Abu biyar da suka kamata ku sani game da lafiyar ƙwaƙwalwa a wuraren aiki
Lafiyar ƙwaƙwalwa ko kuma mental health a Turance na cikin fannonin likitanci da mutane da dama a faɗin duniya ba su fiya zuwa asibiti saboda da shi ba.
Hukumar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta ware kowace ranar 10 ga watan Oktoba domin wayar da kai game da lafiyar ƙwaƙwalwa a faɗin duniya.
Taken ranar na wannan shekara shi ne "Lafiyar Ƙwaƙwalwa a Wurin Aiki" kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana, yayin da ta ce tana aiki da abokan hulɗa domin kyautata walwalar ma'aikata a wurin aiki.
WHO ta bayyana lafiyar ƙwaƙwalwa a matsayin walwalar da ƙwaƙwalwa ke samu da ke bai wa mutane damar jure walahar rayuwa, da gane ƙwazon da suke da shi, da koyon abubuwa da kuma yin aiki da kyau da zai taimaka wa al'umma baki ɗaya.
Albarkacin wannan rana, mun duba wasu abubuwa biyar da suka kamata ku sani game da lafiyar ta ƙwaƙwalwa.
Su wane ne ke kamuwa da lalurar ƙwaƙwalwa?

Asalin hoton, Getty Images
Duk wani mutum mai rai zai iya kamuwa da larura a ƙwaƙwalwarsa.
Hukumar WHO ta yi ƙiyasin cewa kowane mutum ɗaya cikin huɗu a duniya zai iya samun matsalar ƙwaƙwalwa tun daga farko zuwa ƙarshen rayuwarsu.
Dr Miftahu Muhammad ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Abuja kuma ya faɗa wa BBC cewa bincike ya nuna cewa kashi 90 cikin na mutanen ba su samun kulawar da ta dace.
Mece ce alaƙar aikin yi da lafiyar ƙwaƙwalwa?
Aikin yi na da matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan'adam, abin da ya sa ma taken ranar na bana ya zama "Lafiyar Ƙwaƙwalwa a Wurin Aiki".
Binciken da WHO ta yi ya nuna cewa kashi 60 na al'ummar duniya na zuwa ko kuma gudanar da aikin yi.
"Abu ne mai muhimmanci ga gwamnatoci, da masu ɗaukar aiki, da ƙungiyoyin ma'aikata, da sauran hukumomin da ke kulawa da lafiyar ma'aikata su yi aiki tare wajen inganta lafiyar ƙwaƙwalwar ma'aikata a wurin aiki," a cewar WHO.
Dr Miftahu - wanda shugaban ƙungiyar Safe Brain Organisation ne - ya ce: "Wajen aiki na cikin wurare masu haɗari da ke haifar da matsalar ƙwaƙwalwa. Amma kuma samun aikin kansa abu ne mai muhimmanci wajen taimaka wa lafiyar ƙwaƙwalwa.
"Wannan ya nuna cewa ya kamata a tabbatar cewa wajen aiki bai haddasa wa mutum larurar ƙwaƙwalwa ba."
Me zai faru idan ba a kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a wajen aiki?
Likitan ya ƙara da cewa rashin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa na da matuƙar tasiri ga lafiyar al'umma baki ɗaya.
"Bincike ya nuna cewa ana asarar ranakun da ba a zuwa aiki biliyan 12 a duniya duk shekara ta dalilin matsananciyar damuwa da tsoro," in ji shi.
"Wannan kuma yana haifar da asarar kuɗi dala tiriliyan ɗaya duk shekara. Wannan yana nuna cewa akwai buƙatar lallai a fitar da tsare-tsare na kare lafiyar ƙwaƙwalwa a wuraren aiki."
Wace matsala larurar ƙwaƙwalwa ke haifarwa tsakanin ma'aikata?
Idan ba a kula da matsalar ƙwaƙwalwa ba takan shafi alaƙa tsakanin ma'aikata.
"Takan haifar da mutum ya ƙi yin aikin da ya kamata ya yi, wanda hakan zai rage yawan aikin da ake yi a ma'aikata da kuma kuɗin da ake samu," in ji likitan.
"Haka nan, matsalar za ta shafi alaƙa tsakanin ma'aikata, saboda dole ne a samu kyakkyawar alaƙa da yin aiki tare domin samar da abin da ake buƙata."
Wace rawa al'umma za su taka wajen rage girman matsalar?
Kowa da kowa na da gudummawar da zai bayar wajen rage girman matsala ko kuma inganta lafiyar ƙwaƙwalwa.
Dr Miftahu ya ce: "Mun san cewa wannan larura za ta iya shafar kowa, saboda haka dukkanmu muna da rawar da za mu taka. Akwai matakan da mutum zai da kansa.
"Daga ciki akwai ɗaukar hutu, da kula da yanayin da mutum yake ji. Idan mutum ya ji wani ɓacin rai ko tsoro ya nemi taimako. Kada a ji kunya.
"Su ma hukumomi da masu ɗaukar aiki na da rawar da za su taka, ciki akwai haɗa bita domin faɗakarwa kan rage tsangwama."