Abin da ya jefa jam'iyyar NNPP a Kano cikin rikici

Jiga-jigan jam'iyyar NNPP a Kano

Asalin hoton, Fadar Gwamnatin Kano

  • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
  • Twitter,

Babbar ɓarakar da ta kunno kai a jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya ta janyo dakatar da wasu jiga-jigan gwamnatin jihar, cikinsu har da Sakataren Gwamnati Bappa Bichi.

A makonnin da suka wuce ne aka fara ganin rarrabuwar kai tsakanin ƴaƴan jam’iyyar, inda wasu ke ƙalubalantar salon jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaban jam'iyyar NNPP na Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya yi wa BBC bayani kan abubuwan da suka faru har ta kai ga ɗaukar matakin kan Bappa Bichi, da kuma Injiniya Muhammad Diggol wanda shi ne kwamishinan sufuri na Kano.

"Jam'iyya ta samu bayani bayan binciken da aka gudanar cewa a mazaɓunsu da [ƙananan hukumominsu] kuma shiyyar Kano ta Arewa cewa abubuwan marasa daɗi na faruwa game da waɗannan mutanen kuma sun bi diddigin abubuwan kuma sun tabbatar abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar da hannunsu, mu kuma muka tabbatar da wannan dakatarwar." in ji Dungurawa.

Ya bayyana cewa rahoton da suka samu ba ya buƙatar ƙarin bincike ko "kare kai" saboda "idan aka kawo maka hujja a fili ga abin da mutum ya faɗa, ga kuma abin da ya sa aka faɗa, ga kuma wanda suka faɗa ɗin duk ana ganinsu tare da shi, in dai ba yaudarar kai ba, babu maganar bincike".

A daidai lokacin da sanarwar dakatarwar tasu ke ɓulla, sai ga shi Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci sulhu tsakanin 'ya'yan jam'iyyar, cikinsu har da Bappa Bichi.

Sai dai Dungurawa ya ce ba shi da wata masaniya game da sulhun da aka yi kafin dakatar da su.

Ba a kan dakatarwar gwamna ya yi sulhu ba

Sai dai wata sanarwa da kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook ta tabbatar da gudanar da wani zaman sulhu a daren ranar Talata.

Ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir ne ya jagoranci zaman tsakanin ɓangarorin jam'iyyar NNPP da ke da saɓani da juna - Baffa Bichi da Hamza Maifata Bichi, ɗantakarar shugaban jam'iyyar NNPP a ƙaramar hukumar ta Bichi.

BBC ta fahimci cewa zaman sulhun da aka yi ba shi da alaƙa da dakatarwar da jam'iyyar ta yi wa Baffa Bichi.

"Bbisa dukkan alamu, sulhu ya tabbata bayan da Kakakin Majalisar Dokokin Kano Jibril Ismail Falgore ya jagoranci sauran jagororin majalisar zuwa wajen Gwamna Abba domin aiwatar da wannan sulhu a karon farko," a cewar Sanusi Bature.

Bayan taron, Baffa Bichi ya miƙa godiyarsa bisa saka bakin da gwamnan ya yi inda kuma ya yi alƙawarin warware saɓanin da ke tsakaninsa da ɓangaren da ba su shiri a mazaɓarsu ta Bichi, da sauran ƙungiyoyin da ke sukar sa.

Daga bisani Bappa Bichi, kamar yadda sanarwar ta ce, ya tsame kansa daga gangamin Abba Tsaya da Ƙafarka da ke neman gwamnan jihar ya daina yin biyayya sau da ƙafa ga jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

A cewar Bichi: "Tuni na miƙa kaina da duk al'amurana ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na jagoranmu, kuma na amince cewa duk abin da yake so a shirye nake na mutunta shi. Game da ɗaya ɓangaren da ake magana a kai [Abba Tsaya da Ƙafarka], ba ni da wata alaƙa da su.

"Da a ce ƙungiyar "1 to tell 10" ce, kowa ya san ni ne na kafa ta, kuma ina da ofisoshi a duka jihohi 19 na arewaci."

Dangane da sulhun da aka yi kuma, Baffa ya bayyana cewa: "Tuni gwamna ya sa baki kuma komai ya wuce. Duka magoya bayansa ne kuma a shirye muke mu amince da duk abin da yake so."

A nasa ɓangaren, Hamza Sule Maifata, ya bayyana ƙudirinsa na son rungumar zaman lafiya da kuma warware ɓarakarsa da sakataren gwamnatin.

Yadda rikici a jam'iyyar NNPP ya samo asali

Bayanai da BBC ta tattara sun nuna cewa rikicin ba ya rasa nasaba da yadda wasu ƴanmajalisar jihar ta Kano suke zargin Sakataren Gwamnati Baffa Bichi da kankane lamuran da suka shafi jam'iyyar ba tare da sanya su a ciki ba.

Wasu ƴanmajalisar sun koka da yadda Bichi ke ƙin saka mambobinsu cikin ayyukan gwamnati ballantana ma a saka su cikin lissafin yanke shawara kan wani mataki da ya shafi jam'iyyar.

Wani batu kuma da ya ɓullo kan rikicin shi ne na fitar da ƴantakarar shugaban jam'iyya a ƙananan hukumomi, inda aka zaɓi Hamza Maifata, mai biyayya ga ɓangaren Ahmed Garba Bichi, a matsayin ɗantakarar shugabancin NNPP a ƙaramar hukumar ta Bichi yayin da aka bai wa Ado Abdu Bichi daga ɓangaren Baffa Bichi sakataren ƙaramar hukuma na NNPP.

Bayanai sun nuna cewa bai yi wa Baffa Bichi daɗi ba kasancewar tun lokacin ne aka lura cewa ya tsame kansa daga shiga harkokin NNPP, har ma da ƙin zuwa tarukanta.

Sannan akwai wasu magoya bayansa da aka lura suna tallata tafiyar Abba Tsaya da Ƙafarka - abin da ke nufin Gwamna Abba Kabir ya koma cin gashinsa ba tare da ya yi wa tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso biyayya ba - kuma wannan na ɗaya daga cikin zarge-zargen da ake masa cewa shi ya assasa gangamin.

A yammacin ranar Litinin ne, shugaban majalisar dokokin jihar Kano da sauran ƴanmajalisar NNPP suka ga buƙatar su kira taron sulhu domin sasanta tsakanin Baffa Bichi da Maifata, wanda tsohon ɗanmajalisa ne a Kano.

Bayan nan ne kuma tawagar ta ɗunguma zuwa ga wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ɓangarorin biyu suka yi jawabai na nuna sun samu sulhu a tsakaninsu.

Sai dai abin da BBC ta fahimta daga wasu jawabai da Baffa Bichi ya yi shi ne, yana da matsala da jagorancin Rabiu Kwankwaso saboda jawabinsa ya nuna cewa gwamna ne jagoransa kuma shi ne ya naɗa shi, don haka idan gwamna ya nemi ya yi sulhu da kowa zai yi.

Bayan wannan ganawa da gwamnan Kano ne kuma sai jam'iyya ta fitar da sanarwar dakatar da Baffa Bichi, da Muhammad Diggol wanda makusanci sakataren gwamnatin ne.

A Kano ne kawai jam'iyyar NNPP - wadda Rabiu Kwankwaso ya yi wa takarar shugaban ƙasa a 2023 - take da kujerar gwamna a Najeriya.