Me ya sa maza suka fi mata saurin mutuwa?

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwararru kan harkokin lafiya sun ce bincike ya tabbatar cewa maza sun fi mata mutuwa da wuri.
Tambayar da masana harkokin lafiya ke yi ita ce mene ne ke haifar da wannan matsala a jikin maza kuma mece ce mafita?
Binciken da ƙwararru kan lafiya suka yi ya nuna cewa akasarin maza na aikata wani abu da zai lahanta lafiyarsu.
Binicken ya kuma tabbatar maza da yawa na ɗari-ɗari wajen neman magani a asibiti.
Mutuwar fuji'a
Misali, maza a Birtaniya na shan sigari, da barasa, da kuma ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.
Akasarin waɗannan mazan sun faɗa wa masu binciken cewa suna fama da matsalolin da suka shafi jini.
Wani binciken kuma daban ya nuna kashi 60 cikin 100 na mazan Birtaniya na da yiwuwar mutuwa lokacin da suka kai shekara 75 saboda ciwon zuciya.
Binciken ya kuma gano cewa akwai yiwuwar irin waɗannan mazan su mutu sakamakon haɗurra daban-daban.
Farfesa Alan White, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar da ke ke kula da lafiyar maza, ya ce laamrin na buƙatar kulawar gaggawa.
Farfesa White ya yi amfani da annobar korona a matsayin misali, inda aka gano cewa ƙarin maza 19,000 ne suka mutu fiye da mata a lokacin.
Ya ce wannan matsalar ba wai tana faruwa ba ne kawai saboda salon rayuwar da maza ke bi, ya ce abin ya wuce haka.
Bambancin jikin maza da na mata
Farfesa White ya ce jikin mace ya fi ƙarfi wajen yaƙar wasu cutuka sama da na namiji.
"Maza da yawa ba su yin magana a kan lafiyarsu, kuma ba su ɗaukar mataki da wuri kan alamun wasu cutuka da suke da su," in ji shi.
Irin hakan na faruwa da maza da yawa waɗanda suka kai munzalin balaga har zuwa sama da shekara 40.
Maza da yawa sun ɗauki lokaci mai tsawo ba su kai kan su asibiti ba domin duba lafiyarsu tsawon shekaru.
Jikin mata na daban ne. Mata kan je asibiti domin gwaje-gwaje iri-iri.
"Haihuwa ma kan sa mata su je ganin likita akai-akai sama da maza," a cewar Farfesa White.
Mark Brooks, wani mai ƙwararre kan lafiyar yara da manya maza, ya ce yadda maza ke kallon kan su ma wani dalili ne da ke shafar lafiyarsu.
Brooks na ganin mutane da yawa a cikin al'umma sun fi son su haɗu da namiji, sama da mace.
Misali, shirin hukumar lafiya ta Birtaniya NHS da ke kula da lafiyar maza masu shekara 40 zuwa 74 ɗaya ne cikin hanyoyin da gwamnati ke bi wajen daƙile matsalar da ke kashe mazan da wuri.
Sai dai kuma, huɗu ne kacal cikin maza 10 ke samun damar cin gajiyar shirin.
Mista Brooks ya ce: "Mutumin da ke aiki a ɓangaren gine-gine ba zai so ya je asibiti ganin likita ba haka kawai ko kuma don a yi masa gwaji."
Bambance-bambance tsakanin ƙabilu da launin fata ma muhimmi ne wajen nau'in cutukan da za su shafi maza.
Misali, bincike ya nuna cewa maza baƙaƙen fata da ke zaune a Birtaniya sun fi samun yiwuwar kamuwa da cutar kansar bayan mafitsara, su kuma maza 'yan Indiya da Bangladesh sun fi samun yiwuwar kamuwa da ciwon suga.
Hanyar da za a bi wajen sauya wa maza tunani
Farfesa Paul Galdas, ƙwararre kan lafiyar maza a jami'ar New York University, ya ce ya kamata maza su dinga sanin halin da lafiyarsu ke ciki.
Farfesa Galdas ya ce an ƙaddamar da wani shirin tallafa wa mazan a Birtaniya domin wayar da kan su game da tunaninsu kan lafiyar tasu.
"Ya kamata maza su dinga kula da lafiyarsu, kamar ta hanyar zagaya unguwarsu, ko ziyartar abokai. Kuma za su iya shiga harkokin wasanni, da koyon yadda za su dinga lalubo hanyar magance wasu matsaloli."
Farfesan ya ce za su dinga gane matsalolinsu a irin wannan yanayin.
"Idan kana jin wata matsala a jikinka, ya kamata ka gano wata hanya da za ka magance hakan, da kuma yin magana da mutane yayin yin hakan.
"Sai kuma mutum ya dinga ƙoƙarin zuwa a duba shi. Idan ka ji wani abu da ba ka saba ji ba a jikinka, ka nemi tallafin likita," in ji Farfesa White.