Ko da gaske ne ana yi wa fararen fata kisan ƙare dangi a Afrika ta Kudu?

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ƴan Afrika ta Kudu fararen fata da Amurka ta baiwa mafaka ya yinda suka halarci taro a filin jirgin sama na Dulles.
  • Marubuci, Farouk Chothia
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Kowa ya ga yadda shugaban Amurka Donald Trump ya titsiye takwaran aikinsa na Afirka ta Kudu a fadar White House ranar Laraba bisa zarge-zargen cewa ana yi wa fararen fata ƴan Afirka ta Kudu kisan kiyashi.

Har ta kai ga cewa an kunna wa shugaban na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa bidiyon irin waɗannan zarge-zarge, duk da cewa wasu daga cikin su ba gaskiya ba ne.

Shugaban na Amurka, Donald Trump a yanzu ya bai wa ƴan Afrika ta Kudu fararen fata, wato wadanda ke kiran kansu Afrikaner matsayin ƴan gudun hijira.

Kusan dubu sittin ne suka isa ƙasar ta Amurka bayan an ba su mafaka.

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta bai wa ofishin jakadancin Amurka damar duba buƙatarsu a cikin ƙasar, ta kuma bai wa ƙungiyar damar ɗaukar hayar jirgi daga filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Johannesburg- ba kasafai ake ba mai neman mafaka irin wannan dama ba a lokacin da ya ke yunƙurin tserewa hukunci.

Su waye Afrikaners?

Wata cibiyar tarihin Afrika ta Kudu a Internet ta ce ''ƴan ƙungiyar Afrikaner na wannan zamani sun samo asali ne daga tsatson Turawan Yammacin Turai waɗanda suka yada zango a Kudancin Afrika a tsakiyar ƙarni na 17".

Daga cikin su kashi (34.8%) ƴan Netherlands ne sai Jamusawa kashi (33.7%) da kuma Faransawa kashi (13.2%) su ne suka yada zango kuma suka ƙirƙiri ƙungiya mai suna "unique cultural group" wadda ke bayyana kanta a matsayin ƴar Afrikal", in ji cibiyar tarihin AFrika ta Kudu a internet watau South African History Online noted.

Harshen da suke amfani da shi mai suna Afrikaans, ya ba kama da harshen Dutch.

To amma duk da suna bayyana kan su a matsayin ƴan Afrika, Afrikaners kamar sauran fararen fata na tilastawa baƙar fata ficewa daga yankunan su.

Ana kiran Afrikaners da sunan Boers, ainda ke nufin manoma kuma yar yanzu ana danganta ƙungiyar noma.

A shekara ta 1948 gwamnatin da Afrikaner ke jagoranta a Afrika ta Kudu ta kaddamar da mulkin wariyar launin fata wanda ya haifar da tsananin wariyar launin fata.

Wannan ya hada da hana aure idan akwai banbancin launin fata, keɓe wasu ayyuka don fararen fata da kuma tilastawa baƙaƙe zama a ƙauyuka.

An kuma hana su karatu, a shekara ta 1950 ne jagoran Afrikaner Hendrik Verwoerd ya ce "Kar a bari baƙaƙe su samu damar yin karatu''. Ya kamata su san cewar matsayinsu a rayuwa shi ne saran itace da janyo ruwa daga rijiya".

A shekara ta 1994 aka kawo ƙarshen ikon kakagidan Afrikaner a Afrika ta Kudu, lokacin da aka baiwa baƙaƙe damar zaɓe karon farko a zaɓen ƙasar, wanda ya kawo Nelson Mandela da jam'iyyar African National Congress (ANC) karagar mulki.

A halin yanzu Afrikaners sune sama da kashimiliyan 2.5 daga cikin al'ummar ƙasar sama da miliyan 60 million - kusan kashi 4 ke nan.

Ko an aikata kisan ƙare dangin?

.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Afrikaner ne kashi 4 na al'ummar Afrika ta Kudu

Babu wata jam'iyya a Afrika ta Kudu, ciki har da waɗanda suke wakiltar Afrikaner da yankunan fararen hula da suka yi iƙirarin ana kisan ƙare dangi a Afrika ta Kudu.

Amma ire-iren wannan iƙirari na ci gaba da bazuwa tsakanin ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi tsawon shekaru da dama har ma Trump ya bayar da misalain kisan ƙare dangin da ya faru lokacin wa'adinsa na farko.

Iƙirarin dai ya samo asali ne daga hare-haren da aka kaiwa farar hula manoma ko kuma labarun bogi da ke yaɗuwa a internet.

A watan fabrairu wani Alƙali a Afrika ta Kudu ya yi watsi da batun kisan ƙare dangi ya yinda ya ke shari'ar gado tsakanin wani mai arziƙi da ya baiwa ƙungiyar fararen ta hula ta Boerelegioen gudummawa.

Afirka ta Kudu ba ta fidda alkalumman laifukan ƙabilanci ba, amma alkalumman baya-bayan nan sun nuna cewa an kashe mutane 6,953 a ƙasar tsakanin watannin Oktoba da Disamban shekara ta 2024.

Daga cikin waɗanda aka kashe ɗin, 12 an kashe su ne a gonaki ya yinda 5 kuma aka kashe su cikin gidajensu da ke gonakin akwaikuma wasu ma'aikata 4 da kae tunanin ɓakar fata ne.

Me Trump da Musk suka ce?

Da ya ke kare manufarsa ta bai wa Afrikaners matsayin ƴan gudun hijira, Trump ya bayyana cewar ''ana aikata kisan ƙare dangi a Afrika ta Kudu sannan ana kashe fararen hula manoma tare da karɓe musu filaye".

Trump ya ce ba ya jin zai iya halartar babban taron shugabannin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi G20 da za a gudanar a Afrika ta Kudu cikin irin wannan yanayi.

"Ba zamu je ba, har sai an kawo gyara," ya ƙara da cewa.

Shima mai ba Trump shawara Elon Musk wanda aka haifa a Afrika ta Kudu ta bayar da misali da ''ikon mallakar filaye ta hanyar banbancin launin fata'', inda ya yi zargin an hana kamfaninsa starlink mai samar da internet aiki a Afrika ta Kudun saboda shi ba baƙar fata ba ne.

Kafin kamfani ya yi aiki a Afrika ta Kudu sai ya samu lasisi sannan sai kashi 30 na kamfanin zai amfani ƙungiyoyin da aka watar a baya.

Hukumar sadarwa mai zaman kanta ta Afirka ta Kudu (Icasa) - hukuma ce mai kula da harkokin sadarwa - ta shaida wa BBC cewa Starlink bai taɓa mika takardar neman lasisi ba.

Musk ya zargi masu fafutukar yaƙi da cin hanci watau (EFF), wadda ita ce jam'iyyu ta 4 mafi girma a Afrika ta Kudu da yaɗa manufofin kisan ƙare dangi cikin waƙoƙin da ta ke rerawa a lokutan gangami.

Mene ne ya sa jam'iyyar siyasa rera waƙar harbin Boers?

.

Asalin hoton, Gallo Images via Getty Images

Bayanan hoto, Julius Malema a birnin Johannesburg da ke Afrika ta Kudu ranar 15 ga watan Disamban shekara ta 2024 .

Taken waƙar Julius Malema jagoran jam'iyyar EFF shi ne "A harbe Boer, a harbe manoma", wannan ya ke ce waƙar da ya ke rerawa ya yin tarukan gangami.

Kungiyoyin masu fafutukar Afrikaner sun yi ƙoƙarin ganin an dakatar da waƙar, wadda suka ce tana ɗauke da kalaan tayar da tarzoma.

Sai dai kotun ƙolin a Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin cewa Malema na da haƙƙin rera waƙoƙin - wanɗanda aka fara yaɗawa a lokacin gwagwarmayar yaƙi da wariyar launin fata a dandalin gangamin siyasa.

Jam'iyyar ANC ta ce ba ta sake rera ta ba, amma ba za ta iya "kayyade wa sauran jam'iyyun siyasa abin da ya kamata su rera ba".

Ko farar fata na fuskantar wariyar launin fata a Afrika ta Kudu?

Duk da cewa mulkin farar fata ya ƙare a shekara ta1994, har yanzu ana jin tasirinsa.

Akwai banbanci sosai tsakanin rayuwar farar fata da ta baƙar fata.

Fararen fata sun mamaye kashi 62.1 na manyan muƙaman gudanarwa, a cewar wani rahoto na baya-bayan nan da hukumar samar da ayyukan yi ta Afirka ta Kudu ta fitar.

Gwamnati ta yi ƙoƙarin sauya wannan tsari ta hanyar raba dai dai a ayyukan yi.

Ya yinda yawancin ƴan Afirka ta Kudu suka yi maraba da waɗannan dokoki, wasu tsirarun ƙabilun suna jin cewa suna wahala wajen samun ayyukan yi da kwangilar gwamnati. Haka kuma an sha sukar cewa za su iya haifar da cin hanci da rashawa, misali idan aka bai wa abokai da ƴan uwan ​​jami'ai damar kasuwanci.

Daga cikin masu sukar tsarin har da jam'iyyar Democratic Alliance, wadda duk da kasancewarta cikin haɗakar gwamnati, a baya-bayan nan ta ƙalubalanci dokar daidaita ma'aikata da aka yi wa kwaskwarima a gaban kotu, tana mai cewa "zai ta haifar da wariya."

An yi Allah wadai da Ministan wasanni Gayton McKenzie bayan an tallata wani aiki a sashinsa a matsayin aikin da al'ummar da suka fito daga yankin Asiya ne kawai zasu iya nema.

Ko Ƴan Ƙungiyar Afrikaner na son komawa Amurka?

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu daga cikin ƴan ƙungiyar Afrikaner na kallon shugaba Donald Trump a matsayin mai goyon bayansuy

Babu alamun hakan..

A watan Maris In March, wata ƙungiyar ƴan kasuwa ta ce kusan ƴan Afrikan 70,000 ne suka nuna sha'awarsu ta komawa Amurka bayan tayin Trump - daga kimanin mutane miliyan 2.5.

Ranar litinin ofishin jakadancin Amurka dake Afrika ta Kudu ya fitar da wata sanarwa da ke fayyace ka'idojin bayar da matsuguni a ƙasar, inda ta ce ta tsarin ya shafi mutanen da suka fito daga kowane irin ƙananan ƙabilu, ba Afrikaners ƙadai ba, waɗanda za su iya ba da misali da wani lamari na zalunci ko kuma fargabar fuskantar matsin lamba a gaba.

Ƙididdiga ta baya-bayan nan a Afirka ta Kudu wadda aka yi a shekara ta 2022, ya nuna cewa Launuka, (kalmar da ake amfani da ita a hukumance wajen bayyana launin fata) su ne mafi yawan tsiraru, waɗanda ke da kashi 8% na yawan jama'a. Masu farar fata na biye da su, ciki har da Afrikaners, kashi 7%, sai ƴan Asiya masu kashi 3%.

Bayan tayin na Trump, kungiyar masu fafutukar kare haƙƙin jama'a ta Afrikaner Solidarity ta wallafa labarin a shafinta na internet mai taken: "Dalilai goma na zama a Afirka ta Kudu a tarihi"

A majalisar dokokin ƙasar a makon da ya gabata shugaban jam'iyyar Freedom Front mai sassaucin ra'ayi ya ce zasu ci gaba da goyon bayan Afirka ta Kudu.

"Muna alfahari da Afirka kuma za mu ginawa ƴa yanmu makoma a nan," in ji Corné Mulder.