Da wuya a samu cigaba a tattaunawar Rasha da Ukraine - Amurka

Marco Rubio

Asalin hoton, Reuters

Amurka ta ce ba ta da yakinin samun wani babban cigaba a tattaunawar zaman lafiya ta tsakanin Ukraine da Rasha da aka tsara yi a Turkiyya, bayan da bangarorin biyu suka kasa ganawa kamar yadda aka tsara a ranar Alhamis.

Ana sa ran sake yunkurin hada tawagogin kasashen biyu ranar Juma'a domin tattaunawar.

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio wanda ya bayyana matsayar ta Amurka a kan wannan ganawa ta tawagar abokan gabar biyu – Ukraine da Rasha, ganawar da ke zaman ta farko ta gaba da gaba tun 2022, a kan yakin da suke yi, ya ce ba sa sa ran za a samu wani cigaba ba har sai Shugaba Trump ya gana keke da keke da takwaransa na Rasha Vladimir Putin domin sanin niyyar shugaban na Rasha.

Shi dai Shugaba Zelensky na Ukraine ya ce a shirye yake ya zauna tare da Mista Putin su tattauna, to amma ya ce bai yarda cewa Moscow ta dauki wannan magana da tattaunawa da muhimmanci ba.

Tun da farko an sa ran shugaban na Rasha zai je ganawar ta Turkiyya amma sai ya tura wata tawaga bisa jagorancin wani hadiminsa, abin da shugaban Ukraine yake ganin Rashar ba ta dauki batun da kima ba.

Shugaba Zelensky ya bayar da tabbacin zai aika da babbar tawaga domin tattaunawar a birnin Santambul, amma ya zargi Rasha da raina musu ajawali.

Da yake magana da manema labarai a babban birnin Turkiyyar, Ankara, ya yi suka kan karamar tawagar da Moscow ta tura, to amma shugaban tawagar Vladimir Medinsky, ya ce, tawagar ta fadar gwamnatin Rasha, tana da duk wata kwarewa da ake bukata.

Tun da farko Shugaba Trump na Amurka – wanda ke ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya shi ma na nuna alamun cewa da wuya a samu wata nasara ta a-zo-a-gani a tattaunawar, har sai shi da Shugaba Putin sun gana gaba da gaba.

Lokacin da BBC ta tambayi shugaban na Amurka, a cikin jirginsa na Air Force One, ko ya ji takaici kan irin tawagar da Rasha ta aika wajen tattaunawar, sai y ace, ''ai ya san baa bin da zai Wakana har sai shi da Putin sun yi gaba da gaba.

Shugaban na Amurka, ya ce zai halarci tattaunawar ta Turkiyya a yau Juma'a, idan har hakan ya dace, to amma kuma daga baya y ace, watakila ya koma gida - Washington

A ranar Alhamis ne aka shirya tawagar Turkiyya da ta Amurka da Ukraine da kuma ta Rasha za su gana a Santambul , to amma har zuwa jiya da daddare, ba a kai ga tsara lokacin da za su yi ganawar ba.

Shugaba Putin ne ya gabatar da shawarar yin tattaunawar ta gaba da gaba inda ya sa ranar 15 ga watan Mayun wato, Alhamis sakamakon kiraye-kiraye na shugabannin Turai da kuma kiran Ukraine na tsagaita bude wuta tsawon kwana talatin ba tare da wani sharadi ba.

To amma sai a ranar ta Alhamis fadar gwamnatin Rasha – Kremlin ta ce shugaban kasar bay a daga cikin tawagarta da za ta halarci zaman tattaunawar.

Bayan ganawar Zelensky da Shugaba Erdogan a Ankara, shugaban na Ukraine ya zargi gwamnatin Rasha da rashin mutunta Trump da Erdogan saboda rashin babban wakilici a tawagar ta Rasha.

Ya kuma jaddada kalubalantar da ya yi wa Shugaba Putin kan su yi ganawar gaba da gaba.

Yayin da ake duka wannan jagoran tawagar ta Rasha Medinsky ya gaya wa manema labarai a Istanbul cewa, Rasha ta dauki tattaunawar a matsayin ci gaban yarjejeniyar da ta wargaje a 2022, da aka yi jim kadan bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar Ukraine din a 2022.