Amfanin ganyen taba sigari ga lafiyar ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images
Akan ce ganyen taba sigari na kashe mutum miliyan takwas a duniya duk shekara, amma ya za ku ji idan aka ce za a iya amfani da shi a matsayin magani?
A baya an taɓa yin amfani da ganyen a matsayin magani. Amma yanzu saboda cigaban da aka samu a fannin fasaha, ganyen sigari zai iya zama kayan haɗa magunguna a duniya nan gaba.
Turawan mulkin mallaka ne suka fara kai ganyen na tobacco nahiyar Amurka a ƙarni na 16. A lokacin, mutane kan yi amfani da shi a fannoni da dama, ciki har da maganin ciwon kai, da mura, da ciwon ciki, da ma rauni.
A Turai kuma, akan yi amfani da shi a matsayin magani a lokacin a kan cutuka da yawa.
Ɗaya daga cikin amfanin da aka dinga yi da shi da ba a saba gani ba a ƙarni na 18 shi ne bai wa mutumin da ya kusa nitsewa a ruwa.
A birnin Landan, akan ajiye curin ganyen tobacco a gaɓar koguna. Idan mutum ya faɗa ciki sai a ba shi a tobacco. Hayaƙin ganyen na sanya mutum ya ji ƙwari a jikinsa.
Sai dai kuma babu wata cikakkiyar hujjar da ke nuna cewa tobacco magani ne.
Sauya tsarin halitta

Asalin hoton, Getty Images
Akasarin magungunan zamani, akan yi su ne daga tsirrai, kamar Taxol da ake maganin ciwon daji ko kuma kansa da shi.
Ana iya sauya halittar tsirrai domin a haɗa magani da su.
A 2012, wani kamfanin magunguna na Canada Medicago ya nuna ƙwarewa, inda ya yi amfani da ganyen tobacco wajen samar da rigakafin mura miliyan 10 a wata ɗaya.
Amma ganin cewa za mu iya samar da rigakafi miliyan 40 a yanzu cikin wata ɗaya, lamarin ba ƙaramin sauyi ba ne.
Saboda alfanunta, za a iya amfani da tobacco wajen haɗa magunguna.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai gwaje-gwaje da ake yi da dama game da ko akwai hanyoyin da za a iya amfani da ganyen wajen haɗa maganin cutar ƙanjamau ta HIV-AIDS, ko ma Ebola.
Waɗannan cutukan sun fi addabar ƙasashe matalauta, inda kuma a nan ne ake yawan noman tobacco.
Akan yi amfani a tobaccon wajen haɗa maganin jinyar cutar kansa. Maganin kan taimaka wa ƙwayoyin halittar garkuwar jiki wajen yaƙar cutar.
An yi ƙiyasin masu shan sigari za su kai kashi 15 cikin 100 na al'ummar duniya, kuma akasarinsu na zaune ne a ƙasashe masu tasowa.
Maza na shan sigari ninki biyar na abin da mata ke sha, kuma an yi ƙiyasin cewa mutum miliyan takwas na mutuwa duk shekara, inda aka alaƙanta shan sigari da kisan 600 daga cikinsu.