Abin da ya sa na goyi bayan Obasanjo lokacin faɗansu da Atiku - El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai wanda ya bar jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta SDP, ya ce tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya fi gaskiya a lokacin rikicinsu da mataimakinsa, Atiku Abubakar.
Nasiru El-Rufa'i ya shaida wa BBC hakan ne a wata tattaunawa ta farko da ya yi da wata kafar watsa labarai tun bayan komawarsa jam'iyyar SDP a farkon makon nan.
"Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar mun yi aiki kuma na ji daɗin aiki da shi. Kuma na yi imanin cewa ya bayar da babbar gudunmowa a shugabancin Najeriya. Amma ni ban taɓa yi masa wani butulcin siyasa saboda siyasa ba ta taɓa haɗa mu ba, aiki ne ya haɗ mu. Amma a cikin aiki idan na ga ya yi wani abu ba daidai ba zan faɗa masa." In ji El-Rufai.
Dangane da alaƙarsa da Abubakar Atiku, El-Rufai ya ce mutane ne kawai suke ta surutansu amma babu wani abu maras daɗi a tsakaninsu.
"Mutane suna ta cewa na butulci Atiku. To wane butulci aka yi masa? Lokacin da ya samu matsala da shi da Cif Obasanjo, mu mun zauna dukkanninmu masu aiki a ƙarƙashinsa kuma muka gano cewa Obasanjo ya fi gaskiya. Ba maganar Arewa ko Kudu ake yi ba. Kuma wannan ba siyasa ba ce magana ce ta wurin aiki. Kuma mun faɗ masa kuma ya san dalili. Kuma yau ni da Atiku muna tare, idan da a ce haka (butulci) ne halina me ya sa yanzu muke tare? Ya san gaskiya." In ji Malam Nasiru El-Rufa'i.
Ko Atiku zai koma SDP?
Da BBC ta tambayi Malam Nasiru El-Rufa'i kan cewa ko Atiku Abubakar zai koma jam'iyyar SDP da El-Rufai ya koma? Sai Malam Nasiru El-Rufa'in ya ce:
"Wannan kuma Atiku za ka tambaya. To amma kuma fatana da addu'ata su ne duk shugabannin adawa da suka haɗa da mai girma Atiku Abubakar, mai girma Peter Obi da Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola da ma dukkan shugabannin adawa gabaɗaya.
Fatana shi ne su zo mu shiga jam'iyyar SDP mu sake wata APC ɗin amma ba tare da an yi maja ko kuma an yi wa sabuwar jam'iyya rijista ba tunda ga SDP nan jam'iyya ce wadda ba ta da matsala mu je mu shiga domin mu fuskanci waɗannan mutanen." In ji Malam Nasir El-Rufa'i.
Dalilan da suka sa na goyi bayan Tinubu - El Rufai
Malam Nasir El-Rufai ya ce duk da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaudare shi amma har yanzu bai yi da-na-sanin goyon bayansa ba saboda wasu dalilai guda biyu.
"Dalili na farko shi ne manyan malamai na kudu maso yammacin Najeriya ne suka zo wurina suka faɗa min cewa ana cutar Musulmi a yankin saboda yadda ake ɗaukar Kirista daga yankin nasu a duk lokacin da aka samu shugaba daga arewa. Hakan ne ya sa na mara musu baya. Yanzu kenan Musulmi za su iya yin mulki daga yankin kudu maso yammaci.
Dalili na biyu kuma shi ne na goyi bayan Tinubu saboda yarjejeniyar da aka yi cewa mulki zai koma kudancin Najeriya. Mu kuma ƴan arewa ba mu saba karya alƙawari ba. Waɗannan dalilan ne ya sa ba na yin da-na-sanin goyon bayan Tinubu." In ji Malam Nasiru El-Rufai.
Ko El-Rufai zai yi takara a 2027?
Da wakilin BBC ya tambayi Nasiru El-Rufai cewa ko zai yi takara?
Sai ya ce "ban sani ba. Ai ba ni ne zan ce zan yi takara ba. Jam'iyya ce da mutane za su kira ka su ce ka tsaya takarar wannan muƙami ko wancan."
Ko takarar da na tsaya ta gwamnan ai mutane suka je suka samu Buhari su ka cusa masa ra'ayi, shi kuma ya kira ni ya ce ka je ka yi takara kuma ni ban ma so na yi takarar ba domin ban iya ba saboda tsoronta nake yi." In ji El-Rufai.
Abin da nake nufi da babu dattijo a Arewa - El-Rufai
A shekarar 2022 ne dai Nasiru El-Rufai ya shaida wa BBC cewa "babu wani dattijo a arewacin ƙasar" a lokacin da yake mayar da martani game da wasu mutane da ya yi zargin suna kutingwilar ganin Bola Tinubu bai ci zaɓen 2023 ba.
Da kuma BBC ta tambaye shi ko yana da-na-sanin yin waɗannan kalamai kasancewar yanzu haka ya amince cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi masa bazata, ya ce:
"A'a ba cewa na yi babu wani dattijo a arewa ba. Ni na san mutanen da ke magana a kai. Ba dattijai ba ne ƴan siyasa ne. Kuma kuɗi suke karɓa daga wurin wannan ɗan takara ko wannan jam'iyya. Ba Allah ne a gabansu ba ba kuma arewa ba.
Idan dattijai ne na gaskiya ai ya kamata bayan wa'adin mulkin Buhari su fito su ce ya kamata mulki ya koma kudanci. Haka dattijon Arewa zai yi tunani." In ji El-Rudai.