyar tura wakilanmu zuwa hukumomi da ma'aikatun gwamnati domin lura da ayyukan da ake yi.

"Mun shirya yin haka domin abin da muke so shi ne Kano ta zamo wuri mai daɗi ga kowa."

Martanin gwamnatin Kano

Tuni gwamnatin Kano ta mayar da martani, inda ta bayyana matakin a matsayin "wanda bai dace ba kuma wanda ya saɓa wa doka".

A cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Abdullahi, gwamnatin jihar Kano ta bayyana matakin na APC matsayin "mai haɗari."

A cikin sanarwar, gwamnatin jihar Kano ta yi iƙirarin cewa a bisa tsarin dimokuraɗiyya na Najeriya "kafa wata gwamnati ƙarƙashin wata gwamnati ya saɓa wa doka da kundin tsarin mulki".

Sanarwar ta ƙara da cewa "tunanin kafa gwamnatin je ka na yi ka wata hujja ce da ke nuna shirin jam'iyyar APC na haifar da ruɗani a jihar Kano."

Mece ce gwamnatin je ka na yi ka?

Ƙasar da ta fi ƙaurin suna wajen gwamnatin je ka na yi ka a duniya ita ce Birtaniya, kuma kamar yadda ƴaƴan jam'iyyar APCn na Kano suka bayyana, suna son samar da tsarin gwamnatin ƴan hamayyar ce kwatankwacin yadda take a Birtaniya.

A ƙarƙashin salon mulki irin na Birtaniya, gwamnatin je ka na yi ka wasu gungun mutane ne da shugaban jam'iyyar adawa ke naɗawa domin sanya ido da kuma tsokaci kan abubuwan da gwamnati mai ci ke gudanarwa.

Ana bai wa kowane mutum da aka naɗa a gwamnatin je ka na yi ka na Birtaniya ɓangaren da zai riƙa sanya ido a kai domin ƙalubalantar wanda gwamnati mai ci ta naɗa.

Wannan na bai wa jam'iyya mai mulki damar fito da manufofinta da kuma ba ta damar bayyana wa al'umma matsayarta kan duk abubuwan da ke faruwa a ƙasar.

A bisa tsari, tamkar gwamnati ce amma wadda ba ta da ikon tabbatar da ƙudurori, sai dai tana sanya ido tare da matsa wa gwamnati mai ci ta hanyar suka a duk inda suke ganin an yi wani abu da bai dace ba.

Sauran ƙasashen da ke amfani da irin wannan salo sun haɗa da Canada da New Zealand da kuma Austria.

Me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce kan 'gwamnatin ƴan'adawa'?

Audu Bulama Bukarti ya ce babu buƙatar sai kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi magana kan batun gwamnatin ƴan hamayya

Asalin hoton, facebook/Bulama Bukarti

Bayanan hoto, Audu Bulama Bukarti ya ce babu buƙatar sai kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi magana kan batun gwamnatin ƴan hamayya

Dakta Sulaiman Usman Santuraki, malami a makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya ya ce batun kafa gwamnatin je ka na yi ka ba lamari ne na kundin tsarin mulki ba, sai dai salo ne na tafiyar da gwamnati irin na Ingila.

A cewarsa "babu batun kafa gwamnatin ƴan hamayya a kundin tsarin mulkin Najeriya, haka nan ma a irin ƙasashen da ƴan hamayyar ke kafa irin wannan gwamnati.

Salo ne na tafiyar da gwamnati irin na tsarin jamhuriya."

A cewarsa "yadda tsarin yake shi ne, ba wai ƴan hamayya za su kafa wata gwamnati a madadin gwamnatin da ke kan mulki ba ne, sai dai akan nada wasu mutane ne da za suanya ido kan abubuwan da gwamnati ke aiwatarwa domin yin adawa."

A nasa ɓangaren, sanannen lauya ɗan Najeriya da ke Birtaniya, Bulama Bukarti ya ce "Babu buƙatar sai kundin tsarin mulki ya tanadi tsarin kafin a ce ƴan'adawa za su iya yin shi.

"Wani tsari ne da ƴan'adawa ke samarwa domin fito da matsalolin gwamnati ta hanyar bibiya da tsettsefe manufofin gwamnati, saboda haka a gani na wannan bai ci karo da doka ba," in ji Bukarti.

Ya ƙara da cewa abin da doka ta hana shi ne "wani mutum ya ce shi ne gwamna alhali ba shi ne ya ci zaɓe ba.

"Wuri ɗaya ne kawai za a iya hana yin amfani da irin wannan tsari, wato inda ake yin mulkin kama-karya," kamar yadda Bukarti ya bayyana.