Abu shida da ya kamata Musulmi su yi a goman farko na Zhul Hajji
Matashin malami a Najeriya, Sheikh Junaid Abubakar ya lissafa wasu ayyuka da ya kamata Musulmi su yi a ranakun goman farkon watan Dhul Hajji wata na 12 a jerin watannin Musulunci.
Shehun malamin ya ce kwanakin 10 na watan sun ƙunshi ibadu kamar azumi da salloli da zikiri da karatun al'ƙur'ani da kuma layya ga masu hali.
Ya kuma ƙara da cewa babbar rana a kwanakin ita ce ranar tara ga wata wato ranar Arfa.
kuma ƙara da cewa babbar rana a kwanakin ita ce ranar tara ga wata wato ranar Arfa.
Ga wasu abubuwa biyar da shehin malamin ya lissafo da suka kamata a yi a ranakun:
- Azumin kwana tara na farkon watan
- Azumin ranar Arafah
- Sada zumunta
- Karatun Al-ƙur'ani
- Sadaka
- Layya ga wanda yake da iko
Ya ƙara da cewa dukkan akwai kyau a ƙara ƙaimi wajen aikata dukkan abubuwan da suke jawo yardar Aallah, "saboda Allah na ruɓanya lada ga waɗanda suka aikata aikin lada a kwanakin, kuma babu ranar da aikin lada ya fi, kamar waɗannan ranakun," in ji shi.