Da gaske alƙawarin ta-zarce ke haifar da guguwar sauyin sheƙa a Najeriya?

Bola Tinubu

Asalin hoton, PRESIDENCY

Guguwar sauyin sheka da 'yan siyasar Najeriya ke yi daga jam'iyyun adawa zuwa jam'iyyar da ke kan gwamnati na cigaba da jan hankali da raɗe-raɗi tsakanin masu zargin ruwa ba ta tsami banza.

Bayanai daga galibin al'umma na ƙara fitowa, inda wasu ke cewa ƴan adawa masu sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki a Najeriya suna yin haka ne a bisa alƙawurra daban-daban da aka yi masu.

Sai dai mafi yawan masu sauya sheƙar dai suna kafa hujja ne da rikicin cikin gidan jam'iyyun su, wanda suka ce ya tilasta masu ficewa domin samun mafita.

Amma bayanan da ɓangarorin da lamarin ya shafa ke yi na nuni da cewa kowa da irin hanyar da ya bi domin kaiwa ga matakin da ya ɗauka.

Wani abun da ke bada mamaki dai shi ne yada lamura suka dau zafi tun kafin a kai ga lokacin neman zaben 2027.

Menene gaskiyar zargin?

Ana dai ganin watakil sauya sheka da jam'iyyar adawa ke yi zuwa APC na da alaka da lasa musu zuma a baka.

Akwai ma majiyoyin da ke cewa wasu 'yansiyasar da ke kan mulki ana musu alkawarin tazarce, shiyasa suke ruguwa jam'iyyar APC domin samun sauki a zaben 2027.

Amma a tattauanwarsa da BBC daraktan yaɗa labaran ofishin jam'yyar APCn na ƙasa, malam Bala Ibrahim ya ce babu gaskiya a cikin wannan zargi.

Bala Ibrahim ya ce dama siyasa na gaji kun ji-kun ji, amma zance na gaskiya kamar yada yake cewa babu batun alkawari ko tazarce da ake yi wa 'yansiyasar.

Malam Bala ya ce zance na gaskiya ana yiwa 'yansiyasar mumunan zato, wanda idan aka bincika kowa na da dama da manufar da ya fi fifitawa.

"Babu wani alkawari da aka yi musu, kowa matsayarsu daya a APC. Kawai zarge-zarge 'yan adawa marasa tushe ne".

Bukatun al'umma

Sai dai yayin da jam'iyyar APCn ke musanta zargin cewa ba ta yi wa sabbin amaren nata alƙawari kafin sauya sheƙar tasu ba, Sanata Suleiman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, ɗaya daga cikin waɗanda suka cire rigar adawa, suka maye gurbin ta da ta jam'iyyar APC, ya ce ai dama siyasa tsari ne na bani gishiri in baka manda.

Sanata Kawu Sumaila, ya ce a mazabar da yake wakiltar an masa alkawarin gyaran hanya da kawo abubuwan cigaba, kuma zance na gaskiya babu wanda hakan ba zai farantawa ba.

Sannan ya ce magana ce ta biyan bukata, kowa da manufarsa a siyasa kuma kowa na duba gajiyar da zai samu.

"Idan mutum ya samu kofa babu wani laifi da korafe-korafe. Komai ka ga mu na yi mu na yi ne domin al'umma.

"Kuma akwai abubuwa da dama da na nema da aka mun, don haka me zan zauna bata lokaci. Ai ba tsarin ƙungiya ko wani gungu ba ne."

Sanata Sumaila ya kuma yi zargin cewa baya ga irin su da suka fito fili suka bayyana inda suka dosa a siyasance, akwai wasu da suka ɗauki salon Angulu da kan Zabo.

"Mu bama munafunci, gaskiya guda ce, mun fi wadanda ke boye-boye suna zagaye da cin amana".

Dan majalisar ya kuma nuna babu batun cin amanar jam'iyyar da ta bashi kujerar Sanata, yana mai jadadda cewa komai ya yi saboda al'ummarsa ya ke yi.

Duk da cewa sauya sheƙa a fagen siyasar Najeriya ba baƙon al'amari bane, da alama wannan karon abin zai ci gaba da jan hankali musamman ta la'akari da yadda siyasar ke ƙara ɗaukar zafi tun ana saura aƙalla shekara biyu wa'adin gwamnati mai ci ya ƙare.