'Yanbindiga sun sace mutum 117 da hallaka wasu tara a Jihar Kebbi

Asalin hoton, NPF
Wasu 'yanbindiga sun hallaka akalla mutum tara sannan kuma suka yi awon-gaba da wasu magidanta 117, a garin Danmuntari da ke yankin Danko-Wasagu a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Wasu mazauna garin da suka tsira daga harin sun tabbatar wa da BBC, da cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata, 27 ga watan Mayun, 2025, lokacin da 'yanbindigan su ka yi wa garin kofar-rago.
Daga cikin wadanda barayin dajin suka kashe har da wata mata mai jego da jaririnta, inda suka harbe su tare da sauran jama'ar da suka hallaka ta hanyar harbin kan-mai-uwa-da-wabi a lokacin da suka shiga garin, kamar yadda shedun suka yi bayani.
''Da la'asar barayin suka kewaye garin suka dinga harbe-harbe wanda hakan ya sa dole mutanen garin suka watse suka cimma na kashewa, suka kashe mutum tara,''in ji daya daga cikin mutanen garin.
Ya kara da cewa, ''Abin ban tausayi akwai mace daya da ba ta wuce sati biyu da haihuwa ba suka kashe ta da ita da jaririnta.''
Haka shi ma wani daga cikin mutanen garin wanda a yanzu yake gudun hijira a garin Baina ya tabbatar wa BBC harin da 'yan bindigar suka kai musu.
Mutumin ya ce suna zaune kawai suna shirye-shiryen ayyukan gona da sauran ayyuka, sai kawai suka ga 'yanbindigan suna ta shigo musu gari ta kowa ne bangare a kan babura.
''Sun shigo garin wasu ta gabas wasu ta yamma, wasu ta kudu wasu ta arewa, suna ta harbe-harbe, sun dauki wasu magidanta 117, sun cimma wata mata tana jego, sabuwar haihuwa, sun kashe ta da ita da jaririnta, bayan sauran wasu bayin Allah da suka kashe kimanin mutum tara dai suka kashe,'' in ji shi.
Ya kara da cewa, ''babu wani sakamako da muka samu daga hukuma. Mu muna tunaninma, mu 'yan jihar Kebbi ne ko ma wace jiha muke?
''Babu dauki babu wasu jami'an tsaro da aka taba kawo mana don su tabbatar mana da tsaro a inda muke zaune, babu wani sakamako da ya zo daga hukuma ko kuma a kan barayin nan, babu dai wani bayani.'' Ya yi korafi.
Bayanai dai sun nuna cewa tun bayan kai harin al'ummar garin na ta watsewa, inda wasu ke nufar jihar Zamfara wasu na tafiya Kebbi.
Al'ummar garin sun ce wannan shi ne karo na uku da 'yanbindigan ke kai musu hari, inda suke zuwa da yawa a kan babura suna ci musu zarafi da kuma kisa.
Duk wani kokari da BBC ta yi na ji daga bakin hukumomin tsaro na jihar ta Kebbi a lokacin hada wannan rahoto ya ci tura.
Al'amarin tsaro dai a yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya da ma wasu sassan kasar na ci gaba da ta'azzara, duk da yadda hukumomin kasar ke cewa suna kokarin sahwo kan matsalar.