Yadda sakamakon JAMB ke dakushe burin matasan Najeriya

...

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Aisha Babangida
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
  • Aiko rahoto daga BBC News, Abuja

Lokacin da Maryam Suleiman 'yar shekara 18 ta zauna jarabawar JAMB a shekarar 2015, burinta shi ne ta zama likita.

Wannan buri nata tun tana ƴar ƙarama take da shi, wanda ta samo daga girmamawa da take yi wa yayarta da ke aiki a wani asibiti a ƙauye kusa da Minna, Jihar Neja.

Amma sakamakon maki 189 da ta samu a jarabawar bai kai makin shiga karatun likitanci.

"Na dade ina mafarkin zama likita. Duk dangina sun san haka," in ji Mariam a lokacin da take tattaunawa da BBC.

"Da na ga sakamakon makin da na samu, a lokacin na san ba lalle burina ya cika ba."

A ƙarshe, Maryam ta ce ta sauya kwas ɗin da take so daga fannin Likitanci zuwa fannin Biochemistry a wata jami'ar jiha saboda ƙarancin makin da ta samu.

"Kawai na amince na karanta wannan kwas ɗin ne ba da son raina ba, na ga yawancin waɗanda muka gama karatun sakandire da su duk sun shiga jami'a, kuma ba na son na ɓata lokaci." in ji Maryam.

A yanzu dai tana da shekara 28 kuma ta kammala karatun Biochemistry amma kuma tana sana'ar kayan kula da fata a Kaduna. Ta ce takardar shaidar digirinta na ajiye a cikin akwati a gidan mahaifiyarta.

A Najeriya, jarrabawar JAMB ta kasance matakin farko da ɗalibai ke bi domin samun gurbin karatu a jami'o'i da sauran manyan makarantu. Duk da haka, sau da dama daliban da ke da burin zama likitoci, lauyoyi, injiniyoyi da sauransu, kan gamu da cikas sakamakon rashin samun maki da ya dace da fannin da suka nema.

Wannan na tilasta musu sauya fanni ko ma barin burin gaba ɗaya.

"Bayan na gama bautar ƙasa, ban samu aiki ba, kuma aiki ta fannin abin da na karata wato Biochemistry yana wahala a Najeriya,"

"Sai na fara haɗa man shafawa da sabulu da kayan gyara jiki. Ina ganin mutane sun fara so kuma suna siya, kawai sai na ci gaba, ban taɓa shirya zama mai kula da fata ba. Mafarkina shi ne saka farin rigar likitoci, ina taimaka wa marasa lafiya ina ba su kulawa" Maryam ta ƙara da cewa.

Kowace shekara, dubban matasa a Najeriya suna fuskantar irin wannan ƙalubale.

Samun ƙarancin maki na jarabawar JAMB na saka mutane da dama su rungumi fannonin da ba su da buri a kansu wanda hakan ke sauya musu rayuwa da aiki, ba bisa muradinsu ba.

'Na so na karanci fannin shari'a amma.....'

Labarin Ibrahim Musa daga Kano ma haka yake inda yake da burin zama lauya amma daga ƙarshe ya karanci fannin ilimin addinin Musulunci.

Ibrahim ya rubuta jarabawar Jamb a shekarar 2018 inda ya samu maki 174, makin da bai kai a ba shi kwas ɗin lauya ba.

"Na yi kuka da na ga sakamakon makin Jamb ɗina. Na san babu yadda zan yi na ƙaranci kwas ɗin Lauya " in ji shi.

A maimakon haka ya ce aka ba shi shawara ya sauya kwas zuwa na addinin Musulunci sai idan shekara ta zagayo, sai ya sayi wani sabon fom na Jamb ya sake neman lauya.

"Tabbas na sami kwas ɗin nazarin addinin Musulunci kuma na fara karatun kwas ɗin, da shekara ta zagaye, sai na sake siyan Jamb na saka kwas ɗin Lauya amma duk da haka maki na bai kai ba." in ji Ibrahim.

"Sai kawai na ci gaba da karatun nazarin addinin Musulunci, sau uku ina sake rubuta jarabawar jamb, ina saka kwas ɗin da nake so, amma makina ba ya kaiwa, hakan nan na haƙura na gama karatun "Islamic studies" ɗin da suka ba ni."

Ya kammala karatunsa a shekarar 2022 kuma yanzu yana koyarwa a wata makarantar Islamiyya. Kodayake yana godiya da samun aiki, har yanzu burinsa da mafarkinsa shi ne ya zama lauya.

Blessing Chidera daga Abuja tana so ta zama masaniya halayyar ɗan adam 'psychologist'. Bayan ta samu maki 182 a JAMB a shekarar 2020, sai aka ba ta kwas ɗin nazarin yadda ake bayar da shawarwari da jagoranci wato "Guidance and Counselling."

"Ni kuma gaskiya da na koma ya saka rubuta wata Jamb ɗin gwara na haƙura da wannan, saboda sake rubuta jamb ɗin babu tabbas."

"Duk da mutane sun ce kusan kwas ɗaya ne, amma ba abin da nake son na karanta ba kenan" in ji ta Blessing.

Blessing ta kammala karatu a 2024 kuma yanzu tana aiki a wani shagon sayar da kaya a Owerri.

"Tunda dai na gama NYSC ban sami aiki ba, na gwada nema a wurare, ban samu ba, yanzu ina aiki ne a wani shagon sayar da kayan sawa, yanayin aikina yana sa ni yawan magana da kwastomomi, wataƙila nan gaba zan samu babban aiki" in ji ta.

...

Asalin hoton, Getty Images

Me masana ilimi ke cewa?

Masanin ilimi, Dr Abubakar Yakubu ya shaida wa BBC cewa Jamb na da tasiri matuƙa a wurin sauya ɗabi'ar yaro da burin abun da yake son ya karanta ko ya zama idan ya girma matuƙar bai sami makin jamb ɗin da kwasa-kwasan fannin abin da yake so ya karanta ba da jami'o'i suka fitar.

Masanin ya kuma ce idan har ba a bai wa yaro kwas din abin da yake burin ya karanta ba, hakan na iya sukurkutar da karatun shi da kuma rayuwar shi gaba ɗaya.

"Akwai yara da ni na gani, sun gama karatun sakandire suna neman shiga jami'a, sun yi jamb sun saka kwasa -kwasan da suke so, amma ba su ci ba, yanzu haka sun zama waɗanda ba su gama karatu ba - sun ƙi su ci gaba da karatun." in ji Dr Abubakar.

Ya ƙara da cewa sau daya za a ga an bai wa yaro wani kwas daban da abun da yake da burin karantawa saboda samun ƙarancin maki a Jamb wanda hakan zai iya saka yaro ya yanke ƙauna ko kuma ma ya kasa yin ƙoƙori ta hanyar rashin fahimtar abin da ake koya masa a kwas din da aka ba shi saboda ainihi ba abin da yake son ya karanta ba ne.

"Sau dayawa wasu yara suna da burin su yi karatu har zuwa babban mataki amma kuma samun ƙarancin maki a jamb na iya sauya karatunsu gaba ɗaya inda za a ga da sun gama makarantar sakadire, sai su koma suna wasu ayyuka" Dr Abubakar ya ƙara da cewa saboda suna ji kamar rayuwarsu a ƙare ta ɓangaren karatu."

Tasirin samun ƙarancin maki a Jamb in ji Dakta ɗin ka iya sanya yaro ya ɓata lokaci sosai kafin ya gama karatu saboda wasu da su canza kwas ɗin da suke so gwanda su jira su wata shekarar su sake rubuta jamb ɗin.

"Wasu yaran sun gwammace suyi ta rubuta jamb ɗin duk shekara har sai sun sami kwas ɗin da suke da burin yi wanda hakan ke da naƙasu sosai saboda lokaci ne ke tafiya.

Me ya kamata Jamb da gwamnati su yi?

.

Asalin hoton, Jamb

Daktan ya ce Jamb tana da naƙasu sosai saboda manhajar karatun da yara suke rubuta jarabawar jamb da shi ba shi bane manhajar karatun da ake karantar da su tun daga matakin sakandire ba. Manhajar karatun ya sha bamban sosai in ji shi.

Saboda haka ya ce dole a dinga samun addadin yara masu tarin yawa da suke samun ƙarancin maki a jamb.

"Za a ga yaro ya ci jarabawar shi na Waec amma kuma ya kasa cin jarabawar shi na jamb ko ya sami ƙaramin maki." in ji shi

Dalilin haka ne ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ɓangaren ilimi da Jamb su zauna kuma su sake nazari kan manhajar karatu ya kasance abin da ake karantarwa a makarantun sakandire shine ake tambaya a jarabawar Jamb ba ki ɗaya.

Dr Abubakar ya kuma ce ya kamata gwamnati ta tsaya ta tabbatar da akwai kayayyakin aiki musamman kwamfutoci.

"Idan muka duba za mu ga cewa rashin waɗannan kwamfutoci da yara ke amfani da su, ba a yawan koyar da su a makarantu saboda babu, kuma yanzu jamb sai da ilimin kwamfuta saboda da ita ake rubuta jarabawar. Daktan ya ƙara da cewa.

Ya ƙara da cewa akwai wasu malamai ma da basu da ilimin yin amfani da kwamfuta balantana a ce su ma ɗalibai su iya amfani da ita har ayi tunanin su ci jarabawa.

"Ya kamata gwamnati ta bai wa malamai horo ta ɓangaren amfani da kwafutoci saoda ɗalibai su ma su ƙaru."

Dr Abubakar ya kuma ce ga iyayen da ke kai hanzarta shigar da yaransu jami'o'i a halin kuma yaran ba su kai matakin rubuta jamb ba, ya kamata su sake nazari, saboda yara na buƙatar gama sakadire kafin ya ce za iya rubuta jamb.

Ya shawarci yara da su dage da karatu domin su ci jarabawa.