Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/05/2025
Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wata kotu a Aljeriya ta yanke wa wasu tsofaffin yantakarar shugaban ƙasa uku hukuncin shekara goma a gidan yari da kuma biyan tarar dubban daloli.
An samu mutanen uku da laifin biyan kuɗin domin su samu sa hannun da ake buƙata domin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na watan Satumban bara.
Kasancewar dukkansu ba su iya rajistar takararsu ba, hakan ya sa shugaban ƙasa mai ci, Abdelmadjid Tebboun ya yi nasara da gagarumin rinjaye.
Kusan wasu mutum saba'in kuma sun fuskanci hukunci a ƙarar.
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya yi kan-kan-kan da Alan Shearer da Andrew Cole a yawan cin ƙwallaye a kaka ɗaya a Premier League.
Salah wanda ya ci Crystal Palace a wasan karshe na gasar Premier ranar Lahadi, yana da hannu a cin ƙwallo 47 kenan a bana.
Ɗan wasan tawagar Masar, ya ci kwallo 29 - ya bayar da 18 aka zura a raga.
Shi ma Shearer da Cole haka suka yi a baya, inda kowannensu ya ci ƙwallaye 47 a kakar tamaula a Premier League.
Asalin hoton, PDP/X
Jami’an babban birnin tarayya (FCTA) sun rufe Wadata Plaza, ginin da ke ɗauke da babbar sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja, saboda kin biyan harajin fili.
Jami’an sun isa wurin ne inda suka umarci mai gadin wajen da ya kira masu kula da wurin, wanda yake yankin Wuse da ke Abuja.
Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin jami'an hukumar FCTA da ma'aikatan sakatariyar, kafin daga bisani aka buɗe domin ma'aikatan su kwashe motocinsu da wasu kayayyakinsu, sannan aka sake garƙame ta.
A makon jiya ne FCTA ta sanar da cewa za ta ƙwace wasu kadarori 4,794 saboda rashin biyan kuɗin harajin ƙasa na tsakanin shekaru.
Asalin hoton, APTN
Shugaba Macron na Faransa ya musanta samun wata rashin fahimta tsakaninsa da mai ɗakinsa bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna ta tana zungure masa fuska.
Bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna Brigitte Macron ta sa hannu a fuskar mijinta yayin da suke shirin saukowa daga jirgi a Vietnam.
Wakilin BBC ya ce ya bayyana a ruɗe amma sai ya yi sauri ya kalli inda na'urar naɗar hoto take ya kuma yi murmushi.
Kafofin yaɗa labaran Faransa sun ce fadar Elysee ta tantance bidiyon kuma ta tabbatar da sahihancinsa bayan ƙaryatawa a baya.
Shugaba Macron ya shaida wa ƴanjarida a Hanoi cewa wasa suke yi kamar yadda suka saba yi.
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na bayyana cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga sun hallaka wani fasto mai suna Mimang Lekyil a karamar hukumar Bokkos na jihar Plateau.
Mazauna garin sun faɗa wa jaridar Daily Trust cewa ƴan bindigar waɗanda ake zargin masu garkuwa ne, sun far wa gidan limamin cocin da misalin karfe 9 na daren Lahadi - a daidai lokacin da iyalansa ke ƙoƙarin kwanciya barci.
Wani mazaunin Bokkos Bishop Ayuba, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa tun da farko an yi garkuwa da wasu mata biyu - amma ƴan bijilanti da matasan yankin sun samu nasarar kuɓutar da su daga bisani.
Ya ƙara da cewa an kai gawar faston mai shekara 70 zuwa mutuware a Bokkos.
A ɗaya gefen, an ƙona gidajen da ake kyautata zaton na al'ummar makiyaya ne a yankin wanda wasu fusatattun matasa suka yi.
Wani shugaban matasan Fulani a Bokkos, Saeed Adamu, ya faɗa wa Daily Trust cewa an ƙona gidajen mambobinsu ne bayan kashe malamin majami'ar.
Adamu ya yi Alla-wadai da kashe jagoran addinin, inda ya yi kira ga jami'an tsaro da su gudanar da bincike kan lamarin da kama waɗanda aka samu da hannu.
Asalin hoton, NDHQ
Sojojin Najeriya sun ce an samu fashewar wani abu kusa da barikin sojoji a Abuja, babban birnin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a barikin sojoji na Mogadishu da ke kan hanyar Mararaba-Nyanya.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ya tayar da bam ɗin ya mutu.
An kuma samu jikkatar mutum guda, inda yanzu yake samun kulawa a asibitin sojojin.
Sojojin sun ce an shawo kan lamarin zuwa yanzu, sannan sun ce babu wata fargaba - mutane kuma su kwantar da hankalinsu.
A watan Janairu, wasu mutum biyu suka mutu lokacin da wani bam ya tashi a makarantar Islamiyya da ke wajen birnin Abuja.
Hukumomi sun ce wani ɗalibi ne ya tayar da bam ɗin.
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya ce hare-haren da Isra'ila ke zafafawa kan Gaza na ƙara yin illa ga farar hula wanda a yanzu hakan ba zai zama hujja ga yaƙin da take cewa tana yi da mayaƙan Hamas ba.
Ya ce ya kasa fahimtar manufofin Isra'ila kan luguden wutar da take kan Gaza kuma zai yi magana da Firaiminista Benjamin Netanyahu domin ya yi kira gare shi da ya guji wuce gona da iri.
Jamus ta kasance ɗaya daga cikin manyan magoya bayan Isra'ila.
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce yana so ya ga ƙasar da ke aiki yadda ya kamata - sannan bai ce dole sai ya zama shugaban Najeriya ba.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi, inda ya sha kaye hannun shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC.
Obi ya bayyana haka ne lokacin bikin murnar cika shekara biyu kan mulki na gwamnan Abia Alex Otti, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ya ce ya kamata a samu shugabanni waɗanda mutane za su yi alfahari da su.
Ya ƙara da cewa hakkin shugaba ne ya kare muradun waɗanda yake mulka.
Asalin hoton, Reuters
Ukraine ta ce Rasha ta ƙara kai hare-hare cikin dare da jirage marasa matuƙa fiye da 350 - adadi mafi girma tun bayan da Rasha ta yi wa ƙasar mamaya.
Labarin na zuwa ne sa'oi bayan da Shugaba Donald Trump ya ce luguden wutar da Vlir Putin ya yi a baya-bayan nan kan biranen Ukraine rashin hankali ne.
Ya ce yana duba yiwuwar ƙaƙaba ƙarin takunkumai kan Moscow.
A nasa ɓangaren, Shugaba Zelensky ya ce rashin ɗaukan mataki ya bai wa Rasha damar ci gaba da zafafa hare-hare.
Wakilin BBC ya ce, Shugaba Zelensky na neman Amurka ta ɗauki mataki domin dakatar da hare-haren Rasha.
Asalin hoton, Reuters
Mayaƙan M23 da ke rikici a Gabashin Congo sun ce tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila ya isa birnin Goma, lamarin da ya kawo ƙarshen gudun hijirar da ya yi.
Gwamnati a Kinshasa ta zargi Mista Kabila da alaƙa da mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan Rwanda.
A makon da ya gabata ne, majalisar dokokin ƙasar ta janye masa rigar kariya domin ya fuskanci shari'a kan cin amanar ƙasa.
A cewar wakilin BBC komawarsa gabashin Congo da yantawaye ke da iko zai yi wuya ga hukumomi su iya kama shi ko ma yi masa shari'a.
Tsohon shugaban ƙasar ya musanta duka zarge-zargen da ake masa.
A wani jawabi ranar Juma'a, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen abin da ya kira mulkin kama-karya.
Masu sharhi sun ba da shawarar Mista Kabila, wanda makusanci ne ga ƙasar Rwanda, na iya shiga cikin masu tawaye domin ƙoƙarin kifar da mulkin Felix Tshisekedi.
Asalin hoton, Anadolu
Rundunar sojin Isra'ila ta sake bai wa Falasɗinawa da ke Khan Younis umarnin ficewa daga birnin na Kudancin Gaza.
Rundunar IDF ta ce za ta ƙaddamar da wani hari da ba a taɓa ganin irin shi ba kan yankin.
Wakiliyar BBC ta ce hakan na faruwa ne bayan da aka harba makamin roka uku daga kudancin Gaza da safiyar yau kamar yadda IDF ta bayyana.
Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla mutum hamsin da huɗu aka kashe a hare-haren cikin dare da Isra'ila ta kai.
Aƙalla mutum talatin da biyar sun mutu ne a wata makaranta da aka mayar matsugunni a Gaza.
Isra'ila ta ce Hamas na amfani da wajen a matsayin cibiyar aiwatar da ayyukanta.
Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgin sama daga kamfanin All Nippon Airways (ANA) da ke tafiya daga birnin Tokyo na ƙasar Japan zuwa Texas ya yi saukar gaggawa a birnin Seattle bayan wani fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar fita daga cikin jirgin yayin da yake cikin iska.
Rundunar ‘yan sandan tashar jirgin saman birnin Seattle ta shaida wa manema labarai cewa sun samu rahoton mutumin da ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar fita daga cikin jirgin a lokacin tashi.
Rahotanni sun bayyana cewa mutumin yana fama da wani yanayi na rashin lafiya wanda ya tilasta wa wasu fasinjoji da ma’aikatan jirgin dakatar da shi.
An garzaya da shi asibiti bayan saukar jirgin. Har yanzu ba a tabbatar ko za a tuhume shi da wani laifi ba.
Kamfanin jirgin saman ANA ya ce: "Lafiyar fasinjojinmu da ma’aikata shine babban fifikonmu kuma muna godewa jami’an tsaron cikin gida bisa taimakon da suka bayar."
Bayan jirgin ya sauka a filin jirgin saman Seattle-Tacoma, an fitar da wani mutum na biyu daga jirgin saboda halin rashin da'a da ya nuna, in ji mahukunta.
A ranar Litinin ɗin nan ne wata babbar kotun shari'ar musulunci da ke Kano ta yanke wa Shafi'u Abubakar, matashin nan da aka tuhuma da ƙona masallata hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun shi da aikata laifin kisan.
Al'amarin da ya faru ne a gari Gadan da ke ƙarƙashin Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano.
A ranar 15 ga watan Mayun 2024 ne matashin ya zuba fetur sannan ya cinna wa mutanen wuta yayin da suke yin sallar Asuba, lamarin da ya janyo da dama daga cikinsu suka kone sannan wasu suka mutu.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne sanadiyyar rikici kan rabon gado tsakaninsa da ƴan uwansa.
Asalin hoton, Indian Coast Guard/Twitter
Hukumomi a jihar Kerala da ke kudancin Indiya sun fitar da gargaɗi cewa suna cikin shirin ko-ta-kwana bayan da wani jirgin ruwa ɗauke da mai da wasu kaya masu haɗari ya kife tare da nutsewa a gaɓar tekun jihar da ke cikin Tekun Arabia da ke India.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, lokacin da jirgin ruwan mai ɗauke da tutar Liberia ya kife a kusa da birnin Kochi.
Yankin gaɓar ruwan da lamarin ya faru ya kasance wurin yawon buɗe ido ne.
Jirgin ruwan na ɗauke da mutum 24 kuma da kwantainoni 640.
An samu an ceto dukkan mutum 24 da ke cikin jirgin, amma rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin kwantainonin da suka faɗa cikin ruwa suna tunkarar gaɓar tekun, lamarin da ya tilasta wa hukumomi fara kwashe mutane daga yankin.
Hukumomi sun nuna damuwa kan yadda kifewar jirgin da zubar mai da wasu sinadarai masu haɗari ka iya zama barazana ga lafiyar mazauna yankin da halittun cikin ruwa.
An shawarci mazauna yankunan da ke kusa da teku da ka da su kusanci ko su taɓa kowanne irin kwantaina ko mai da ruwa zai iya korowa zuwa gaɓar, yayin da aka shawarci masu kamun kifi da su nisanci wurin da jirgin ya nitse.
Asalin hoton, Reuters
Ma’aikatar lafiya ta Habasha ta bayyana cewa an samu bullar cutar ƙyandar biri wato Mpox a karon farko a kudancin ƙasar, a yankin da ke kan iyaka da Kenya.
A cewar sanarwar da ma’aikatar ta fitar jiya: “Hukumar Lafiyar Jama’a ta Habasha ta tabbatar da gano wasu mutane da suka kamu da kwayar cutar, bayan an ɗauki samfuransu a lokacin da aka yi zargin suna ɗauke da cutar a cikin birnin Moyale da ke yankin Oromia.”
Ma’aikatar ta ce tana bin sawun mutanen da suka yi mu’amala da wata uwa da jaririnta, waɗanda gwaje-gwaje suka tabbatar su ma sun kamu da cutar inda aka bayyana cewa mahaifin jaririn ya dawo kwanan nan daga ƙasar Kenya.
Yankin Moyale na ɗaya daga cikin wuraren da ke da yawan mu’amala ta ciniki da sauran harkoki tsakanin al’ummar Habasha da Kenya.
Kenya dai ta ruwaito fiye da mutum 60 da suka kamu da cutar mpox tun daga watan Yuli na bara.
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure da ake zargi da kashe kishiyarta.
Lamarin ya faru ne a bayan wata makarantar firamare ta Dadi da ke unguwar Sabon Gari, a ƙaramar hukumar Daura bayan da wata matsala ta cikin gida tsakanin matan auren biyu ta rikiɗe zuwa rikici mai muni da ya kai ga mutuwa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyanawa manema labarai abin da ya faru.
Sanarwar ta ce: “A ranar 24 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11 na dare ne ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari suka samu rahoto daga wani Nasir Yusuf, mijin matar, cewa ya dawo gida daga kasuwa ya tarar da matarsa ta farko mai suna Zainab Lawal tana kwance cikin jini, an caka mata wuƙa sau da dama.”
“Da samun rahoton, DPO na yankin tare da tawagar jami’ai suka garzaya wurin da abin ya faru, inda suka gaggauta kai matar zuwa asibitin koyarwa na tarayya da ke Daura domin ceto rayuwarta, amma likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarta.”
“A yayin bincike ne aka kama kishiyarta, Rabi’a Labaran, wadda suke zaune a gida ɗaya bisa zargin aikata kisan." in ji sanarwar.
"Kishiyar dai ta amsa laifin cewa ita ta aikata kisan bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninsu da mamaciyar, wanda ya rikiɗe zuwa fada har ta kai ga wannan mummunan lamari” sanarwar ta ƙara da cewa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello Shehu, ya gargaɗi jama'a da su nisanci tashin hankali a cikin gida da kuma gujewa ɗaukar doka a hannu.
Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun hana babban malamin addinnin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi shiga ƙasar domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sheikh Gumi wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnatin Saudiyya bayan ta ba shi bizar shiga ƙasar domin aikin Hajji amma kuma sai ba a ba shi damar shiga Madina domin fara aikin ibada ba.
"Bisa waɗansu dalilai saboda ra'ayi na kan siyasar duniya, hukumomi a Saudiyya ba sa son kasancewata a Hajji duk da sun ba ni biza," in ji Sheikh Gumi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ƙara da cewa "Ina godiya ga hukumomi a Najeriya waɗanda suka sha alwashin tuntuɓar hukumomin Saudiyya a kan wannan lamarin."
Bayanan da BBC ta tattaro sun nuna cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na cikin tawagar malaman da hukumar aikin hajjin Najeriya - NAHCON ta ɗauki nauyi domin zuwa aikin ibada a Saudiyya.
Gumi ya isa Madina ne tare da sauran malamai a ranar Asabar ɗin da ta gabata da misalin karfe 10:30 na dare a cikin jirgin sama na kamfani Umza Air, amma da isarsu filin jirgin sama na birnin sai jami'an hukumar shige da fice na Saudiyya suka hana malamin shiga cikin ƙasar.
Bayanai sun nuna cewa a yanzu haka Sheikh Gumi ya koma Najeriya domin ci gaba da harkokinsa na yau da kullum musamman karantarwa.
Matsalolin da ke addabar jam’iyyar PDP sun ƙara tsananta a ranar Lahadi, bayan ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya janye daga duk wata yarjejeniya ta sulhu da aka taba cimmawa a cikin jam’iyyar adawar.
Wike dai ya ɗora alhakin rikicin PDP a kan gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, yana mai gargaɗin cewa rashin bin yarjejeniyoyin da aka cimma ne ke haddasa rikicin jam’iyyar, kuma ya bayyana Makinde a matsayin wanda ya fi haddasa wannan matsala.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Wike ya zargi manyan shugabannin jam’iyyar, ciki harda gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da cin amanar juna da rashin gaskiya da kuma karya yarjejeniyoyi da dama da aka cimma a baya.
Yayin da yake bayani kan asalin rikicin PDP tun bayan kammala zaɓen 2023, Wike ya zargi Makinde da gurɓata dukkan ƙoƙarin sasanci da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
Asalin hoton, EPA
Akalla Filasɗinawa 54 ne suka mutu a sakamakon hare-haren jiragen saman Isra’ila guda biyu da suka faru a cikin dare, ciki har da hari da aka kai wani makaranta da ke zama mafakar ‘yan gudun hijira a tsakiyar Gaza, in ji jami’an lafiya da na hukumar agajin gaggawa.
Makarantar Fahmi Al-Jargawi da ke birnin Gaza na zaman mafakar ɗaruruwan ‘yan gudun hijira daga garin Beit Lahia, wanda ke fuskantar mummunan hari daga sojojin Isra’ila a halin yanzu.
Kakakin hukumar agajin gaggawa da ke ƙarƙashin Hamas ya ce sun fitar da gawarwaki 20 daga cikin makarantar – ciki har da na yara – da dama daga cikinsu sun kone sosai bayan gobara ta tashi a dakunan karatu da aka mayar mafakar kwana.
Dakarun tsaron Isra’ila IDF sun ce sun kai harin ne kan wani “cibiyar jagoranci da tsara hare-hare na Hamas.
IDF ta bayyana cewa Hamas na amfani da wannan wajen shirya hare-hare akan fararen hula na Isra’ila da sojojin IDF, tare da zargin Hamas ɗin da amfani da jama’ar Gaza a matsayin “garkuwa” wajen kare kansu.
“Wuta ta mamaye ko’ina. Na ga gawarwaki da suka ƙone kwance a kasa,” in ji wani mazaunin yankin mai suna Rami Rafiq, cikin wata hira da BBC ta wayar tarho. “Har ɗa na ya suma bayan ganin wannan mummunan hali.”
Bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta ya nuna gobara mai ƙarfi tana cin sassan makarantar, inda aka ga hotunan gawarwakin da suka kone matuƙa, ciki har da yara, da kuma waɗanda suka jikkata da munanan raunuka.