Shugaban Falasɗinawa Abbas ya nemi Hamas ta zubar da makamanta

Mahmoud Abbas ya faɗa wa wani taro da aka yi a Ramallah cewa Hamas ta bai wa Isra'ila "damar" ci gaba da yaƙi a Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mahmoud Abbas ya faɗa wa wani taro da aka yi a Ramallah cewa Hamas ce ke bai wa Isra'ila "damar" ci gaba da yaƙi a Gaza

Shugaban hukumar Falasɗinawa ta Palestinian Authority (PA) ya kira mambobin ƙungiyar Hamas da '"ya'yan karnuka" yayin wani jawabi cikin kakkausar murya, inda ya nemi ta zubar da makamanta.

Kazalika, ya kuma nemi ƙungiyar mai iko da Zirin Gaza da ta miƙa mulkin zirin domin kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Isra'ila.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin wani taro da aka a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, yana mai cewa Hamas ta bai wa Isra'ila "damar" ci gaba da kai hare-hare kuma ya nemi ta saki duka Isra'ilawan da take garkuwa da su.

Kalaman nasa su ne mafiya tsauri kan Hamas tun bayan fara yaƙin a watan Oktoban 2023.

Wani jami'in Hamas ya yi tir da kalaman na Abbas da ya bayyana da "kalaman ƙasƙanci" kan "babban ɓangare na al'ummarsa".

A makon da ya gabata ƙungiyar ta yi watsi da wani ƙudirin tsagaita wuta da Isra'ila ta gabatar a Gaza, wanda ya nemi ta zubar da makamanta domin dakatar da yaƙin na mako shida da kuma sakin mutanen da ke hannunta 10 cikin 59.

Gwamnatin PA wadda Abbas da jam'iyyarsa ta Fatah ke jagoranta na iko ne da yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tun bayan da Hamas ta kama iko da Gaza a 2007 bayan lashe zaɓen majalisa.

PA ta sha nanata cewa a shirye take ta karɓi iko da Gaza bayan gama yaƙin, amma tana shan suka daga Falasɗinawa saboda zargin ƙin yin magana.

"Hamas ta bai wa 'yan mulkin mallaka [Isra'ila] damar aikata laifuka a Gaza, babba daga ciki shi ita ce garkuwa da mutane," a cewarsa.

"'Ya'yan karnuka, kawai ku saki duk wanda kuke riƙe da shi a wuce wurin. Ku kawo ƙarshen damar da kuke ba su ku shafa mana lafiya."

Wani babban jami'i a majalisar siyasar Hamas, Bassem Naim, ya soki kalaman na Abbas da cewa "ya siffanta babban ɓangare na al'ummarsa da munanan kalamai," a cewar rahoton AFP.

Hamas da PA sun daɗe suna adawa da juna, abin da ya sa Falasɗinawa ba su taɓa magana da murya ɗaya ba.

Falasɗinawa da yawa na kallon Abbas mai shekara 89 a matsayin maras farin jini.

Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ne domin fatattakar Hamas a matsayin martani kan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da ta kai cikin Isra'ilar, wanda ya jawo kashe mutum 1,200.

Tun daga lokacin, Isra'ila ta kashe sama da mutum 51,000 a Gaza, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza ƙarƙashin mulkin Hamas.