window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/02/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka ƙarshen wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai kuma gobe Juma'a, inda za mu ɗora daga inda muka tsaya.

    A madadin sauran abokan, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Tattalin arzikin Syria zai yi aƙalla shekara 50 kafin ya gyaru - MDD

    Syria

    Asalin hoton, Syria Civil Defence

    Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce tattalin arzikin Syria zai ɗauki sama da shekara 50 kafin ya koma yadda yake kafin yaƙin basasar ƙasar.

    Shirin raya ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce rikicin na shekara goma sha hudu ya rushe ababen more rayuwa da dama.

    Bugu da ƙari ga kuma takunkuman da aka ƙaƙaba wa tsohuwar gwamnatin Assad.

    Binciken ya ƙara da cewa 9 daga cikin ƴan Syria 10 na rayuwa cikin talauci a yanzu, don haka ana buƙatar ingantaccen tsari don farfado da tattalin arzikin ƙasar.

  3. Gwamnatin Ghana ta ƙara kuɗin masu aikin ƙwadago, Abdussalam Ibrahim Ahmed

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara kuɗaɗen da ake da biya a kullum na ƙwadago da kimanin kashi goma cikin ɗari, wanda zai fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Maris.

    An cimma matsayar ce a ƙarshen wani taron haɗin gwiwa kan batun, wanda ya ƙunshi wakilan gwamnati da masu ɗaukar ƴan ƙwadago aiki, da kuma ƙungiyoyin ma'aikata.

    Ƙarin kuɗaɗen ƙwadagon da ake biya a duk rana, na kashi goma cikin ɗari da aka yi ƙasar ta Ghana, ya tashi ne daga Cedi 18.17, zuwa Cedi 19.97.

    Kamfanin dillancin labarai na ƙasar Ghanar (GNA) ya ruwaito cewa, an cimma matsayar ce, kamar yadda dokar da ta shafi harkokin ƙwadago ta ƙasar ta tanada.

    Sakamakon amincewar kwamitin wakilan gwamnati da na masu ɗaukar ƴan ƙwadago aiki, da kuma na ƙungiyoyin ma'aikata, a wajen taron haɗin gwiwa da ya yi kan wannan batu yau Alhamis, a birnin Accra, inda aka yi la'akari da ƙalubalen tattalin arziki da ake fama da su, da tsadar rayuwa da dai sauran su.

    Kwamitin, wanda ya bayar da shawarar a ɗauke wa wannan nau'i na ƴan ƙwadago biyan haraji, ya buƙaci ma'aikatu da cibiyoyi da kuma ƙungiyoyi da ke biyan ƙasa da wannan sabon farashi, da su yi ƙoƙarin gyara shi zuwa ga abin da aka amince da shi.

    Saboda za a hukunta duk wanda ya yi biris da hakan kamar yadda doka ta tanada.

  4. Zan aiwatar da shawarwarin babban taron ƙasa - Janar Tchiani

    ...

    Asalin hoton, RTN

    Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar, Birgediya Janar Abdourahamane Tiani ya ce zai aiwatar da shawarwari da matakan da aka cimma a babban taron ƙasar.

    Tiani ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu, inda ya ce zai duba tare da nazarin matakan da aka ɗauka a taron.

    Babban taron ƙasar ya bayar da shawarwari masu yawa, ciki har da amince Tiani ya yi shekara biyar yana mulkin riƙon-ƙwarya, sannan an amince masa ya tsaya takara bayan ƙasar ta koma tsarin dimukuraɗiyya.

    Ya ce zai ba muhamman matakan da suka shafi ƙasar, ciki har da batun haƙo albarkatun ƙasar da batutuwan da suka shafi muhalli da tsaro da mulki da ilimi da kuma alaƙar ƙasar da ƙasashen duniya.

    Ya nanata cewa taron ya samar da tsarin komawa mulkin dimukuraɗiyya, da kuma tsara yadda mulkin ƙasar zai kasance.

  5. Faransa ta miƙa wa Ivory Coast sansanin dakarunta da ke ƙasar

    Faransa

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Faransa sun mallaka sansaninta na ƙarshe a ƙasar Ivory Coast zuwa ga rundunar sojin ƙasar, wanda ake ganin hakan zai ƙara rage ƙarfin sojin Faransa a Afirka ta yamma.

    Sai dai ministan tsaron Ivory Coast, Tene Birahima Outtara ya ce wannan ba yana nufin an kawo ƙarshen alaƙar soji tsakanin ƙasarsa da Faransa.

    "Za mu haɗa wata sabuwar yarjejeniyar ce da Faransa."

    Sansanin sojin da ke Port-Bouet yana kusa ne da filin jirgin Abidjan, kuma an sanya masa sunan babban hafsan sojin ƙasar na farko ne, Thomas d'Aquin Ouattara.

    Sojojin Faransa guda 600 za su fice daga ƙasar ne a hankali a wannan shekarar, sai dai hukumomi a ƙasar kusan sojoji guda 100 za su ci gaba da zama a ƙasar domin horar da sojojin ƙasar.

    Yanzu ƙasashen Gabon da Djibouti ne kawai suke da sojojin Faransa a nahiyar, kuma ba su wuce 2,000 kamar yadda wata majiya ta tabbatar.

  6. Ana shirin hana jagoran ƴan adawa a Kamaru yin tarukan siyasa

    Ministan harkokin cikin gida a Kamaru, Paul Atanga Nji ya umarci gwamnan Adamawan Kamaru ya ɗauki matakai don hana tarukan da jagoran jam’iyyar adawa ta PCRN Cabral Libii zai jagoranta a faɗin lardinsa.

    Cabral Libii wanda ɗan majalisar dokoki ne, yana yunƙurin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe.

    Shi ne ya zo na uku a sakamakon zaɓen 2018 kuma ɗan takarar shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a wancan lokaci.

  7. Abin fashewa ya hallaka mutum bakwai a Syria

    Aƙalla fararen hula bakwai da suka haɗa da mata da yaro ƙarami sun rasa rayukansu a arewa maso yammacin Siriya sakamakon fashewar wasu makamai.

    Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Siriya ta ce fashewar ta faru ne sakamakon tashin wasu makamai da aka ajiye kusa da gidan mutanen.

    Al'amarin ya faru kwana guda bayan wata ƙungiya mai zaman kanta ta yi gargaɗin cewa kowane bam uku cikin goma da aka bari a Siriya bayan yaƙin basasa ba zai iya tashi ba.

    Sama da mutane 100 ne suka muku daga irin waɗannan makamai a watan Janairu.

  8. Dubban Isra'ilawa sun taru don alhinin gawarwakin da Hamas ta mayar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Dubban Isra'ilawa ne suka taru a sansanin da ake kira da "hostage square' da ke Tel Aviv domin jimamin waɗanda suka rasu a hannun Hamas.

    Zaman makokin na zuwa ne bayan Hamas ta miƙa musu gawarwakin mutum huɗu da suka rasu daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su.

    Masu binciken ƙwaƙwaf na gawarwaki na Isra'ila suna ci gaba da nazarin gawarwakin domin tabbatar da ikirarin Hamas cewa uku daga cikin gawarwakin na wata mata ce da ƴaƴanta biyu.

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana rashin daɗinsa da abin da ya kira "dabbancin Hamas", sannan ya ɗauki alwashin ganin bayansu.

    Wasu waɗanda ake tunanin mayaƙan Hamas ne da suka rufe fuskokinsu suka miƙa gawarwakin ga ƙungiyar Red Cross a garin Khan Younis da Zirin Gaza.

  9. Za mu farauto Bello Turji - Sojin Najeriya

    Soja

    Asalin hoton, @DefenseNigeria

    Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar janar Olufemi Oluyede, ya ce sojojin Najeriya za su yi farautar ɗanbindigar nan Bello Turji da hukumomin ƙasar ke nema ruwa a jallo.

    Babban hafsan ya bayyana haka ne a birnin Gusau da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin ƙasar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar shirin sojojin Najeriya da aka yi wa laƙabi da Fansar Yamma, inda ya ce nan ba da daɗewa ba, Turji zai zama labari.

    "Yanzu haka da muke magana da ku, Bello Turji na ta guje-guje ne, amma duk inda ya buya, za a bi shi, mu yi farautarsa. Ya ci gaba da guje-gujensa, amma zai gama, kuma za mu cimmasa," in ji shi.

    Oluyede ya kuma bayyana wasu nasarorin da sojojin suka samu, inda ya ƙara da cewa dakarun ƙasar sun kashe manyan jagororin ƴanbindigar a cikin watannin da suka gabata.

    Bello Turji na daga cikin jagororin ƴan fashin daji waɗanda suka addabi ƙauyukan arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Zamfara, wadda rikicin ƴan bindiga ya yi ƙamari.

    A baya-bayan nan dakarun Najeriya sun matsa ƙaimi wajen kai wa ƴan fashin daji farmaki, a wani yunƙuri na kawar da matsalar tsaro a arewa maso yammacin ƙasar.

    Sai dai duk da haka ƙauyuka da dama a jihar ta Zamfara, da wasu jihohin masu maƙwaftaka, kamar Sokoto da Katsina na ci gaba da fuskantar hare-haren na ƴan fashin daji.

  10. APC ta ce ba za ta shiga zaɓen ƙananan hukukomin jihar Osun ba

    APC

    Asalin hoton, Getty Images

    Jam'iyyar APC a Osun ta ce ba za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar, a ranar Asabar, 22 ga Fabrairu ba.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a ranar 17 ga Fabrairu, wadda sakataren watsa labaran jam'iyyar, Alao Kamoruddeen ya fitar, sannan ya aika zuwa ga hukumar zaɓen jihar mai zaman kanta, OSSIEC.

    Wasiƙar, wadda NAN ta gani a ranar Alhamis a Osogbo, ta nuna cewa APC ba za ta shiga zaɓen ba ne lura da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wanda ya mayar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolinsu aiki.

  11. Rikicin Kongo: Mutum 30,000 sun tsere zuwa Burundi

    Kongo

    Asalin hoton, EPA

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yawan ƴan gudun hijirar da suka tsere zuwa Burundi sakamakon rikici a gabashin Kongo ya kai 30,000.

    Burundi mai fama da matsin tattalin arziƙi, na fuskantar ƙwararar mutanen da suka rasa muhallansu irinsa na farko a shekaru 25.

    Sojojin ƙasar 10,000 da aka jibge a gabashin Kongo don su taimaka a yaƙi da ƴan tawayen da Rwanda ke goyon baya sun janye, yayin da ƴan tawayen ke ƙara dannawa.

    Dakarun Uganda sun tsallaka arewaci don karɓe ikon birnin Bunia.

    Ana fargabar rikicin zai koma maimacin wanda ya faru a Kongo shekaru 25 da suka gabata, abin da ya haifar da asarar rayuka sakamakon yunwa da ɓarkewar cuta.

  12. Za a biya kowane fasinjan jirgin da ya faɗi a Toronto dala 30,000

    Jirgi

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin jirgin sama na Delta Air Lines da ke Amurka ya ce zai biya kowane fasinja da yake cikin jirginsu da ya faɗi a birnin Toronto na ƙasar Canada, kuɗi dala 30,000.

    Jirgin ya samu matsala ne, inda ya faɗo a birnin Toronto, amma dukkan fasinjojin sun tsira da ransu, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da musabbabin faɗuwar ba.

    Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 76 da ma'aikatan jirgin guda huɗu, ya taso ne daga birnin Minneapolis na Amurka, kafin ya faɗi a birnin na ƙasar Canada.

    Ofishin lauyoyi na Rochon Genova ya ce wasu fasinjoji da iyalansu ne suka neme su, domin su bi musu kadi da neman diyya.

    Lauya Vincent Genova ya ce suna fata a samu mashala "cikin sauƙi da zai yi wa kowa daɗi," inda ya ce waɗanda yake wakilta "sun ji raunuka har sai da suka yi jinya a asibiti."

    A wani saƙon imel da ya tura wa BBC, Genova ya ce dala 30,000 somin-taɓi ne kamfanin zai bai wa fasinjojin, amma za a cire kuɗin daga cikin ainihin kuɗin diyyar da aka cimmawa daga baya.

    A shekarar 2013, kamfanin jirgin Asiana ya biya fasinjojin da jirginsu ya faɗi a San Francisco dala 10,000 a matsayin diyyar farko.

  13. Kotu ta ci Rubiales tarar dala 10,000 saboda sumbatar ƴar wasa ba da amincewarta ba

    Luis Rubiales

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar kotu a Madrid ta samu tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya, Luis Rubiales da laifin sumbatar ƴar wasa ba tare da yardarta ba, a wasan ƙarshe na cin kofin Duniya ta mata.

    Kotun ta kuma ci tararsa dala 10,000 saboda laifin, sai dai ta wanke shi bisa zargin tilastawa ƴar wasan.

    A makon da ya gabata ne, Mista Rubiales ya faɗa wa kotu cewa Jenni Hermoso ta ba shi damar ya sumbaceta a lokacin da ya bayyana da na ''farin ciki'' bayan lashe gasar Kofin Duniya.

  14. Na yi nadamar rushe zaɓen June 12 - IBB

    IBB

    Asalin hoton, Youtube/Channels

    Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), mai ritaya ya bayyana takaicinsa kan rushe zaɓen shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Yunin 1993.

    Yayin da yake jawabi a wurin bikin ƙaddamar da littafin da ya rubuta kan tarihin rayuwarsa mai taken “A Journey in Service”, a Abuja, babban birnin ƙasar, IBB ya ce in da zai samu wata damar da ya tabbatar da zaɓen.

    Zaɓen na June 12 - wanda manyan ƴantakara biyu suka yi kankankan, Mashood Abiola na jam'iyyar SDP da Bashir Usman Tofa na jam'iyyar NRC - Abiola ne ya yi nasara.

    “Na yi nadamar rushe zaɓen June 12, na kuma ɗauki alhakin matakin - wanda aka ɗauka a zamanin mulkina, na kuma ɗauki hakan a matsayin kuskure.''

  15. An bayar da shawarar samar da mulkin rikon ƙwarya na shekara biyar a Nijar

    Kwamitin shirya babban taron ƙasa na Jamhuriyar Nijar ya bayar da shawarar samar da wa'adin riƙon ƙwarya na tsawon shekara biyar domin miƙa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula.

    An cimma hakan ne a babban taron ƙasa da aka kwashe tsawon mako guda ana gudanarwa a ƙasar, da a wani mataki na shirye-shiryen mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyya.

    A baya shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya alƙawarta mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyya a cikin shekara uku.

    A shekarar 2023 ne sojoji suka ƙwace mulkin Nijar, bayan hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, inda suka bayar da hujja da taɓarɓarewar matsalar tsaro da rashin shugabanci nagari.

  16. 'Dakarun Isra'ila sun harbe Bafalasɗine guda a Gaza'

    Kafar yaɗa labaran Falasɗinawa taa ce dakarun Isra'ila a birnin Gaza sun harbe mutum guda.

    Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba game da Iƙirarin, amma ta bayyana yadda sojoji suka buɗe wa Falasɗinawan da suka yi musu barazana wuta a wasu yankunan Gaza.

    Sojoji sun ce an harbi wani mutum kai-tsaye bayan ya ci gaba da tunkarar inda suke duk da gargaɗin da suka yi masa.

  17. Faransa ta kammala kwashe sojojinta daga Ivory Coast

    sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A baya-bayan nan Faransa na sake fasalta alaƙar sojinta da wasu ƙasashen Afirka

    Faransa ta miƙa wa hukukomin Ivory Coast sansanin sojinta ɗaya tilo da ke ƙasar, a wani mataki na kawo ƙarshen ayyukan sojojinta a ƙasar na tsawon gomman shekaru.

    Ministocin tsaron ƙasashen biyu ne suka sanya hannu kan takardun miƙa sansanin, jim kaɗan bayan ɗaga tutar Ivory Caost a filin farenti na sansanin.

    Ministan tsaron Ivory Coast Tene Birahima Ouattara ya ce matakin wani sabon babi ne a ƙawancen da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Yayin da shi kuma takwaransa na Faransa, Sebastien Lecornu ya ce sauyi za a samu a wanzuwar Faransa a Ivory Coast, ba shuɗewa ba, inda ya bayyana bikin miƙa sansanin a matsayin wani mataki na tarihi.

    Sansanin mai girman eka 570 da ke kusa da Abidjan, babban birnin ƙasar ya kasance wani muhimmin wuri a harkar tsaron ƙasar tun shekarar 1987, inda ya taimaka wajen daidaita ƙasar - wadda ke kan gaba a arzikin cocoa a duniya - bayan juye-juyen mulki da tashin hankalin da ya ɓarke a ƙasar bayan 2000.

    An kuma sauya wa sansanin suna zuwa 'Thomas d'Aquin Ouattara'- sunan babban hafsan sojin ƙasar na farko - da aka sanya hotonsa a sansanin domin girmamawa a gare shi.

    Faransa na sake fasalta alaƙar sojinta da ƙasashen Afirka bayan korar dakarunta daga ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar - inda sojojin da ke adawa da Faransa suka ƙwace mulki.

    Kusan sojoji 1,000 ne Faransa ta girke a sansanin domin taimaka wa dakarun ƙasar wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi da ke ƙaddamar da hare-hare a wasu sassan ƙasashen yammacin Afirka.

    To sai dai ana sa ran kimanin sojoji 100 za su ci gaba da zama domin bayar da horo da taimaka wa ayyukan wanzar da zaman lafiya.

    Alaƙar soji tsakanin ƙasashen biyu ta faro ne tun shekarar 1961 lokacin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar soji, bayan samun ƴancin kan ƙasar, yayin da alaƙar ƙasashen biyu ta soma tun zamanin mulkin mallaka.

  18. Ana bikin ƙaddamar da littafin tarihin Ibrahim Babangida

    Janar Ibrahim Badamasi Babangida

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsoffin shugabannin Najeriya da na ƙasashe masu maƙwabtaka da sauran masu faɗa a-ji a ƙasar suna birnin Abuja inda ake taron ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

    Bikin wanda ya samu halartar tsoffin shugabannin Najeriya da suka haɗa da Janar Yakubu Gowon da janar Olusegun Obasanjo da Abdussalami Abubakar da kuma tsoffin shugabannin ƙasar Ghana, Nana Akufo Addo da na Sierra Leone Arnest Bai Koroma, na son samar da wata gidauniya da za ta tallafa wa al'ummar Najeriya musamman marasa ƙarfi.

    Littafin mai shafi fiye da 400 da janar Babangida ya rubuta da hannunsa ya yi waiwaye kan rayuwar tsohon shugaban ƙasar daga yarintarsa a matsayin maraya har zuwa rayuwarsa ta makaranta da aikin soji inda ya zama shugaban ƙasa.

    Da yake yinbitar littafin, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce littafin ya yi cikakken bayani kan juyin mulkin soji da irin rawar da janar Ibrahim Babangidan ya taka.

    A karon faro janar Babangida a cikin littafin ya amince da cewa Cif Mashood Abiola shi ne ya ci zaɓen da aka rushe a ranar 12 ga watan Yunin 1993.

    "Lallai Mashood Abiola shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 bayan da ya samu ƙuri'u fiye da miliyan takwas inda ya samu nasara a kan Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC mai ƙuri'a fiye da miliyan biyar." In ji Janar Babangida a cikin littafin da ya rubuta da kansa.

    Abdulsamad Isiyaka Rabi'u shugaban rukunin kamfanonin BUA da Janar Theoplus Ɗanjuma wanda aka wakilta suka jagoranci ƙaddamar da littafin da ɗakin karatu.

    Yayin da Abdussamad ya bayar da kyautar naira biliyan biyar ga ginin ɗakin karatun, shi kuma janar Ɗanjuma ya sanar da bayar da naira biliyan uku, inda shi kuma Alhaji Aliko Ɗangote ya sanar da naira biliyan takwas.

    Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya bayar da naira miliyan 50 inda shi kuma mataimakin shugaban majalisar ya sanar da naira miliyan 20.

  19. Hotunan yadda sojojin Isra'ila suka karɓi gawarwakin Isra'ilawan da Hamas ta saki

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, IDF

    Rundunar sojin Isra'ila ta saki hotunan yadda dakarunta suka karɓi gawarwakin Isra'ilawan da Hamas ta saki.

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, IDF

    Gawarwakin lulluɓe da tutar Isra'ila za a wuce da su zuwa cibiyar bincike domin tantance abin da ya yi sanadin mutuwarsu.

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, IDF

    Ba a dai bayyana wurin da aka ɗauki hotunan ba. Dakarun IDF ɗin ne dai suka karɓi gawarwakin da safiyar yau a Gaza daga hannun Red Cross kafin su wuce da su zuwa Isra'ila.

  20. Sojojin Isra'ila sun ce gawarwakin ƴan ƙasarta sun isa Isra'ila

    Motoci

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun ce gwarwakin Isra'ilawan da Hamas ta saki yau a Gaza sun isa ƙasar.

    Sojojin na Isra'ila - waɗanda suka ɗauko gawarwakin za su wuce da su zuwa cibiyar bincike ta Abu Kabir da ke Jaffa domin tabbatar da gawarwakin.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce tana tare da iyalan gawarwakin a wannan lokaci na alhinin.

    mutane

    Asalin hoton, Isra'el Police