Yadda iyakar Pakistan da Indiya ta zamo mai tsananin hatsari a duniya

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Soutik Biswas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, India correspondent
- Twitter,
Rayuwa a iyakar da ta haɗa Pakistan da Indiya watau (LoC) - rayuwa ce ta har abada cikin fargaba tsakanin zaman lafiya da rikici.
Rikici na baya-bayan nan bayan hari a Pahalgam ya sake rura wutar rashin jituwa tsakanin Indiya da Pakistan. An yi ruwan harsashai a ɓangarorin biyu na LoC, lamarin da ya rusa gidaje. Aƙalla mutane 16 ne aka ruwaito an kashe a bangaren Indiya, yayin da Pakistan ta yi iƙirarin mutuwar fararen hula 40, kodayake ke ba a san adadin waɗanda harin ya rutsa da su kai tsaye ba.
"Iyalan da suke iyakar, wadda ake yi wa lakabi da LoC na ɗanɗana kuɗar su duk lokacin da Indiya da Pakistan suka gauraya," Anam Zakaria wata marubuciya ce ƴar Pakistan da ke zaune a Canada, ta shaida wa BBC cewa:
“A duk lokacin da harbe-harbe ya ɓarke mutane da dama na fakewa cikin ɗakunan ƙasa, ana asarar dabbobi da abubuwan more rayuwa, sannan lalacewar gidaje da asibitoci da makarantu ta yi tasiri a rayuwar mazauna yankin ta yau da kullun," in ji Ms Zakaria, marubuciyar wani littafi kan Kashmir da Pakistani.
Indiya da Pakistan na amfani da iyaka ɗaya mai kilomita 3,323 (mil 2,064), tare da LoC mai tsawon kilomita 740; da iyakar ƙasa da ƙasa (IB), wadda ta kai kusan kilomita 2,400. An fara aiki da LoC bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a shekara ta 1949 bayan yakin Indiya da Pakistan na farko, kuma an sake mata suna a ƙarƙashin Yarjejeniyar Simla ta 1972.
Hanyar LoC da ta ratsa ta cikin Kashmir - ta kasance ɗaya daga cikin iyakokin da aka fi jibge jami’an tsaron sojoji a duniya. Ba wuya rikici sai ya tashi kuma ko da an tsagaita wuta nan take sai wani rikicin ya sake ɓallewa.
Matakan karya yarjejeniyar tsagaita wuta sun haɗa da "harbin bindiga ko mamayar filaye'', in ji Happymon Jacob ƙwararre kan manufofin ƙasashen ƙetare a Jami'ar Jawaharlal Nehru ta Delhi (JNU). (Karbe filaye zai iya haɗawa da karɓe muhimman wurare kamar kan tsauni da gefen gari da kuma sansanin dakarun tsaro.)
Masana sun bayyana LoC a ''matsayin iyakar da aka raba ta hanyar amfani da jini sakamakon rikici". Ms Zakaria ta ce layi ne da "Indiya da Pakistan suka ƙirƙira, kuma aka yi amfani da su wajen yaƙi da makamai, ba tare da la'akari da al'ummar Kashmir ba".

Asalin hoton, Getty Images
Irin waɗannanm iyakoki ba su yi fice a Kudancin Asiya ba. Sumatra Bose farfesa a fannin siyasar ƙasa da ƙasa a jami'ar Krea da ke Indiya kuma marubuciyar Kashmir at the Crossroads: ta bayyana cewar iyakar da aka fi sani ita ce s 'Green Line' - iyakar da aka samar bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a shekara ta 1949 - iyaka ce tsakanin Isra'ila da Gabar Yamma da Kogin Jordan.
Babu mamaki yadda kwanciyar hankalin da aka samu a iyakar LoC tun shekara ta 2021 tsakanin maƙotan ƙasashen masu makaman nukiliya ta rushe bayan ɓallewar rikici tsakanin su a baya bayan nan.
''Tabarbarewar yanayin a yanzu a kan LoC da iyakar ƙasar waje (IB) na da mahimmanci bayan shekaru huɗu na zaman lafiya a kan iyakar," Surya Valliappan Krishna a Carnegie India ta shaida wa BBC.
Rikici tsakanin Indiya daPakistan ba sabon abu ba ne, kafin yarjejeniyar tsagaita wuta a shekara ta 2003, Indiya ta bayar da rahoton yadda aka karya yarjejeniyar sau 4,134 a shekara ta 2001 da kuma 5,767 a shekara ta 2002.
Da farko dai an fara tsagaita wuta a shekarar 2003, an fara karya yarjejeniyar daga shekara ta 2004 zuwa 2007, amma tashe-tashen hankula sun sake kunno kai a cikin shekara ta 2008 kuma ya ƙaru sosai nan da 2013.
Tsakanin shekara ta 2013 zuwa farkon shekara ta 2021 LoC da IB sun shaida ci gaba da yawan rikice-rikice. Sabon tsagaita wuta a watan Fabrairun shekara ta 2021 ya haifar da raguwar karya tsagaita wutar har zuwa watan Maris shekara ta 2025.
''Ya yin tsananin harbe-harbe a kan iyakoki, mun ga yadda al'ummar da ke zaune a kan iyaka suka rasa muhallansu tsawon watanni," in ji Mista Krishna. A tsakanin karshen watan Satumba zuwa farkon Disamba shekara ta 2016, fiye da mutane 27,000 ne suka tsere daga yankunan kan iyaka saboda an karya tsagaita wuta a kan iyaka.

Asalin hoton, Getty Images
Rikici ya tashi bayan an kai hari Pahalgam, inda Indiya ta dakatar da ruwan da ta ke rabawa tsakaninta da Pakistan kamar yadda ya ke ƙunshe cikin yarjejeniyar Indus Waters Treaty (IWT). Pakistan ta mayar da martani ta hanyar barazanar ficewa daga yarjejeniyar Simla Agreementa ta shekara ta 1972, wadda ta tabbatar da LoC a hukumance.
''Wannan yana da mahimmanci saboda Yarjejeniyar Simla ita ce dalilin ƙirƙirar LoC a yanzu, wadda bangarorin biyu suka amince da cewa ba za su sauya ba duk da bambance-bambancen siyasa da ke tsakanin su, "in ji Mista Krishna.
Mista Jacob ya bayyana manyan abubuwa guda biyu da ke haifar da karya yarjejeniyar kamar haka: Pakistan sau da yawa tana amfani da tashin gobara don sauƙaƙawa ƴan tada ƙayar baya su kutsa cikin yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi, wanda ya sha fama da ƴan tada ƙayar baya sama da shekaru talatin. Sannan Pakistan na zargin Indiya da harbe-harbe a yankunan fararen hula.
Yawancin kwamandoji ne ke fara tayar da rikicin a wasu lokutan tare da amincewar shugabannin su. Ya kuma ƙalubalanci cewar Sojojin Pakistan ne kaɗai ke karya ƙa'ida yana mai nuni da ƴancin cin gashin kai da aka bai wa sojojin kan iyaka na bangarorin biyu.

Asalin hoton, Getty Images
''Wannan shawara ba mai yiwuwa ba ce, taswirorin Indiya sun nuna ɗaukacin yankin Jammu da Kashmir a matsayin wani bangare na Indiya," Sumantra Bose ya shaida wa BBC.
A cikin littafinsa na shekara ta 2003: mai sunan Roots of Conflict, Paths to Peace, Farfesa Bose ya rubuta cewa: "Zaman lafiya a Kashmir na buƙatar canza LoC - daga labulen ƙarfe da ɗakunan ƙarƙashin ƙasa da shinge da kuma sojoji, a siyasar gaskiya ana samar da iyaka ne ta din-din-din, wadda ba za a iya kau da ita ba.''
A yau iyakar ta sake kunna rikice-rikice da rashin tabbas da fargaba ga waɗanda ke zaune a inuwar ta.
''Ba wanda ya san abinda zai faru nan gaba. Babu wanda zai iya bacci yana fuskantar wani layi da ake iko da shi''. kamar yadda wani ma'aikacin otal a yankin Kashmir da ke Pakistan ya shaida wa BBC Urdu ya yin rikicin na baya-bayan nan.
Tunatarwa ce game da yadda zaman lafiya ya ke da rauni a lokacin da tagar ɗakin ka ke kallon fillin daga ko filin yaƙi.