Taimakon da ya kamata ku bai wa wanda ya samu bugun jini

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Bugun jini na iya faruwa a kowanne lokaci — a gida ko a wurin aiki ko a titi, ko ma yayin hira da abokai, ba tare da nuna wata alama ba kafin lokacin.
Haka kuma ɓata lokaci, duk ƙanƙancinsa ka iya janyo wa mutum babbar matsala a rayuwa ko ma ya kai ga mutuwa.
Duk da haka, mutane da yawa ba su san matakan farko da za su iya bi domin taimaka wa mutum ba wajen ceto rai kafin zuwan ƙwararren likita ko zuwa asibiti.
A dalilin haka ne BBC Hausa ta tuntuɓi Dr Salihu Ibrahim Kwaifa, ƙwararren likita a Abuja dangane da abubuwan da suka kamata mutane su sani wajen taimaka wa wanda ke fuskantar bugun jini ko kuma ma su da kansu.
Matakan taimakon farko

Asalin hoton, Getty Images
"Bugun jini shi ne a samu daskarewar jini, wanda zai toshe wata hanya da ke kai jini ga ƙwaƙalwa ko kuma a samu fashewar ƙananan hanyoyin jini da ke kai jini ga ƙwaƙalwa." In ji dakta Kwaifa.
Dr kwaifa ya ce tun da samun motocin taimakon gaggawa na wahala a Najeriya ko kuma kafin su isa inda maras lafiya yake za a iya ɗaukar dogon, ya kamata mutane su san waɗannan matakan taimako biyar masu muhimmanci idan wani ya samu bugun jini;
- A kwantar da mutum a gefen jikinsa na hagu ko dama: Idan wani ya samu bugun jini, kada a kwantar da mutum kan gadon bayansa a rigingine saboda harshen shi zai iya toshe masa hanyar numfashi, abin da ake so shi ne a tabbatar an kwantar da mutum a gefen hagunsa ko dama.
- A tabbatar cewa mutum yana numfashi da kyau: Dr Kwaifa ya kuma ce, "Idan kuna son ku tabbatar cewa mutum na numfashi, za ku taɓa hannu mutumin inda akwai jijiya ko wuya, nan za ku ga yana bugawa.
- Matsar da duk wani tufafi ko wani abu da ke rataye a wuyansa zuwa ƙirji domin bai wa mutum damar numfashi:
- Cire duk wani abu da zai iya ji masa rauni.
- Kada a bai wa mutumin abinci, ko ruwa ko magani.
Alamun bugun jini

Asalin hoton, GETTY IMAEGES
Dr Kwaifa ya ce bugun jini ya kasu kashi biyu da suka haɗa da Bugun jini sakamakon ƙarancin jini da ke zuwa zuciya da kuma bugun jini saboda fashewar jini a ciki ko kuma kusa da ƙwaƙwalwa.
Likitan ya ce bugun jini da ake kira ƙarancin jini da ke zuwa zuciya shi ne wanda ya fi yawa kuma ya fi afkuwa ga mutane.
"A wannan ne mutum zai fara jin wasu alamu da suka haɗa da
- Sandarewar wani ɓarin jiki.
- Mutum ya ji ba ya gani da ido ɗaya.
- Fuska ta juye gefe ɗaya
- Mutum zai dinga jin sagewa a jikinsa
- Mutum ya ji ba ya iya yin magana
Amma kuma likitan ya ce waɗannan alamomi na ɓacewa bayan awa ɗaya
Dr Kwaifa ya ce "duk wanda ya samu irin waɗannan alamu, wato kashi 70 zuwa 80 idan ba a yi hattara ba zai samu wannan bugun jini cikin wata ɗaya ko biyu."
Likitan ya ce irin wannan bugun jini zai kama mutum ne yana cikin hankalinsa, babu wani ciwon kai.
Likitan ya ce bugun jini na biyu shi ne wanda ake samun fashewar jini a ciki ko kusa da ƙwaƙwalwa.
"Idan wannan bugun jinin ya afku shi ne wanda mutum zai faɗi kuma ya fita hayyacinsa amma kafin nan, ga irin alamun da mutum zai ji ko gani."
- Ciwon kai
- Amai
- Ƙaƙƙafewa
- Shiɗewa
"Irin wannan bugun jini shi ne wanda ya kamata a damu da shi kuma a san da shi saboda shi ne wanda zai bugi mutum kuma ya faɗi."
Abubuwan da ke haifar da bugun jini

Asalin hoton, SPL
Dr Kwaifa ya ce akwai abubuwa da yawa da ke haifar da bugun jini a Najeriya da kuma Afirka waɗanda suka haɗa da;
- Hawan jini: Hawan jini shi ne babban abun da ke janyo bugun zuciya ga mutane, waɗanda ke fama da hawan jini sun fi fuskantar haɗarin kamuwa da bugun jini ko shanyewar ɓarin jiki.
- Ciwon suga: Wannan shi ne abu na biyu bayan hawan jini da ke haddasa bugun jini, waɗanda ke fama da ciwon suga su ma suna cikin haɗarin kamuwa da bugun jini.
- Cutar zuciya: Dr Kwaifa ya ce wannan cutar ma tana ɗaya daga cikin abubuwan da ke haɗɗasa wa mutum bugun jini.
- Cutar HIV da dai sauransu.
Yadda za a kiyaye kamuwa da bugun jini
Dr Kwaifa ya lissafo abubuwan da suka kamata a yi domin kiyaye kamuwa da bugun jini.
- Cin abinci mai lafiya da gina jiki
- Motsa jiki akai-akai
- Kiyaye shan taba sigari da giya
- Kula da ciwon suga
- Kula da hawan jini
- Rage damuwa
- Zuwa ganin likita akai-akai
Likitan ya ce yawanci a Najeriya, mutane ba su cika zuwa asibiti ba idan suka fara jin alamun da ya lissafo har sai abin ya yi tsanani.
"Sai ka ji yawanci mutane suna cewa aljanu ne idan suka ga irin waɗannan alamomi, ba a alaƙanta shi da ciwon, wanda shi ne babban abun da ke cutarwa," kamar yadda likitan ya bayyana.