Mece ce gaskiyar asalin mutanen da aka kashe a Edo?

...

Asalin hoton, FB/Multiple

A ranar Juma'a shafukan sada zumunta musamman a arewacin Najeriya sun cika da fushi da alhini na abin da ya faru a Edo, ɗaya daga cikin jihohin kudancin ƙasar.

Hotunan da aka riƙa yadawa, waɗanda BBC ba ta tantance da kanta ba sun nuna yadda aka yi wa wasu mutane jina-jina, sannan aka riƙa jefa tayoyin mota a kansu.

Haka nan an ga yadda wasu ke dukan wani mutum da katako a cikin kwalbati, sannan a wani hoton kuma an ga wuta na ci daga nesa.

Sannan kuma an ga babbar motar kamfanin Dangote, wadda aka farfasa wa gilashi yayin da wani ɓangare nata ke ci da wuta.

Wani hoton kuma ya nuna bindigogin harba ka ruga, irin ta masu farauta ta gargajiya, da kuma adduna.

Bayanai sun nuna cewa mutanen da lamarin ya rutsa da su, wadanda suka bayyana kansu a matsayin mafarauta, ƴan sintiri ne suka tare su yayin da suke tafiya a wata babbar mota.

Binciken da ƴan sintirin suka yi ya sanya aka gano bindigogi a motar, lamarin da ya janyo mutanen gari suka far wa waɗanda ke cikin motar bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.

BBC ta tattauna da shugaban ƴan arewa mazauna Edo, Alhaji Badamasi Saleh, wanda ya ce mafarauta 27 ne a cikin motar, inda mutane ne ƴan arewacin ƙasar waɗanda suka tashi daga garin Fatakwal domin zuwa gida bukukuwan Sallah.

"Lokacin da suka zo garin sai ƴan bijilante suka tare su, sai suka ce kidinafas ne, suka kama su da duka, suka kashe su, suka ƙona wasu daga daga cikinsu."

"Mutum 11 suna nan da lafiyarsu amma mutum biyu na jinya a asibiti."

Yanzu haka dai shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da hukunta waɗanda ke da hannu.

Tsautsayi ne - Gwamnan Edo

...

Asalin hoton, FB/David Ekpebholo

Bayanan hoto, Lokacin da gwamnan jihar Edo Monday Ekpebholo ya kai ziyara ya buƙaci al'umma su kwantar da hankali

Tuni dai gwamnan jihar ta Edo, Monday Ekpebholo ya ziyarci garin na Uromi, inda ya ga inda lamarin ya faru sannan ya jajanta wa al'umma.

A tattaunawarsa da BBC, Ekpebholo ya bayyana lamarin a matsayin tsautsayi.

Ya ce: "Haruna, ni a ganina wannan tsautsayi ne kawai, saboda yadda wannan abin ya faru. Mutanen nan na tafiya ne abinsu cikin wata babbar mota sai 'yan banga suka tare su. To da suka gan su da makamai, daga nan gardama ta kaure, sai kawai dayansu ya zaro ta wuka ya so ya soki daya daga cikin 'yan bangar. A nan ne fa rayuka suka baci suka fara fada. An samu wadanda suka mutu a duka bangarorin biyu. Amma dai mun dawo da kwanciyar hankali. Na gana da al.'ummar Hausawa, da shugabannin tsaro da kuma sarakuna kuma duk mun cimma matsayar cewa irin hakan baza ta sake faruwa ba."

Gwamna Ekpebholo ya ƙara da cewa: "Lamarin ya faru ne saboda shigar da mutanen suka yi cikin jihar da makamai. Kuma ka san abin da ke faruwa a Najeriya yau nan da can, wato batun satar mutane. Ba a kudu kadai yake faruwa ba yana faruwa a arewa. Yanzu ba wanda ya yarda da wani a kasar nan. A maimakon da suka gan su da makamai su su yi bayani sai ɗaya ya yi ƙoƙarin soke ɗaya daga cikinsu abin da ya sa suka ɗauka da gaske masu garkuwa da mutanen ne. Abin dai bai yi min daɗi ba. Gaba ɗaya al'ummar Edo ba ta ji dadin hakan ba don bai taba faruwa ba."

Su wane ne aka kashe?

Bayanai sun nuna cewa abin ya faru ne a ranar Alhamis 27 ga watan Maris, a wani gari da ake kira Uromi da ke jihar Edo a kudancin Najeriya.

Shugaban ƴan arewacin Najeriya mazauna Edo, ya shaida wa BBC cewa sun gano asalin garuruwan da mutanen da aka kashe suka fito, inda akasarin su suka fito daga jihar Kano.

"Mutanen Kano ne, wasu daga Rano, wasu daga Bunkure, wasu daga Kura sai kuma mutane biyu daga Katsina," in ji Alhaji Badamasi.

Ya kuma bayyana wa BBC cewa yanzu haka gwamnan ya alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki ɗawainiyar wadanda aka raunata, sannan kuma ya ce gwamnan ya yi alƙawarin cewa za a tallafa wa iyalan waɗanda aka kashe.

An kama mutum 14 - Ƴansanda

Sanarwar da ƴansandan Najeriya suka fitar ta ce an samu mutanen ne da bindigogi ƙirar gida guda 19

Asalin hoton, FB/Nigeria Police Force

Bayanan hoto, Sanarwar da ƴansandan Najeriya suka fitar ta ce an samu mutanen ne da bindigogi ƙirar gida guda 19

A wata sanarwa da ta fitar cikin daren ranar Juma'a, rundunar ƴansandan Najeriya ta hannun mai magana da yawunta, A Olumuyiwa Adejobi ta ce ya zuwa daren na Juma'a an kama mutum 14 waɗanda ake zargi da hannu a kashe-kashen.

"Ya zauwa yanzu, an kama mutum 14 bisa zargin su da hannu a lamarin, kuma ana ci gaba da bin sawu domin gano sauran mutanen da ke da hannu," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa "Sufeta-janar na ƴansandan Najeriya ya umarci mataimakin sufeta-janar na ƴansanda mai kula da binciken manyan laifuka (FCID), DIG Sadiq Abubakar ya karɓi ragamar jagorantar binciken, sannan ya tabbatar an gaggauta yin sahihin bincike."

Sai dai sanarwar ta ce ƴan sintirin da suka tare motar sun kama matafiyan ne ɗauke da bindigogi ƙirar gida guda 19, "kasancewar ba su gamsu da hujjojin da suka ba su ba, sai suka yanke hukuncin cewa masu garkuwa da mutane ne".

Daga nan sai sanarwar ta buƙaci al'umma su guji riƙe makamai ba tare da samun izini ba, "kasancewar hakan babban laifi ne a dokar Najeriya".

Me mutane ke cewa?

A wani bayani da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin abin kaɗuwa.

Ya ce "Shugaban ƙasa ya kaɗu da wannan mummunan aiki da ya faru a ranar Alhamis. Sannan ya umarci ƴansanda da sauran hukumomin tsaro su gaggauta yin bincike tare da hukunta waɗanda ke da hannu.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Cikin waɗanda suke kiran a yi adalci har da ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya wadda ta bayyana lamarina a matsayin abin takaici.

Ƙungiyar ta ce "yana da muhimmanci duk hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike, a gano waɗanda ke da hannu, a kama su kuma su fuskanci hukunci cikin hanzari."

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ya ce: "wannan abin takaici na buƙatar a yi sahihin bincike a kai ba tare da nuna son rai ba, domin ganowa tare da hukunta masu hannu a lamarin."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso a nasa martanin cewa ya yi: "Wannan abu da ya faru a Uromi tunatarwa ce kan rashin kan-gado a duk lokacin da mutane suka ɗauki doka a hannunsu.

"Sanin kowa ne cewa ya kamata a ce mutane daga ko'ina a ƙasar nan na da ƴancin zuwa duk inda suke soba tare da fuskantar wata kyara ko tsangwama ba."

Sannan ya buƙaci hukumomi su yi bincike tare da tabbatar da cewa an hukunta duk mai hannu a lamarin.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty Internation ta buƙaci hukumomi su gudanar da bincike kan "kisan sama da matafiya 16" wadanda aka tare su a mota kafin aka lakaɗa musu duka tare da cinna musu wuta, kamar yadda sanarwar ƙungiyar, wadda ta samu sa hannun daraktanta a Najeriya, Isa Sanusi ta bayyana.