Rufewa
Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu kawo muku wasu labaran.
Dafatan za mu kwana lafiya.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/05/2025
Haruna Ibrahim Kakangi da Abdullahi Bello Diginza da Aisha Aliyu Jaafar
Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu kawo muku wasu labaran.
Dafatan za mu kwana lafiya.
Asalin hoton, Embassy of Israel to the USA
Kotu a Amurka na tuhumar Elias Rodriguez, mutumin da ake zargi da kisan ma'aikatan ofisihin jakandancin Isra'ila a Amurka da laifin kisan kai.
Tun da farko babbar lauyar ƙasa ta Amurka, Pam Bondi, ta yi iƙirarin cewa shi kaɗai ne ya kitsa ya kuma aikata kisan da aka yi wa ma'aikatan a Washington a daren jiya Laraba.
Ta ce an ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, kuma ta yi kira ga dukkan addinai da su hada kai domin zaman lafiya.
Ta ce mutum ko bayahude ne ko ba bayahude ba ya kamata ya kasance a ankare domin mutanen biyu ba su taba tsammanin haka zai faru da su ba ganin cewa sun fito ne daga taro na addini tare da yanuwa da abokan arziki.
A wani bangare kuma Faransa ta yi watsi da iƙirarin da ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Sa'ar ya yi na cewa gwamnatocin Turai na haifar da ƙiyayya kan Isra'ila, wanda a cewarsa hakan ne ya haddasa harin.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Faransa Christophe Lemoine ya bayyana zargin nasa a matsayin mara tushe balle makama .
Gwamnatin Mauritius ta yaba da yarjejeniyar da aka ƙulla da ta damka mata ikon mallakar tsibiran Chagos bayan shekaru da dama ana takaddma kan batun.
Firaminista, Navin Ramgoolam, ya faɗi hakan ne bayan wani taron rattaɓa hannu da aka yi ta intanet da takwaransa na Birtaniya, Keir Starmer.
Yarjejeniyar ta baiwa Biritaniya da Amurka damar ci gaba da amfani da sansanin sojin da ke yankin ƙarkashin yarjejeniyar shekara casa’in da tara.
Mauritius, wadda ta kasance ƙarkashin mulkin mallakan Birtaniya -- ta dade tana iƙirarin cewa an tilasta mata mika tsibirin na Chagos ne don samun ƴancin kanta fiye da shekara hamsin da suka gabata
Asalin hoton, AP
Hukumar samar da abinci ta Majalisar ɗinkin ɗuniya (WFP) ta ce fiye da ƴan gudun hijira dubu 700 a Kenya za su sami kashi 1 ne kawai bisa huɗu na abincin da suke buƙata daga wata mai zuwa saboda katse tallafi.
WFP na daga cikin waɗanda katse tallafin ƙasashen waje da gwamnatin Trump ta yi ya shafa, wanda kuma Amurka ce ta fi ba ta tallafi mai tsoka.
Hukumar ta ce an tilasta mata rage tallafin abinci da take bayar wa zuwa matakin da bata taɓa gani ba.
Hakazalika ta kuma dakatar da bayar da tallafin kuɗi ga ƴan gudun hijira.
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Trump ta ƙara matsa kaimi a taƙaddamar da ke tsakaninta da ɗaya daga cikin manyan jami'o'in Amurka, Harvard, inda ta haramta mata ɗaukar dalibai yan kasashen waje.
Sakatariyar tsaron cikin gida, Kirsti Noem, ta ce an ɗauki matakin ne domin a kawar da kyamar Amurka da ƙin jinin yahudawa a harabar jami'ar.
A wata wasiƙa da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta ce haramcin zai fara aiki ne nan take.
Ta ce daliban ƙasashen waje da ke jami'ar a halin yanzu sai dai su koma wata makarantar.
Hukumar jami'ar Harvard ta bayyana matakin a matsayin abin da ya sabawa doka.
Fiye da kashi ashirin da biyar cikin ɗari na ɗalibanta suna zuwa ne daga ƙasashen waje, lamarin da ke samar da kuɗaɗe masu dimbin yawa ga jami'ar.
Asalin hoton, TINUBU/X
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar wakilan ƙasar ta duba tare da amincewa da kasafin kuɗin jihar Rivers na naira triliyan ɗaya da biliyan 48.
Kakakin majalisar Abbas Tajudeen ne ya karanto saƙon da shugaban ya aike wa majalisar a fadar majalisar a yau.
A cikin wasiƙar, shugaba tinubu ya ce idan an amince, shugaban riko na jihar Vice iral Ibok-Ete Ibas mai ritaya zai yi amfani da kasafin kudin wajen samar da ilimi wanda zai laƙume sama da naira biliyan 75, da lafiya da za a kashe naira biliyan 166, da ayyukan noma da zai laƙume sama da naira biliyan 31, da samar da magunguna kyauta wanda zai kwashi naira biliyan biyar da dai sauransu.
Bayan karanto wasiƙar shugaban ƙasar, kakakin majalisar ya miƙa ƙasafin kuɗin ga kwamitin da aka kafa domin sanya ido kan dokar ta-ɓaci da aka sanya a jihar ta Rivers domin su duba su kuma kawo rahoto nan ba da jimawa ba.
A ranar 18 ga watan Maris na 2025 shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Asalin hoton, Reuters / Getty Images
Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce gwamnatin Tehran za ta ɗorawa Amurka alhakin duk wani harin da Isra'ila ta kai kan cibiyoyinta na nukiliya.
Abbas Araghchi ya yi wannan gargaɗin ne bayan wani rahoto da kafafen yaɗa labaran Amurka suka fitar na cewa Isra'ila na shirin kai hari.
Ya zargi Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da yunƙurin wargaza tattaunawar nukiliyar da ake yi tsakanin Amurka da Iran da za a ci gaba da zama a birnin Roma gobe Juma'a.
Wannan dai shi ne karo na biyar na ganawa tsakanin ɓangarorin biyu tun tsakiyar watan Afrilu.
Asalin hoton, BOLA TINUBU
Zaɓaɓɓun gwamnoni ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun goyi bayan shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Gwamnonin sun yi hakan ne a taron ƙoli na jam'iyyar karo na farko da aka yi a yau.
Gwamnan jihar Imo, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma ne ya kawo buƙatar goyon bayan shugaba Tinubu, yayin da gwamnan jihar Kaduna Uba sani kuma ya mara masa baya.
Daga baya kuma gwamnan ya miƙa tambayar ga taron inda masu amincewa da buƙatar suka yi rinjaye.
Duk da dai shugaban bai kammala cike shekara biyu kan mulki ba, batun zaɓen 2027 ya mamaye fagen siyasar ƙasar.
Asalin hoton, Getty Images
Wani gidan burodi na Majalisar ɗinkin duniya da ke tsakiyar Gaza ya ci gaba da aiki kwanaki huɗu bayan Isra'ila ta sanar da sauƙaƙa matakan ta na toshe shigar da kayan agaji na makonni 11.
An bai wa motoci ƙalilan ɗauke da fulawa da wasu kayyayaki damar shiga, sai da ƙungiyoyin agaji sun ce ana buƙatar ƙarin wasu da dama.
A ƙiyasi sun ce ana buƙatar aƙalla manyan motoci biyar maƙare da kaya duk rana.
Ƙungiyar likitoci ta MSF ta ce har zuwa yanzu ba ta sami kayyayakin kula da lafiya ba tun farkon watan Maris, kuma ba za ta iya ci gaba da kula da ɗimbim mutanen da ke buƙatar kulawa ba.
Sojojin Isra'ila sun bayar da ƙarin umurnin ficewa daga unguwannin da ke arewacin Gaza a yayin da take cigaba da zafafa kai hare-hare.
Asalin hoton, Shekarau New Media Facebook
Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau ta ce za ta goyi bayan sabuwar haɗakar ƴan hamayya ta National Coalition Group ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark domin tunkarar zaɓen 2027.
A wata sanarwar bayan taron da ƙungiyar ta yi ranar Alhamis, ND ta ce duk da amincewar da ta yi na shiga haɗaka, amma za su ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tattaunawa yiwuwar kafa sabuwar jam'iyya ko kuma shiga wata jam'iyyar domin yin tafiya tare.
Harwayau, ƙungiyar ta Northern Democrats ta ƙara da cewa sun amince da matsa wa gwamnati lamba musamman jagorancin majalisar dokoki wajen ganin an tabbatar da bin tsarin mulkin ƙasar sau da ƙafa.
Daga ƙarshe ƙungiyar ta ce mambobinta sun amince su tattauna da jihohin arewacin ƙasar 19 dangane da halin-ko-in-kula da ake ciki dangane da yanayin da yankin yake ciki da suka haɗa da talauci, rashin aikin yi da rashin tsaro.
Pakistan ta gargaɗi makwabciyarta Indiya da kada ta yi amfani da ruwan sha a matsayin makamin yaƙi, bayan da Delhin ta ce Pakistan ba za ta ƙara samun ruwa daga kogunan da take iko da su ba.
Babban lauyan gwamnatin Pakistan, Mansoor Usman ya ce ƙasarsa na fatan magance matsalar da aka samu kan yarjejeniyar ruwa tsakaninta da Delhi, wadda Indiyan ta dakatar da watan da ya gabata, bayan da wasu ƴanbindiga suka kai hari a yankin da Kashmire da Indiya ke iko da shi, tare da kashe mutum 26.
Kalaman Mista Usman na zuwa ne bayan da Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya ce Indiya za ta yi amfani da ruwanta na kogunanta da suka rasa zuwa Pakisatan.
Delhi ta zargi Islamabad da kashe-kashe a Kashmir, zargin da Pakistan ta musanta.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙalubalanci Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu kan zarge-zargen "kisan kiyashi" kan fararen fata a Afirka ta Kudu, inda ya sa aka kunna wasu bidiyoyi.
Ramaphosa ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya ce mafi yawan mutanen da ake kashewa a rikice-rikice a ƙasar baƙaƙen fata ne.
Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce gwamnatin Tehran za ta ɗora wa Amurka alhakin duk wani harin da Isra'ila ta kai kan cibiyoyin nukiliyarta.
Abbas Araghchi ya yi wannan gargaɗin ne bayan wani rahoto da kafafen yaɗa labaran Amurka suka fitar na cewa Isra'ila na shirin kai hari.
Ya zargi Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da yunƙurin wargaza tattaunawar nukiliyar da ake yi tsakanin Amurka da Iran da za a ci gaba da zama a birnin Roma gobe Juma'a.
Wannan dai shi ne karo na biyar na ganawa tsakanin ɓangarorin biyu tun tsakiyar watan Afrilu.
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sabon ragin farashin man fetur a gidajen da ke hulɗa da shi.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis ya ce ragin ya bambanta daga yankunan ƙasar daban-daban.
Kamfanin ya ce za a riƙa sayar da litar mansa a Legos kan naira 875, yayin da za a riƙa sayar da litar a jihohin arewa maso yamma kan naira 895, sai kuma naira 905 a jihohin arewa maso gabashin Najeriya.,
Asalin hoton, Dangote/X
Shugaban rundunar sojin Bangladesh ya ce za a gudanar da zaɓen farko a ƙasar, cikin watan Disamba, karon farko tun bayan hamɓarar da tsohuwar firaministar ƙasar, Sheikh Hasina
Janar Waker-Uz-Zaman ya faɗa wa jami'an sojin ƙasar cewa zaɓaɓɓiyar gwamnati ce kawai za ta iya ɗaukar wasu manyan matakan da suka shafi tsaro.
Tun bayan boren da ƴanƙasar suka gudanar a watan Agustan shekarar da ta gabata ne, gwamnatin riƙon ƙwarya - ƙarƙashin jagorancin Muhammad Yunus , wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel - ke jagorantar ƙasar.
Tun bayan hawanta, gwamnatin riƙon ta gaza sanya ranar gudanar da zaɓen ƙasar, to amma wasu jami'anta sun alƙawarta gudanar da shi cikin watan Yunin shekara mai zuwa.
Asalin hoton, State House
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da taron ƙoli, karo na farko gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.
Mahalarta taron, wanda ke gudana a yau Alhamis su ne Shugaban ƙasar, Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da kuma shugabannin Majalisar Dattaijai da Wakilai da mataimakansu.
Haka nan gwamnonin jam'iyyar masu ci da kuma tsofaffi suna cikin waɗanda aka gayyata domin halartar taron.
Wannan na zuwa ne gabanin cikar shugaban na Najeriya shekara biyu da kama mulki, daidai lokacin da ake ganin jam'iyyar na ƙara samun tagomashi sanadiyyar tuɗaɗar ƴan adawa zuwa cikin jam'iyyar daga sauran jam'iyyu.
Jam'iyyun adawar ƙasar da dama na fama da rikicin cikin gida, ciki har da babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar - PDP, wadda ake kyautata zaton ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar ya kammala tattaunawar yin haɗaka da wasu manyan ƴan adawa a wata jam'iyyar ta daban.
Jam'iyyun adawar na zargin APC da yi wa ƴan adawar alƙawurra masu gwaɓi domin janyo su zuwa cikinta, lamarin da jam'iyyar ta sha musawa.
Sanarwar taron ƙolin na APC ta ce ɗaya daga cikin abin da za a tattauna shi ne duba manufofin Tinubu tun bayan kama mulki.
Shugaba Tinubu dai ya bijiro da sabbin manufofi a ƙasar daga ranar da aka rantsar da shi, inda wasu daga cikinsu suka sauya lamurran ƙasar.
Al'ummar ƙasar sun koka kan faɗawa cikin rayuwa mai tsanani bayan cire tallafin man fetur da kuma wasu matakai da gwamnatin ta ɗauka a fannin tattalin arziƙi.
Haka nan matsalar tsaro na ci gaba da addabar yankunan ƙasar duk da matakan da gwamnatin ke cewa tana ɗauka.
Sai dai masu kare gwamnatin na cewa matakan da shugaban ya ɗauka a fannin tattalin arziƙi za su yi amfani ga ƙasar a nan gaba.
Asalin hoton, Reuters
Manyan motci ɗauke da kayan agaji, musamman fulawa sun shiga Zirin Gaza ta mashigar Kerem Shalom bayan mako 11 da Isra'ila ta yi tana hana shigar da agaji yankin.
Majalisar Dinkin Duniya da shirin samar da Abinci na Majalisar sun ce a ranar Laraba an shigar da motoci aƙalla 90, wadanda a yanzu suka isa wuraren ajiyar abinci, inda kuma aka kai fulawar gidajen burodi.
A gefe guda kuma Isra'ila ta ci gaba da hare-harenta a cikin dare, tare da kashe aƙalla mutum 10 a tsakiyar Gaza.
Sojojin Isra'ial sun ce bayar da umarni ga mazauna wurare 14 a arewacin Gaza, ciki har da Beit Lahia da Jabalia su tashi daga wuraren.
Dakatan asibitin al-Awda da ke Jabalia sun ce dakarun Isra'ila sun kai hari kan asibitin, inda suka lalata asibitin.
Asalin hoton, Nigerian Police/X
Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata tsohuwa mai shekara 80 da aka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar Kano.
Kakakin Rundunar ƴansandan jihar SP Lawan Adam Shiisu Adam ya ce mutanen da suka yi garkuwa da tsohuwar sun ɓoye ta a cikin wani daji na jihar Jigawa mai makwabtaka.
''Bayan sace tsohuwar, barayin sun tafi da ita wasu dazuka da ke tsakanin ƙananan hukumomin Garki da Sule Tankarkar, daga nan ne jami'ansu tare da haɗin gwiwar ƴanbijilanti da na ƙungiyar ƴanbulala suka far wa maharan, bayan ɗauki-b-daɗi kuma suka samu nasarar ceto ta''
SP Shiisu ya ce jami'ansu sun yi nasarar kama wasu manyan ƴanfashin daji biyar da aka jima ana nema ruwa-a-jallo.
''Daga ciki akwai wanda ma har yana tsallakawa jamhuriyar Nijar ya kuma aikata laifuka a can,'' in ji shi.
Ya ƙara da cewa jami'an sun ƙwato bindigogi irar AK-47 guda biyu, da ƙiarar GPM da aka fi sani da mai jigida, guda ɗaya sai wayoyin hannu da kuma babura.
Asalin hoton, Tajudeen Abbas/X
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ceto ƴanƙasar da ke maƙale a Saudiyya sakamakon sabbin sauye-sauyen dokokin ayyukan ƙwadogo da hukumomin Saudiyya suka bijiro da su.
Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Shehu ne ya gabatar da udurin a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
A baya-bayan nan ne dai hukumomin Saudiyya suka bijiro da wasu sauye-sauye kan dokokin da suka shafi ayyukan baƙi a ƙasar, ciki har da daina sabunta takardun izinin aiki a ƙasar ga wasu mutanen.
Hon. Muhammad Shehu ya ce sauye-sauyen sun tilasta wa wasu ƴan Najeriya da dame da ke zaune a Saudiyya rasa ayyukansu, yayin da wasu ke fuskantar tsadar kuɗin sabunta takardunsu.
“Ɓangaren zartarwa ta hannun ma'aikatar kula da harkokin ƙasashen waje ba su tuntuɓi hukumomin Saudiyya kan wannan batu ba da nufin samar wa ƴanƙasarmu sauƙi, ko yin wani shiri na kwaso mutanen domin maido su Najeriya ba'', kamar yadda ya bayyana.
Haka kuma ɗan majalaisar ya yi kira ga hukumomin Saudiyya ta sassauta tare da yin la'akari ga mutanen da ke da sha'awar komawa gida.
Asalin hoton, Reuters
Masu bincike a Amurka sun ce ya kamata a bai wa sauro magungunan maleriya domin kawar da ƙwayar cutar tun daga jikin sauro masu sauro ta yadda ba za su iya yaɗa ta ba.
Tawagar binciken da ke jami'ar Harvad ta gano wasu magunguna da za kawar da cutar daga jikin sauro idan suka zuƙe shi ta ƙafafunsu.
Za a shafa maganin a jikin gidan sauro ta yadda saurayen za su riƙa sauka a kai, suna zuƙar maganin, saboda cikin dare suka fi yaɗa zazzaɓin na maleriya, a cewar masu binciken
A ƙasashe da dama, sauro ba ya jin magani, inda suke yaɗa cutar - wadda ke cikin jerin cutakan da suka fi kisa a duniya.
Wani rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa rashin jin magani ya sa malariya na kashe fiye da mutum 500,000 - mafi yawancinsu ƙananan yara - a kowace shekara.