Hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi kan rikicin masarautar Kano

Masarautar Kano

Asalin hoton, Mai Katanga/Facebook

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a Abuja, babban birnin Najeriya ta yanke hukunci kan ƙararrakin da aka ɗaukaka game da rikicin masarautar Kano a gabanta.

Rikicin ya shafi nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 da kuma soke masarautun Kano biyar da dokar masarautun Kano ta 20190 ta naɗa.

Hukuncin nata ya shafi hukunce-hukunce biyu ne da aka yanke a kotuna biyu da ke birnin Kano, wato Babbar kotun tarayya da ke Kano da kuma Babbar kotun jihar ta Kano.

'Rikicin masarautu ba hurumin kotun tarayya ba ne'

A hukunci na farko, kotun ta yanke hukuncin cewa Babbar kotun gwamnatin tarayya ba ta da hurumin tsoma baki a rikicin masarauta.

Kotun ta ce Babbar kotun Kano ce kawai take da damar yanke hukunci kan duk wani ruɗani da ya shafi sarauta a jihar.

Sai dai an samu saɓani tsakanin alƙalai uku da suka yanke hukunci kan lamarin.

Mai shari'a Gabriel Kolawale, wanda shi ne ya karanto hukuncin ya umarci da a mayar da ƙarar zuwa kotun da ta dace, wato Babbar kotun Kano domin ci gaba da sauraro.

Sai dai sauran alƙalan biyu sun ƙi amincewa da batun mayar da ƙarar zuwa Babbar kotun jihar Kano, inda suka bayar da umarnin watsi da batun shari'ar baki ɗayanta.

Watsi da hukuncin kotun Kano

A hukunci na biyu kuma kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da matakin Babbar kotun Kano na haramta wa Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu na jihar bayyana kansu a matsayin sarakuna.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Mohammed Mustapha ta bayyana cewa akwai kuskure a hukuncin Babbar kotun Kano na ranar 15 ga watan Yulin 2024, kuma ya saɓa wa ƙa'idar jin ta-bakin kowane ɓangare.

Kotun ta kuma umarci alƙalin kotun ta Kano ya miƙa shari'ar ga wani alƙalin na daban domin a sake sauraron shi daga farko.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukuncin kotun ta Kano na cike da "rashin adalci da saɓa ƙa'idar bai wa kowane ɓangare dama".

Kotun ta ce Babbar kotun Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar ne ba tare sanar da Aminu Ado Bayero game da ƙarar ba, kuma ba a ba shi damar gabatar da nasa hujjojin ba.

Rikicin masarautar Kano

Rikicin masarautar Kano na baya-bayan nan ya samo asali ne daga matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka a 2023, inda gyaran da majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun jihar ta bai wa gwamnan jihar damar rushe masarautu biyar na jihar.

Wannan ne ya bai wa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf damar sauke Aminu Ado Bayero da sarakunan masarautun Bichi, Gaya, Karaye da Rano daga kan muƙamansu.