Shin akwai riga-kafin ƙyandar biri ta mpox, ko zai yi aiki a kan sabon nau'in cutar?

Hannun a cikin safa riƙe da kwalbar asibit da aka rubuta "allurar riga-kafin kyandar biri"

Asalin hoton, Reuters

  • Marubuci, Natasha Preskey
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Wani sabon nau'in ƙwayar cutar kyandar biri ya yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, sannan ya yaɗu zuwa wasu sassa na tsakiya da gabashin Afirka.

Tun a farkon wannan watan, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da ɓarkewar cutar a matsayin mai buƙatar kulawar gaggawa a duniya.

Sabon nau'in ƙwayar cutar mai suna Clade 1b ne yake jawo wannan cutar.

WHO ta ce ta tabbatar da cewa idan riga-kafin ya kai wuraren da aka fi buƙata yana da muhimmanci domin daƙile annobar.

Amma me muka sani game da riga-kafin kyandar birin, sannan wane ne ya fi kamata a yi wa allurar?

Shin akwai riga-kafin mpox?

Akwai riga-kafin kyandar biri biyu da WHO ta tabbatar - amma har yanzu ƙasashe da dama ba su amince da su ba.

WHO ta amince da riga-kafin MVA0BN ko kuma LC16, ko kuma ACAM2000 idan ba a samu waɗancan biyun ba.

A farkon wannan watan, hukumar ta ayyana dokar ta ɓaci a kan riga-kafin na mpox domin a samu sauƙin kai shi ga ƙasashe ƙanaana waɗanda har yanzu ba su sanar da amincewa da riga-kafin ba a hukumance.

Bisa wannan tsarin, ke nan ƙungiyoyi irin su Unicef da Gavi za su iya tarawa tare da raba allurar.

Sai dai har yanzu WHO ba ta ba da shawarar gudanar da riga-kafin na gama-gari, inda ta ce akwai buƙatar a fara ne da waɗanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar, da waɗanda suka samu haɗu da masu cutar ta mpox, da kuma waɗanda suke garurunwa da aka samu annobar.

Idan jami'an lafiya suka yi tunanin kana buƙatar allurar saboda wata tafiya da za ka yi, WHO ta ce za ka iya karɓar allurar.

A makon jiya, Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Turai wato (ECDC) ta shawarci matafiya su yi allurar idan za su yi tafiya zuwa wuraren da akwai annobar a Afirka.

Waɗanda suka yi allurar riga-kafin a baya, yanzu idan aka ƙara musu wani guda ɗayan ya wadatar, ba sai an yi guda biyu ba.

An shawarci waɗanda suka yi allurar da suka riƙa kara mata ƙarfi duk bayan shekara biyu zuwa 10 idan suka cigaba da kasancewa cikin waɗanda suka barazanar kamuwa da cutar.

Shin tsohon riga-kafin smallpox zai yi aiki a kan mpox?

Ƙwayar cutar da ke jawo Mpox na da dangantaka da na smallpox.

Allurar riga-kafin da dattawa suka yi domin smallpox zai iya ɗan bayar da kariya a kan mpox.

WHO ta tabbatar da yaƙar smallpox a shekarar 1980 (cuta mai yaɗuwa kaɗai da aka tabbatar mata da wannan matsayin), sannan aka dakatar da amfani da riga-kafin kimanin shekara 40 da suka gabata.

Shin akwai isasshen riga-kafin mpox?

Mai shekara shida da ke fama da cutar da ake zargi Mpox ce, a asibitin Yalolia da ke Tshopo, Democratic Republic of Congo, October 3, 2022.

Asalin hoton, Reuters

Hukumar Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa ta Afirka ta ce a "shirye" take domin tabbatar da samun allurar riga-kafin miliyan 10 a nahiyar zuwa shekarar 2025.

A DRC da Najeriya, a mako mai zuwa ne za a fara allurar riga-kafin a daidai lokacin da DRC za ta yi amfani da allurar da ta samu daga Amurka da Japan, ita kuma Najeriya ta samu nata ne daga Amurka.

Ministan Lafiya na DRC, Roger Kmba, ya ce ƙananan yara za a fara yi wa allurar domin cutar ta mpox ta fi kama ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara 15.

Hukumar Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa ta Afirka ta ce ta shiga yarjejeniya da wani kamfani a Denmark mai suna Bavarian Nordic domin yin amfani da kimiyyarsa wajen haɗa riga-kafin a nahiyar Afirka.

Kwanan nan WHO ta buƙaci kamfanonin haɗa magunguna da su fito da riga-kafinsu na mpox domin ko-ta-kwana, ko da kuwa ba a riga an tabbatar da ita ba.

Najeriya ta karɓa zagayen allurar na farko guda 10,000 a ranar Talata daga Amurka.

Ita kuma DRC ta ce Amurka ta mata alƙawarin allurar guda 50,000, sannan Japan ta mata alƙawarin guda miliyan 3.5.

Shin riga-kafin mpox ɗin na aiki?

WHO ta ce riga-kafin na mpox "yana ba da kariya daga cutar da wasu cututtuka".

Tun a farkon wannan makon, daraktan WHO na yanki a Turai, Dokta Hans Kluge ya ce mpox ba "sabuwar Covid ba ce"-duk kuwa da cewa an samu wani sabon nau'in- domin za a iya kiyaye yaɗuwarta-ta hanyar matakin kiwon lafiya da kuma samar da riga-kafi.

WHO ta ba da shawarar kauce wa kamuwa ko yaɗa cutar ta mpox bayan an yi allurar riga-kafin, domin tana ɗaukar makonni kafin ta faraaiki. Wasu mutanen ma wataƙila allurar ba za musu aiki ba.

Ko da ka kamu da mpox bayan allurar riga-kafin, za ta ba ka kariya daga wasu cututtukan da kuma kwanciya jinya.