Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Dauda da Muftwang da Sanwo-Olu

....

Asalin hoton, facebook/X

  • Marubuci, Mukhtari Adamu Bawa
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Broadcast Journalist

Kotun ƙoli ta tabbatar da Caleb Mutfwang a matsayin halastaccen gwamnan jihar Filato.

Mutfwang na Jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 525,299 inda ya doke abokin takararsa na jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda da ya samu ƙuri'u 481,370 a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a Jos, babban birnin jihar ya tabbatar da zaɓen gwamna Mutfwang.

Sai dai kotun ɗaukaka ƙara a Abuja a nata hukuncin ranar 19 ga watan Nuwamban bara ta soke nasarar Mr Mutfwang lamarin da ya sa gwamnan ya garzaya kotu domin ɗaukaka ƙara da nufin ƙalubalantar hukuncin ƙaramar kotun.

Nasarar Lawal Dare a Zamfara sahihiya ce - Kotun ƙoli

Dauda Lawal Dare

Asalin hoton, facebook/Dauda Lawal

Bayanan hoto, Dauda Lawal Dare

Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Lawal Dare na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Zamfara.

Kotun ƙolin ta yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba inda ta ba da umarnin a sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi uku.

Hukumar zaɓe dai ta ayyana Dauda Lawal a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'a 377, 726, inda a wani lamari mai cike da ban mamaki, ya kayar da gwamna mai ci Bello Matawalle.

Sai dai ɗan takarar na APC, Bello Matawalle wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaron Najeriya, ya zargi Inec da kassara nasarar da ya samu, saboda ta gaza haɗawa da sakamakon wasu mazaɓu.

Hujjojin da kotu ta dogara da su

Mai shari'a Emmanuel Agim wanda ya karanta hukuncin ya ce wanda ya ɗaukaka ƙara, Bello Matawalle ya yi zargin cewa Gwamna Dauda Lawal na PDP bai ci rinjayen ƙuri'u a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Ya tambaya, ko wacce shaida aka gabatar da ke tabbatar da hujjar zargin da masu ƙara suka yi? Ya tambaya.

A ƙaramar hukumar Maradun, Bello Matawalle ya yi iƙirarin cewa Gwamna Lawal ya yi maguɗi. Sai dai a cewar Mai shari'a Agim: "Abin da ake buƙata shi ne a gabatar da madadin kwafin sakamakon, wanda mai ɗaukaka ƙara ya gaza yi".

Sannan an gaza tabbatar da zargin aringizon ƙuri'i saboda hukumar Inec ba ta samar da rijistar masu zaɓe ba, ba ta kawo rahoton baturen zaɓe mai kula da rumfar zaɓe ba, ko kuma shaidar mutanen da suka kasance a rumfar zaɓe, in ji alƙalin.

Haka zalika, na'urorin tantance masu zaɓe na Bvas a karan kansu, ba za su iya tabbatar da an yi maguɗin zaɓe ba.

“Mai ɗaukaka ƙara bai iya gabatar da gamsasshiyar shaida ba.

“Wannan kotu na ganin cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi daidai. Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ya tauye adalci, saboda wanda ya ɗaukaka ƙara ya gaza sosai wajen tabbatar da hujjar zarge-zargensa,” alƙalin ya ayyana.

Mai shari'a Agim ya ce hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ba a gina shi a kan ginshiƙin shaidar da aka gabatar ba.

“Hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a watan Nuwamba, an jingine shi. umarnin da ke jingine zaɓen wanda ya ɗaukaka ƙara, shi ma an jingine shi. Sannan an tabbatar da zaɓen wanda ya ɗaukaka ƙara.” in ji Emmanuel Agim.

Bala Mohammed ne gwamnan Bauchi - Kotun ƙoli

...

Asalin hoton, X/Bala Mohammed

Kotun ƙolin Najeriya da ke zaman ta a Abuja ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad na PDP ya samu a zaɓen gwamna na shekarar 2023.

A hukuncin da ta zartar a yau Juma'a, kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Siddique Abubakar wanda ya ƙalubalanci hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da na sauraron ƙorafin zaɓen jihar, waɗanda suka tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed.

Wannan dai shi ne mataki na ƙarshe a shari'ar da ake yi ta tantance ingancin nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen na watan Maris.

Bala Mohammed ya lashe zaɓen ne a ƙoƙarin sa na neman karo na biyu na mulkin da ya fara a a watan Mayun 2019.

Tun da farko, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Bauchi da kotun ɗaukaka ƙara duk sun kori ƙararsa, suna cewa ba ta da tushe.

Saddique Abubakar dai yana tunƙahon cewa takardun zaɓe masu yawa da aka yi amfani da su, ba a cike su yadda ya kamata ba. Sannan ya yi zargin cewa ba a yi biyayya ga kundin dokokin zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamna a Bauchi ba.

Sai dai, kotun ɗaukaka ƙara ta ce ɗan takarar na APC ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu da za su tallafi zarge-zargensa.

Duk da haka, bai yi ƙasa a gwiwa ba, a Juma'ar nan Saddique Abubakar yana fatan kotun ƙoli za ta yi hujjojin da ya gabatar duban basira, kuma ta ba shi gaskiya, yayin da abokin takararsa na PDP ke fatan alƙalan kotun kamar takwarorinsu na kotunan baya, su kori wannan ƙara.

Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnan Sanwo-Olu na Legas

Kotun Ƙoli ta tabbatar da Babajide Sanwo-Olu a matsayin halastaccen gwamnan jihar Legas.

Alƙali Garba Lawal ne ya gabatar da hukuncin inda ya kori ƙarar da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam'iyyar Labour ya ɗaukaka saboda rashin cancanta.

Sakamakon zaɓen gwamnan jihar ya nuna cewa Sanwo-Olu ya yi nasara ne a zaɓen da ƙuri'u 762,134.

Jam'iyyar LP ce ta zo ta biyu inda ɗan takararta Gbadébo Rhode-Vivour ya samu ƙuri'u 312,329, sai kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP Abdulazeez Olajide Adeniran da ya zo na uku da ƙuri'u 62,449.

Kotu ta mayar da Mutfwang kan kujerarsa ta Filato

Kotun Ƙoli ta mayar da Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, kan kujerarsa, bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara a baya ta soke nasarar zaɓensa.

Hukuncin Kotun ƙolin, wanda ɗaukacin alƙalai biyar suka amince da shi, ya rushe hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, da ya kori Muftwang na PDP.

Sun ce Muftwang ne halastaccen ɗan takarar da ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

Ta ce babu tantama cewa Gwamna Muftwanga ya tsaya takara ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar siyasa, kuma ingancin hanyar da aka tsayar da shi takara, ba batu ba ne, da za a iya ƙalubalanta a kotun sauraron ƙorafin zaɓe.

Hukuncin wanda Mai shari'a Emmanuel Agim ya karanta, ya ce kotun ɗaukaka ƙara ba ta da hurumi na tabbatar da sahihanci ko akasin haka ga zaɓen fitar da gwanin da ya samar da Muftwang a matsayin ɗan takara.

Kotun ta cimma matsayar cewa batun zaɓen fid da gwanin Muftwang ya zama ruwa-ta-sha saboda kwana 21 da doka ta ba da dama don a ƙalubalance shi a gaban babbar kotu, ya wuce.

Gwamna Mutfwang dai ya garzaya gaban kotun ne bayan kotun ɗaukaka ƙara a watan Nuwamba ta rusa zaɓensa, inda ta umarci Inec ta bai wa abokin shari'arsa, Nentewe Goshwe shaidar cin zaɓen watan Maris.