Ko Kwankwaso da Ganduje za su iya sake haɗuwa a inuwa ɗaya?

Asalin hoton, Hon Saifullahi Hassan
Da alama rikicin siyasa da zamna tankiya da ke tsakanin tsoffin gwamnonin jihar Kano biyu wato Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Dr Abdullahi Umar Ganduje ya fara damun al'ummar jihar musamman magoya bayansu.
Magoya bayan ɓangarorin biyu da suka ja-daga a yanzu na kiran da a yi sulhu, inda suke nuna cewa tsamin dangatakar da ke tsakanin tsoffin gwamnonin biyu na janyo wa jihar Kano koma-baya a siyasance da ma fannin cigaba.
Rahotanni dai sun nuna cewa na gaba-gaba wajen ganin an yi wannan sulhu su ne Murtala Sule Garo tsohon mataimakin gwamnan jihar da Baffa Babba DanAgundi tsohon shugaban hukumar KAROTA daga ɓangaren Ganduje, sai da kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji a jihar Kano, Abdulmuminu Jibrin Kofa daga Kwankwasiyya.
Dole ne mu haɗa kansu - Baffa Ɗan'agundi
Dakta Baffa Babba Ɗan'agundi shugaban hukumar kula da nagartar ayyuka ta Najeriya kuma tsohon shugaban hukumar KAROTA a Kano lokacin mulkin Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce dole ce ta sa suke son yi musu sulhu.
"Mun duba mun ga irin siyasar gaba da rashin jituwa da tsofaffin gwamnoninmu suke yi wadda ke janyo wa jihar Kano naƙasu. Misali za mu so mu ga ana zama da tuntubar juna tsakanin Sanata Kabiru Gaya da Malama Ibrahim Shekarau da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Idan ka duba me ya janyo wa yau Kano take fama da rikicin masarauta? Siyasa ce ba wani abu ba. Ka ga kenan Kano na fama da rikicin da ke mayar da ita baya amma jihar Legas na can na ci gaba. Dole ne tsoffin gwamnonin nan su zo su jagorance mu mu matasa." In ji Baffa Babba Dan'agundi.
Ko Kwankwaso da Ganduje za su iya zama jam'iyya a guda?
Malam Kabiru Sufi msanin kimiyyar siyasa a birnin Kano, ya ce ba a cire kowane irin tsammani a siyasance.
"Lallai komai zai iya faruwa tunda dai siyasa ce. Ita siyasa ai kasuwar buƙata ce shi ya sa ba a ire tsammanin haɗuwar kowaɗanne irin mutane a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso." In ji Malam Kabiru Adamu.
To sai dai Dr Baffa Dan'agundi ya ce "ba lallai mutanen biyu da sauran tsaffin gwamnonin su haɗu a ƙarƙashin jam'iyya ɗaya ba.
"Ba za a yi musu dole ba cewa sai sun haɗe a jam'iyya guda ba amma ba za mu ƙi kasancewarsu a cikin jam'iyyar guda ba domin samun cigaban da jihar ke buƙata."
Da aka tambaye shi ko wane ne zai kasance jagora idan har suka haɗe? Sai Dan'agundin ya ce "ai gwamnan jiha ne jagoran kowa. Wannan sanannen al'amari ne."
Rikici tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Asalin hoton, Others
Kwankwaso da Ganduje sun kasance makusanta juna inda mutanen biyu suka yi takarar gwamnan da mataimakin gwamnan jihar Kano a 1999 har zuwa 2001 lokacin da Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya kayar da su a ƙoƙarin neman zango na biyu.
Mutanen biyu sun ci gaba da kasancewa abokai bayan rashin samun nasarar zaɓen nasu na gwamna a karo na biyu, inda shugaba Obasanjo ya naɗa Kwankwaso a matsayin ministan tsaro, shi kuma Ganduje ya samu kujerar wakili na musamman a kwamitin kula da tafkin Chadi,
Sanata Rabi'u Kwankwaso da aminin nasa, Abdullahi Umar Ganduje sun sake tsayawa takarar gwamna da mataimakinsa a 2011 inda kuma suka samu nasarar lashe zaɓen.
To sai dai dangantaka tsakanin mutanen biyu ta fara tsami tun a ƙoƙarin tsayar da mutumin da zai gaji Kwankwaso a 2015, inda daga bisani Dr Abdullahi Umar Ganduje ya samu takarar.
Kuma jimkaɗan bayan samun nasarar Ganduje sai tsamin dangatakatar ya fito fili, inda aka ja daga tsakanin jagoran Kwankwasiyya da gwamna Ganduje wanda shi ma ya kafa gidansa na siyasa.
Rikicin ya fito fili bayan Ganduje ya kammala wa'adinsa ya kuma tsayar da mataimakinsa, Nasiru yusuf Gawuna a matsayin wanda zai yi takarar gwamna a 2023, inda shi ma Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir Yusuf wanda ya samu nasara bayan kwashe watanni ana tataɓurzar shari'a.
A yanzu dai Abdullahi Umar Ganduje shi ne shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya inda shi kuma Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kasance jagoran ɗarikar siyasa ta Kwankwasiyya kuma jagora a jam'iyyar NNPP.
Ko Kwankwaso da Ganduje za su sake komawa tsohuwar dangantakarsu a siyasance? Lokaci ne kawai zai iya tabbatar da hakan.