PDP za ta ɗauki mataki kan rufe babban ofishinta

Asalin hoton, PDP
Babbar jam'iyyar hammaya ta PDP a Najeriya ta ce tana nazari kan matakin da ya kamata ta ɗauka game da rufe hedikwatarta da hukumar kula da birnin Abuja ta yi.
Hukumar kula da birnin Abuja dai ta rufe gine-gine sama da dubu huɗu waɗanda ta ce sun karya dokar biyan harajin ƙasa.
PDP ta ce za ta bi diddigi domin gane abin da ya janyo tsaiko wajen buɗe ofishin nata duk kuwa da umarnin da shugaba Tinubu ya bayar na a buɗe wuraren da aka rufe saboda rashin biyan harajin ƙasa a birnin Abujan domin ba su damar biya.
Yusuf Dingyadi babban mataimaki ne ga shugaban jam'iyyar PDP kan sadarwa, kuma ya shaidawa BBC cewa idan har shugaban ƙasa ya bayar da umarnin buɗe wuraren da aka rufe to ya kamata su gani a ƙasa.
Ya ce ''Mu mun san mun bi duk ƙa'idojin da suka dace.''
''Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa ya bayar da umarni ga sashin shari'a na jam'iyyar da kuma sashi kuɗi domin su yi nazari kan abin da ya kamata a yi, kuma da sun ƙare za mu fitar da sanarwa.''
Ya kuma bayyana cewa su a wajen su, rashin buɗe ofishin nasu ƙin biyayya ne ga umarnin da shugaban ƙasa ya bai wa ministan birnin na Abuja.