window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Mahajjata sun bar filin Arafa sun tafi Muzɗalifa

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, amma zai fi mayar da hankali ne a kan tsayuwar Arfa a yau.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi barkanku da shan ruwa, da fatan Ahlah Ya karbi ibadu da addu'o;inmu.

    A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni na wasu abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya, ciki har da tsayuwar Arfa..

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. APC ta ce ba ta sauya matsayi kan kwamitin riƙonta ba

    A Najeriya, hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa ta ce ba ta sauya matsayi ba a kan kwamitin riko na mutum uku da ta kafa don gudanar da harkokin jam`iyyar a jihar Zamfara bayan sauya-sheka da Gwamna Matawalle ya yi daga PDP zuwa jam`iyyar, don haka ragamar jam`iyyar tana hannun kwamitin.

    Daraktan yada labaran Jam`iyyar, Malam Salisu Na`inna Danbatta ya ce kamata ya yi ƴaƴan jam'iyyar su mai da hankali ga manyan tarukan da jam'iyyar ke shirin yi kwanan nan, maimakon balle barakar da take dinkewa.

    A tattaunawarsu da Ibrahim Ibrahim Isa, Malam Salisu Na'inna Danbatta ya ce babu abin da jam'iyyar ke yi ba tare da tuntuba ba, saboda haka babu dalilin ka-ce-na-cen da ake yi:

    Bayanan sautiHirar Ibrahim Isa da Daraktan yada labaran jam'iyyar APC
  3. Rikicin yankin Tigray na ƙara faɗaɗa a Habasha

    Akwai alamun da ke nuna cewa rikicin yankin Tigray na kasar Habasha ya daɗa faɗaɗa zuwa wasu yankuna bayan rahotannin da aka samu cewa rikici ya barke a jihar Afar.

    Gwamnati dai ta zargi yan tawayen Tigray da kai wa fararen hula hari tare da toshe duk wasu hanyoyin shigar da kayan agaji.

    Jam'iyyar TPLF a Tigray dai ta musanta tana mai cewa mayakanta ba sa kai wa fararen hula hari.

    Abu ne mai wuya a iya tantance hakikanin mutanen da rikicin ya shafa.

    An dai toshe yawancin hanyoyin zuwa Tigray.

    Rahotanni dai sun ce yanzu shigar da kayan agaji zuwa jihar Afar inda dubban mutane ke fama da yunwa ya zamo abu mai wuya. T

  4. Al'ummar jihohin Najeriya shida na cikin hatsarin kamuwa da cutar korona

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana jihohi shida na kasar a matsayin wadanda mazauna cikinsu ke cikin hatsarin kamuwa da cutar Covid-19, kuma ta bukaci mutane a jihohin su ƙauracewa yin taruka da suka hada da na ibada, kuma su yi salloli a wajen masallatai, musamman a wannan lokaci da ake bukukuwan sallah babba.

    Najeriya, wadda ita ce kasa mafi yawan jama'a a Afirka, na fuskantar sake bazuwar annobar korona zagaye na uku, bayan da aka gano nau'in nan na Delta mai saurin yaduwa a cikin kasar.

    Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron rahoton da Sani Aliyu ya hada mana:

    Bayanan sautiRahoton Sani Aliyu kan yaduwar cutar korona a jihohi shida
  5. Mahajjata sun bar filin Arafa sun tafi Muzɗalifa

    Bayan da alhazan bana suka kammala tsayuwar Arafa, tuni suka kama hanyar tafiya Muzɗalifa.

    A can ne za su sllaci Magariba da Isha'i su kuma kwana sai da asuba su tafi wajen jifan shaiɗan.

    An saba ganin cunkoso na tafiya Muzɗalifa duk shekara sai dai a bara da bana lamarin ya sauya saboda rage yawan mahajjatan da hukumomin Saudiyya suka yi.

  6. Kotu ta dakatar da Majalisar Dokokin Zamfara daga tsige mataimakin gwamna jihar

    Wata Babbar Kotu a Najeriya ta dakatar da majalisar dokokin jihar Zamfara daga daukar matakin tsige mataimakin gwamna jihar, Mahdi Aliyu daga kan mukaminsa.

    Jam’iyyar PDP ce ta shigar da ƙarar, bayan wata ƙarar da ta kai gaban kotun ƙolin Najeriya, tana neman fashin baki a kan makomar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da mafi yawan ƴan majalisar dokokin jihar da na tarayya, wadanda suka sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

    Bayanan sautiRahoton Ibrahim Isa kan matakin kotu na hana tsige Mahdi Ali Gusau
  7. Ba a bar ƴan Najeriya a baya ba wajen addu'o'in Ranar Arafa

    A yayin da alhazai 60,000 ke can Dutsen Arafa suna kwarara addu'o'i, su ma sauran al'ummar Musulman duniya ba a bar su a baya ba duk da cewa suna ƙasashensu.

    A nAjeriya ma ƴan ƙasar dama ne suke ta yin addu'o;i ga kawunansu da kuma ƙasar a gidajensu da kuma a shafukan sada zumunta.

    Wasu kuma suna tuna aikin Hajjin baya da suka taɓa halarta ne suna walafa hotuna cikin kewa.

    Ga dai wasu daga cikinsu:

  8. Yariman Saudiyya ya bai wa matasa 200 dala miliyan ɗaya a matsayin tallafin aure

    MBS

    Asalin hoton, Getty Images

    Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Muhammad Bin Salman ya bayar da izinin fitar da kuɗaɗe har riyal miliyan 3.74, kwatankwacin dala miliyan daya a raba wa matasa 200 a matsayin tallafin aure.

    Jaridar Saudi Gazette ta ce kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ne ya wallafa sanarwar a ranar Lahadi.

    Sanarwar ta ce za a raba kuɗaɗen ne ga matasa maza da mata a faɗin ƙasar.

    Ta ce wannan umarni na MBS ya zo ne a ƙoƙarinsa na taimaka wa marayun da ke cikin halin ƙaƙa-ni-ƙa-yi da kuma mutane masu fama da lalurar naƙasa, waɗanda saboda su aka buɗe tallafin na aure mai suna SNAD Al-Zawaj.

    A karon farko na gabatar da tsarin an fitar da tallafin riyal miliyan 250, inda fiye da mutum 26,000 daga sassan ƙasar daban-daban suka amfana.

    Baya ga haka kuma za a bai wa matasan horo kan yadda ya kamata su dinga kashe kuɗaɗe.

    Shirin SNAD na Muhammed Bin Salman an fara shi ne da niyyar ƙarfafa tattalin arziƙi da zamantakewar mutanen ƙasar, tare kuma da inganta rayuwarsu.

  9. Wasu hotunan alhazai suna addu'a a filin Arafa

    Wasu hotunan alhazai suna addu'a a filin Arafa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Wasu hotunan alhazai suna addu'a a filin Arafa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Wasu hotunan alhazai suna addu'a a filin Arafa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

  10. Kasashen Yammacin duniya sun yi Allah-wadai da China kan kutsen komfuta

    Microsoft

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Kasashen sun ba da misali da kutsen komfuta da China ta kai wa wasu na'urorin Microsoft a bana

    Kasashen Yammacin duniya sun yi Allah-wadai da China saboda kutsen komfuta da take kai wa inda suka ba da misalin ta'adin da aka yi wa wasu na'urorin Microsoft a bana.

    Birtaniya da Amurka sun zargi gwamnatin China kai tsaye.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antonio Blinken ya ce Amurka da ƙawayenta na ɗora wa China alhakin abubuwan da ke faruwa.

    Ya ce China tana mafani da masu aikata laifin wajen aiwatar da kutsen domin kasarsu da kuma ribar da samu ta fuskar kudi.

    Shi Blinken din da kuma masu gabatar da kara a Amurka sun tuhumi jami'an ma'aikatar uku da kuma wani wanda aka dauki kwangilarsa da ke yi wa komfuta kutse.

    Shi kuwa sakataren harkokin wajen Birtaniya Dominic Raab ya bayyana kutsen da China ke yi a matsayin rashin hankali, amma kuma wani salo da aka san da shi.

    Ƙungiyar NATO da kuma Tarrayar Turai su ma sun fitar da sanarwa.

  11. Mutumin da ake zaton ya mutu sama da shekara 40 ya koma gida Jigawa

    Al’ummar garin Mai Mazari da ke yankin karmar hukumar Gumel a jihar Jigawan Najeriya sun yi farin cikin dawowar wani mutum da ake zaton ya mutu sama da shekara 40 da suka gabata.

    Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ce dai ta gano mutumin mai suna Abdullahi Ali Mohammad, tare da nemo inda danginsa suke a jihar Jigawa bayan da ya nuna musu sha’awarsa ta koma wa gida.

    Abdullahi Ali Mohammad ya ce ya bar gida ne domin neman arziki zuwa Saudiyya, daga bisani ya zarce zuwa kasar Sudan bayan ya je hajji da kafa.

    Haka zalika ya tafi ya bar mata uku, amma bayan tafiyarsa dukkan Allah ya yi musu rasuwa.

    Daga Kano Ga Khalifa Shehu Dokaji da karin bayani:

    Bayanan sautiRahoto kan mutumin da ya koma gida bayan shekara 40
  12. Alhazai sun duƙufa yin addu'o'i a Filin Arafa

    Wani Alhaji na addu'a a kan dutsen Arfa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    A yayin da aka kammala sallolin azahar da la'asar a matsayin ƙasaru a Masallacin Namirah da ke filin Arafa, dukkan Musulman da suke Aikin Hajjin sun duƙufa wajen yin addu'o'i kafin lokacin tafiya ya yi.

    Idan an jima kafin faɗuwar rana ake son alhazai su bar filin Arafa don tafiya Muzɗalifa inda a can za su sallaci Magariba da Isha'i.

  13. Sojan sama ya tsallake rijiya da baya bayan hatsarin jirgi a Zamfara

    Sojin Sama

    Asalin hoton, Nigerian Airforce

    Wani jirgin saman rundunar sojin Najeriya ya yi hatsari a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, bayan da ƴan fashi suka buɗe masa wuta.

    Jirgin yana komawa ne bayan da ya kammala wani aiki mai cike da nasara a tsakanin iyakokin jihohin Zamfara da Kaduna.

    Wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar ranar Litinin ta ce sai dai cikin sa'a matukin jirgin Laftanal Abayomi Dairo, ya fita daga cikinsa.

    Bayan da ya tsira daga faɗuwa daga jirgin sai kuma ƴan bindigar suka buɗe masa wuta, amma ya samu sa'ar kauce musu ya kuma nemi mafaka a wani ƙauye har zuwa wayewar gari.

    "Daga nan sai ya yi amfani da wayarsa don gano hanyar da za ta fid da shi, inda ya yi sa'ar kauce wa sansanonin ƴan bindigar da dama har ya isa ga wani sashe na rundunar sojin Najeriya, inda daga nan ne ya samu tsira," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin da aka samu labarin hatsarin, sai Shugaban Rundunar Sojin Sama Air Marshal Oladayo Amao, ya bayar da umarnin cewa a yi duk ƙoƙarin da za a yi don ceton matuƙin.

    Sojin Sama

    Asalin hoton, Nigerian Airforce

    "Daga nan ne sai aka yi amfani da hanyoyin leƙen asiri na rundunar sojin saman da helikwaftocin yaƙi da kuma taimakon rundunar sojin ƙasa inda aka gano wajen da hatsarin ya faru tare da ganin lemar da matuƙin ya yi amfani da ita wajen sauƙa.

    Sai kuma suka ci gaba da neman matuƙin a kusa da inda lamarin ya faru.

    "Abin jin daɗi ne matuƙa yadda Laftanal Dairo ya tabbatar da cewa shawagin jiragen yaƙin a wannan yanki da hatsarin ya faru ya taimaka wajen tsorata ƴan bindigar da suke neman gano shi.

    "Hakan ce ta sa ya tsere musu har ya samu mafaka," a cewar sanarwar.

    Rundunar sojin sama ta ce mako biyu kenan tun sanda ta fara kai samame ta sama ba dare ba rana a maɓoyar ƴan bidniga, don bin umarnin da Shugaba Buhari ya bayar cewa a zaƙulo su duk inda suke a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara.

  14. An saurari ƙarar Jacob Zuma ta bidiyo

    Zuma

    Asalin hoton, others

    Tsohon shugaban kasar Afirka Ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana a cikin wani faifen bidiyo inda daga cikin gidan yari zai wuce zuwa halartar shari’ar cin hanci da rashawa.

    Mista Zuma na fuskantar tuhume-tuhume na aikata laifukan aitakat zamba, da almundahana tun daga shekarar 1990.

    Wannan shi ne karon farko da aka fara ganin shit un bayan da aka kai shi gidan yari a kan aikata laifin raina umarnin kotu.

    Matakin ya haddasa mummunanr zanga-zanga da kwasar ganima na ƙone-ƙone wanda na tsawon mako guda a kasar Afirka Ta Kudu.

    Yana zaune shiru a kan wata babbar kujerar ofis a wani dakin gidan yari marar fasali.

    Yana sanye da baƙar kwat da jar laktaye, kuma ya ka yi magana a takaice ne a yayin da lauyaunsa ke neman a ɗage sauraron karara.

    An yi sauraron karar ne ta shafin yanar gizo – saboda damuwar da ake da ita kan annobar korona.

    Yanzu haka Mista Zuma ya shafe fiye da mako daya a gidan yari bayan da aka same shi da aikata laifin raina kotu – da ya ki ya halarci zaman kotun na daban kan binciken cin hanci da rashawa.

    Matakin yanke wa Mista Zumu hukuncin daurin watanni 15 a gidan yarin ya haifar da zamga-zangar da ba tare da ɓata lokaci ba ta rikiɗe ta zama mummunan tashin hankali.

    Ta kuma haddasa mutuwar mutum fiye da 200, da kuma sace-sacen da ƙone-ƙonen a fadin kasar.

  15. Kalli yadda alhazai ke barin Masallacin Namirah

    Alhazai sun bar Masallacin Namirah bayan kammala sallolin azahar da la'asar da aka haɗe su a lokaci guda.

    Bidiyo daga Haramain Sharifain

  16. Mutum 13 sun mutu a gobarar tankar man fetur

    Kenya Tanker

    Asalin hoton, AFP

    Mutume akalla 13 ne suka mutu a loacin da wata tankar mai da fadi ta kuma kama da wuta a yammacin kasar Kenya cikin karshen mako.

    Babbar motar ta yi taho-mu-gama da wata motar a kan babbar hanyar da ke tsakanin garuruwan Kisumu da Busia a daren Asabar.

    Shaidu sun bayyana wurin da hadarin ya faru a matsayin wani ‘’mummuna tashin gobara’’.

    Mutane sun yi ta tururuwa wurin abkuwar hadarin dauke da jarkoki sun kwasar man da yake Malala daga cikin tankar da ta fadi kafin ta fashe ta kama da wuta.

    Wani jami’in ƴan sanda a yankin ya ce mutum 24 da suka samu munanan kuna na kwance a asibiti, kana ya ce kananan yara na cikin wadanda suka jikkata.

    Har yanzu masu bincike na ta gudanar da aikin a wurin da hadarin ya faru tare da gargadin cewa adadin wadanda suka mutun ka iya karuwa.

    "Muna bukatar binciken kwakwaf don gano ko akwai mutanen da suka riga suka kone kurmus, a inda aka gano ƙasusuwa,’’ babban jami’a Charles Chacha ya ce.

    Ya dauki tsawon lokaci wa jami’an kwana-kwana su kai ga wurin da hadarin ya faru, a kusada garin Malanga, mai nisan kilomita 320 (mil 200) arewa maso yammacin Nairobi babban birnin kasar.

    Wata babbar motar daukar kaya ce dauke da madara da ke kan tafiya ta yi taho mu gama da tankar man.

    Shaidu sun ce babura da daa e aka gano na cin wuta a kusa da wuri hadarin..

  17. Yan bindiga sun harbe mutum takwas a lokacin wani biki a Mexico

    Mexico Police

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan-sanda a Mexico sun ce ƴan bindiga sun harbe mutane takwas lokacin wani biki a jihar Zacatecas da ke arewacin kasar.

    An kuma jikkata wasu mutum shida a lamarin wanda ya faru a karshen mako a garin Panuco.

    Hukumomin kasar na bincike ko kungiyoyi mafiya karfi a na masu aikata laifuka a kasar na da hannu a lamarin.

    Sun ce kungiyoyin Sinaloa da Jalisco New Generation sun tsaurara kai hare-hare a jihohin arewacin kasar don neman iko da hanyoyin da ake amfani da su wajen fasa kaurin miyagun kwayoyi tsakanin Mexico da Amurka.

  18. Hotunan wasu alhazai a filin Arafa suna sauraron huɗuba

    Anan wasu alhazan ne suke sauraron huɗuba a filin Arafa.

    filin arafa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    filin arafa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    filin arafa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    filin arafa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

  19. Azahar ta yi a filin Arafa

    Sheikh Emad Baqree ya rangaɗa kiran Sallar Azahar daga Masallacin Al Namirah da ke Filin Arafa.

    A irin wannan lokaci alhazai kan haɗe sallolin azahar da la'asar ne sai kuma su ci gaba da addu'o'insu.

  20. An sauya wa Ɗakin Ka'aba rigar Kiswah

    A jiya Lahadi ne jajiberin Ranar Arafa ne aka yi gagarumin aikin sauya rigar Ɗakin Ka'aba a birnin Makka na kasar Saudiyya, wanda ake yi sau daya a kowace shekara.

    Ana wannan aikin ne a lokacin da alhazai suka bar birnin Makka suke tsayuwar Arfa, wadda ita ce babban rukunin aikin Hajji.

    Sabon abin da alhazai za su tarar idan suka koma Makka ranar Babbar Sallah shi ne sabuwar rigar Ka'aba.

    Ana ɗaukar sauya wa Ka'aba riga a matsayin wani babban lamari na girmama ɗakin na Allah da kuma tsarkake shi.

    Sauya rigar na daga abubuwa mafiya daɗewa a tarihin duniya.

    An shafe ɗaruruwan shekaru ana sauya wa Ka'aba riga gabanin zuwan Musulunci, abin da wasu sarakunan Larabawa suka riƙe kuma ya zama wani babban abin alfahari a wajen Larabawa.