Chelsea na zawarcin Guehi, Arsenal na da yaƙinin saye Zubimendi

Marc Guehi

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea da fafutikar ganin ta doke abokan hamayyarta a Firimiya wajen saye ɗan wasan Crystal Palace da aka yi wa kuɗi fam miliyan 70, Marc Guehi. Matashin mai shekara 24 ya koma Palace daga Chelsea a shekara ta 2021. (Mirror)

Liverpool da Manchester City na kwaɗayin saye ɗan wasan Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong, da ke da yarjejeniya da ƙungiyar ta Jamus na sayar da shi kan yuro miliyan 40. Matashin daga Netherlands mai shekara 24, ya zauna a makarantar horaswa ta City kafin Celtic ta saye shi a 2019. (Teamtalk)

Arsenal na da kwarin gwiwar cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya a Real Sociedad da Sifaniya, Martin Zubimendi, mai shekara 26, wanda ke son zama da ƙungiyarsa maimakon tafiya Liverpool a kakar da ta gabata. (Teamtalk)

Mai tsaron raga a Liverpool da Jamhuriyar Ireland, Caoimhin Kelleher mai shekara 26, ya kasance wanda Chelsea ke hange a sabuwar kaka. Kungiyar dai na fatan biyan fam miliyan 40 kan ɗan wasan. (Football Insider)

Ɗan wasan Barcelona mai shekara 17, Lamine Yamal ya yi watsi da rade-radin tafiyarsa Paris St-Germain - yana mai jadadda cewa yana kaunar Barca. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Ɗan wasan gaba a Liverpool da Colombia, Luis Diaz mai shekara 28, na son sanya hannu a sabon kwantiragi - duk da cewa wanda yake kai a yanzu sai nan da shekara biyu zai kare. (TBR Football)

Leicester City da Crystal Palace na sa ido kan ɗan wasan gaba a Midtjylland da Guinea-Bissau, Franculino Dju mai shekara 20, wanda ya zo ƙungiyar daga makarantar horaswa ta Benfica. (Bold - in Danish)

Tsohon ɗan wasan Fulham da Arsenal da West Ham, Luis Boa Morte, wanda yanzu haka ke horas da Guinea-Bissau na son karban aikin horas da Blackburn Rovers. (Sun)