Wane ne halastacen shugaban jam'iyyar NNPP a Kano?

Asalin hoton, Facebook/Multiple
Wata sabuwar dambarwa da zaman rashin tabbas na ci gaba da addabar jam'iyyar adawa ta NNPP da ke mulki a jihar Kano, kan shugabancin jam'iyyar.
Wannan dambarwa ta ja-ni-in-ja-ka game da halastaccen shugabancin jam'yyar a tsakanin masu biyayya ga Kwankwaso da waɗanda suka raba tafiya da shi.
Ɓangarori biyu ne ke jayayya kan shugabancin jam'iyyar ta NNPP; a tsakanin masu alamar kwando da kayan marmari da masu alamar littafi da hula da alƙalami.
Shugabancin Sanata Mas'ud El-Jibrin Doguwa da Hashim Sulaiman Dogurawa ne ke ta kokawar ganin cewar kowannensu shi ne zai ja ragamar jam'iyyar a Kano, abin da ke kara nuna ɓaraka ƙarara a jam'iyyar tun bayan da ta lashe kujerar gwamnan jihar Kano a babban zaben 2023.
Me ɓangaren El Doguwa ke cewa?
Hon Umar Haruna Doguwa ya ce "ni ne shuagaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano mai Kwando mai cike da kayan alatu, tsagin wanda kotu a Abia ta tabbatar da da shi Dr Boniface da waɗanda suke cikin kwamitin amintattaun, cewar su ne ke da izini da hakki a kanta, mu an zabe mu ne bisa tafarkin zabe, kuma mu ne halastattun shugabannin jam'iyyar NNPP a Kano," in ji Doguwa.
To sai dai Sanata Mas'ud El-Jibrin Doguwa ya mayar da martini kan hakan yana mai cewar suna da hujja shi ya sa suke jan zarensu.
"Daga lokacin da waccar kotun ta yi hukunci na ranar 1 ga watan Nuwamban 2024, kowanne tsagin shugabanin na kasa aka rushe su, sai idan shugabann kwmitin amintattun jam'iyyar ya tabbatar, kamar yadda aka tabbatar da namu, saboda hakan shi Dungurawa abin da na sani a kan sa a yanzu shi ne tsohon shugaban jam'iyyar NNPP ne a Kano," a cewarsa.
Martanin NNPP Kwankwasiyya
To sai dai bangaren jam'iyyar mai alamar hula da littafi da alkalami sun ce ba su da masaniyar wani bangare da ke cewa shi ke da jam'iyyar.
Hashim Sulaiman Dungurawa na bangaren Kwankwasiyya, ya ce "NNPP ɗaya ce a Kano karkashin Hashim Dungurawa, idan akwai wani shugabancin wanda na ga wani dan PDP rana tsaka an dora masa tallar kwando da kayan marmari a ka, mu ba mu san lokacin da ya bar jam'iyyar PDP ba ko ya shigo NNPP ba," in ji Dungurawa.
Ita jam'iyya akwai yadda ake tafi da ita ba shugabanin sai da Congress ba a kuma yi shugabancin sai da sahhalewar da kwamitin gudanarwa, don haka ba za ka, kawai shari guri ka zauna ka ce wai kai ne shugaba, bayan kuwa dukkan wadancan matakai babu daya da ya tabbatar da shi a matsayin shugaba," a cewar Dr Hashim Sulaiman Dungurawa.
Haka kuma Hashim Dungurawa ya ce wannan tirka-tirka ba ta ba su tsoro, kasancewar sha'ani na shari'a yana da matakai.
"Abu in yana gaban shari'a ai ba ka yanke masa hukunci ba, matakai nawa muka tsallake a kotun da muka ci zabe da bayan an rantsar da mu, ai jira ake yi tunda akwai kotu daukaka kara. Don haka, mu ba bakin kotu ba ne, don haka ba ta ba mu tsoro," in ji Dungurawa.
Matashiya
Ɓarakar da ke cikin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta fara ɗaukar hankali a siyasar Najeriya ne, bayan da wasu ƙusoshin jam'iyyar, suka yi hannun-riga da jagoran jam'iyyar, Rabi'u Musa Kwankwaso, lamarin da masana suka ce ba abin mamaki ba ne.
Ɗanmajalisar wakilai mai wakiltar Dala, wanda kuma ƙusa ne a jam'iyyar, kuma na gaba-gaba a tsarin Kwankwasiyya, Ali Sani Madakin Gini ya fito a wani faifan bidiyo ya na cewa ya fita daga tsagin Kwankwasiyya.
Haka zalika shi ma tsohon shugaban majalisar dokoki ta Kano Hon. Kabiru Alassan Rurum shi ma ya bi sahun shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilan Najeriya.
Har ila yau an jiyo wasu kalamai da toshon sakataren gwamantin ta Kano Abdullahi Baffa Bichi ya yi, waɗanda ke nuna tsamin dangantaka a tsakanin sa da bangren kankwasiyya, musmaman zargin da ake masa da daya daga cikin wadanda ke da hannu samar da kungiyar nan ta 'Abba tsaya da kafarka' wani zargi da Baffa Bichin ya sha musantawar.
Bayanai na cewa akwai wasu gaggan ƴan siyasa da kuma wasu ƴan majalisar jiha da na tarayya da ke biyayya ga bangaren Sanata Mas'ud El-Jibrin Doguwa.
Tuni dai masu sharhi kan al'amuran siyasa suka fara tsokaci kan wannan dambarwa inda suke gargadin cewa idan NNPP ba ta yi kaffa-kaffa ba, to wannan rigimar za ta iya yi mata mummanan lahani.