'Ko na zama shugaban ƙasa ba zan manta uƙubar da nake sha a Libya ba'

An yi amannar cewa akwai ɗaruruwan matasan Najeriya da ke maƙale a Libya waɗanda ba su iya bin hanyar da suka bi zuwa ƙasar domin komawa gida saboda hatsarinta, kuma ba su da wata hanyar da ta fi ta aminci balle su bi domin komawa gidan

Asalin hoton, Mukhtar

Bayanan hoto, An yi amannar cewa akwai ɗaruruwan matasan Najeriya da ke maƙale a Libya waɗanda ba su iya bin hanyar da suka bi zuwa ƙasar domin komawa gida saboda hatsarinta, kuma ba su da wata hanyar da ta fi ta aminci balle su bi domin komawa gidan
  • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Twitter,
  • Aiko rahoto daga Abuja

"Wallahi yanzu haka in da zan bayar da duk abin da na mallaka don in koma gida zan yi hakan, idan na koma gida sai na zuba ruwa a ƙasa na sha, na yi sujada don gode wa Ubangiji."

Wannan ne kalami na ƙarshe da Mukhtar ya faɗa min a tattaunawar da na yi da shi game da tafiyarsa da kuma zaman da yake yi yanzu haka a Libya.

Yana daga cikin dubban matasan da ke ficewa daga ƙasashen Yammacin Afirka domin zuwa neman rayuwa mai kyau a ƙasashen Turai ta ɓarauniyar hanya, waɗanda akasarinsu kan faɗa tarkon ƙungiyoyin masu riƙe da makamai a ƙasashen yankin arewacin Afirka.

Da dama daga cikinsu kan gamu da ajalinsu, ko dai a kan hanyarsu ta tafiya ko kuma a lokacin da suka tsinci kansu a ƙasashe irin Libya inda ƙungiyoyin ƴanbindiga ke yaƙi da juna sanadiyyar raunin hukumomi.

Su kuma waɗanda kan ci sa'a su isa ƙasashen da ke iyaka da tekun meditaraniya, yawancinsu kan maƙale, su kasa gaba su kasa baya, inda suke shiga rayuwa mai tattare da ɗimbin ƙalubale.

Kamar sauran matasan da ke ci gaba da haɗa kayansu yanzu haka suna kama hanya, shi ma Mukhtar ya samu labarin hatsarin da ke tattare da irin wannan tafiya, amma bai yi tunanin abin ya yi muni kamar yadda jikinsa ya gaya masa ba a yanzu.

Ɗaya daga cikin abin da ya sanya Libya ta kasance hanya mafi hatsari ga irin waɗannan matasa shi ne halin da ƙasar ke ciki na rashin ƙwaƙƙwarar gwamnati tun bayan kashe shugaban ƙasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011.

Tun daga wancan lokaci ne ɓangarori biyu ke ja ni in ja ka domin nuna ƙarfin iko, tsakanin gwamnatin ƙasar da ke Tripoli ƙarƙashin jagorancin Abdelhamid Dbeibah, wanda ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, sai kuma gwamnatin da ke Tobruk a gabashin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Khalifa Haftar.

Baya ga haka nan ƙananan ƙungiyoyin masu riƙe da bindiga na cin karensu babu babbaka a sassa da dama na ƙasar.

Wannan ya sanya matasan da ke bin hanya domin ratsawa ta Libya a ƙoƙarin isa Turai a mafi yawan lokuta kan faɗa hannun ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, inda wani lokaci ake mayar da su tamkar bayi ko kuma a riƙa cinikayyar su tamkar kayan sayarwa.

Duk da cewa gwamnatin Najeriya kan kwashe mutanenta da suka maƙale a Libya lokaci zuwa lokaci, amma matsalar ba za ta ƙare ba kasancewar a kowace rana akan samu masu ɗaukar kasadar bin hanyar mai hatsari da niyyar isa ƙasashen Turai.

Shugabar hukumar kula da ƙaurar jama'a a Jamhuriyar Nijar, Fatsuma Dankaou ta shaida wa BBC cewa yawan matasan da ke bi ta Nijar domin tsallakawa zuwa ƙasashen da ke arewacin Afirka sun zama wa ƙasar babbar matsala.

Ta ce yayin da ƙasar Nijar ke ƙoƙarin yaƙi da matsalar tsaro da kuma talauci da ke addabar mutanenta, matasa ƴan ci rani waɗanda ke maƙalewa a ƙasar sanadiyyar ƙarewar guzuri ko kuma waɗanda aka koro su daga ƙasashe irin su Algeria da Libya kan zame wa ƙasar ƙarin nauyi.

Ta ƙara da cewa lamarin na haifar da asarar mutane da dama a cikin hamadar Sahara saboda yunwa da rashin kyakkywan yanayi.

Turbar Turabulus

Dubban ƴan ci-rani daga wasu ƙasashen Afirka ne ke bin hanya mai cike da hatsari da nufin tsallakawa zuwa ƙasashen Turai domin neman abin duniya

Asalin hoton, Mukhtar

Bayanan hoto, Mukhtar a cikin Sahara kan hanyarsa ta zuwa Libya a watan Disamban 2023

Baya ga rashin aikin yi da talauci, ta ɓangaren Mukhtar abin ya haɗu masa kashi biyu, domin yana daga cikin waɗanda suka yi hijira daga ƙauyukansu zuwa cikin birnin Maiduguri sanadiyyar rikicin Boko Haram - ƙungiyar da ta shafe sama da shekara 10 tana kai wa fafaren hula da jami'an tsaro hare-hare da sunan jihadi a yankin tafkin Chadi.

Mukhtar, wanda yanzu haka ke zama a Tripoli babban birnin ƙasar Libya yana aiki tare da wani ɗan kasuwa a matsayinmai tafinta, ya kama hanya ne ba tare da neman shawarar iyalansa ba domin gudun kada su hana shi tafiya, bisa yaƙinin cewa idan ya je zai samu dukiyar da zai tallafa wa iyalan nasa.

Duk da cewa ya kammala karatunsa na babbar difloma, ya bayyana rashin aikin yi da taɓarɓarewar tsaro a yankinsa na arewa maso gabashin Najeriya a matsayin manyan dalilan da suka sa ya bi zugar zuciyarsa.

Bayan ya bar gida Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya tafi Kano inda daga nan ne tafiyarsa 'zuwa Turai' ta soma.

Daga Kano ne ya kama hanya zuwa Agadez a Jamhuriyar Nijar, sannan bayan wasu kwanaki aka loda su cikin mota suka yi tafiyar kwana 12 a cikin Sahara kafin isa garin Qatrun da ke cikin ƙasar ta Libya.

Sai dai bayan tsallake waɗancan wurare, Mukhtar ya faɗa hannun hukumomi yayin da ya tashi daga birnin Sabha a ƙoƙarin isa Tripoli.

"Mun isa wata cibiyar binciken ababen hawa inda aka tambaye ni inda na fito da kuma takardu, to amma ba ni da su.

"Suka ce min 'inta kilifti', wato kai mai laifi ne.

Daga nan ne suka kama mu gaba ɗaya baƙaƙen fata, akwai ƴan Sudan da ƴan Chadi da kuma Nijar, aka ingiza mu gidan yari a Misrata."

A lokacin da yake bayyana irin tafiyar da suka yi, ya ce: "An zuba mu a cikin motar dabbobi, wasu kan wasu, aka ɗora mana buhuna domin ɓoye mu sannan aka rufe mu da tamfal babu ko wurin shan iska.

"Wallahi ba na fatan ko da maƙiyina ne ya bi wannan hanyar ta Sahara zuwa Libya."

Daga nan ne aka kwashe su zuwa wani gidan yari a birnin Tripoli, inda rashin lafiya ya kwantar da Mukhtar.

Bayan gaza yi masa magani a asibitin gidan yari, sai aka kai shi asibitin cikin gari inda a nan ne ya samu lafiya, sannan ma'aikatan lafiya suka taimaka masa ya tsira daga komawa gidan yari.

Yanzu haka Mukhtar na aikin tafinta ƙarƙashin wani balarabe ɗan ƙasar Masar mai sayar da kaya a birnin na Tripoli.

'Wahalar da ba zan taɓa mantawa da ita ba'

...

Asalin hoton, Reuters

"Ka san ni ɗan Maiduguri ne, na yi gudun hijira tun daga Baga har Maiduguri a ƙafa, amma wahalar da na sha wadda ba zan taɓa mantawa da ita ba a duniya ita ce wadda na sha a gidan yarin Tripoli, ko da a ce zan zama shugaban ƙasa, ko ma wane matsayi zan kai a duniya ba zan taɓa mantawa da wahalar ba."

"Na sadakar kawai, ban zata zan fita da rai ba. Na fita daga hayyacina, sai dai idan na farfaɗo na rinƙa salati kawai."

Babu mafita

A watan Maris, Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NiDCOM) ta sanar da cewa ta kwashe ƴan Najeriya 956 daga ƙasar Libya a cikin watanni uku na farkon 2025, ta hanyar haɗin gwiwa da Hukumar kula da ƙauran al'umma ta duniya (IOM) da wasu hukumomi daban-daban.

To amma duk da haka da alama akwai ƴan Najeriya jibge a ƙasar ta Libya waɗanda babban fatansu a rayuwa shi ne su koma gida, sai dai hakan ba ta yiwu ba kuma babu alamar za su samu hakan a nan kusa.

Mukhtar ya shaida min cewa ya sha zuwa ofishin jakadancin Najeriya domin ganin ko zai samu shiga cikin waɗanda gwamnati ke kwasa tana mayar da su gida, to amma abin ya ci tura. "Mutane ne sun cika wurin kamar kasuwa, babu ma takardar da za ka cika.

"Amma sun faɗa min cewa an fi mayar da hankali kan mata da kuma waɗanda ke cikin gidan yari.

"Yanzu haka ƙasar nan ban san yadda zan fita na bar ta ba saboda rikice-rikicen da ke kan hanya idan na ce zan bi ta ƙasa. Sannan kuma ko da kana da kuɗi ba za ka iya samun damar shiga jirgi ba saboda mutum ba ya da takarda."

"Wallahi zuwa ƙasar nan (Libya) ba shi da alfanu, don mu yanzu in da za mu samu mu koma gida ba abin da ya fi mana haka daɗi, da shi muke kwana da shi muke tashi."

Wane aiki baƙaƙen fata ke yi a Libya?

Yawancin matasan da ke isa Libya da nufin tsallakawa zuwa ƙasashen Turai mutane ne waɗanda ba su yi karatu mai zurfi ba, kuma da daman su ba su da ƙwarewa a wata sana'a.

Ko da ma suna da karatun ko kuma ƙwarewa, kasancewar sun shiga ƙasar ne ba bisa ƙa'ida ba zai yi wahala su samu wani aiki mai kyau.

Duk da cewa Mukhtar na da shaidar takarda da ke daidai da karatun digiri a Najeriya, to amma ba zai iya amfani da ita domin neman aiki ba, wanda hakan ya sanya ya ɓuge da aiki a kantin wani balarabe.

"Yawanci a birnin Tripoli, ayyukan da baƙaƙe ƴan Afirka ke yi su ne aikin tsintar leda, ko aikin gidan bulo, ko aikin gadi da kuma aikin gadin dabbobi, ko kuma tonon rijiya," in ji Mukhtar.