window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail, Aisha Babangida da Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Rufewa

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya daga nan sashen Hausa na BBC.

  2. Iran ta ce sakaci ne ya haifar da mummunar fashewa a Iran

    Ministan cikin gida na Iran ya ce mummunar fashewar da ta faru a tashar jirgin ruwa ta kasuwanci mafi girma a ƙasar ta faru ne sakamakon sakaci da kuma gazawa wajen ɗaukan matakan kariya.

    A cewar wakiliyar BBC, Eskander Momeni wanda ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru ya faɗa wa gidan Talabijin na Iran cewa wasu kayayyaki da ke tashar jirgin bai kamata a ce suna wajen ba.

    Fashewar da ta faru shekaran jiya a tashar jirgin ruwa na Shahid Raja'ee ta halaka mutum sittin da biyar tare da raunata fiye da mutum dubu ɗaya.

    Mista Momeni ya ce an gano wasu daga cikin mutanen da ke da hannu a lamarin kuma an yi masu sammaci.

  3. Gwamnatin Najeriya ta damu da yadda ake damfarar 'yan ƙasar a Intanet

    Maitama Tuggar

    Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun karuwar aikata laifuka da damfara ta Intanet a yammacin Afrika

    Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana damuwar a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumarsa ya fitar.

    Ministan ya yi zargin cewar masu aikata laifin ta Intanet sun aikata hakan a kan 'yan Najeriya, ta hanyar yi musu romon-baka.

    Sai dai masana harkokin sadarwar a Najeirya na ganin akwai sakacin hukumomin ƙasashen waje, wajen aiwatar da dokoki da ke bai wa hukumomin da ke sanya idanu damar yin aikin da suka dace don magance wannan matsala.

    Wannan na zuwa ne bayan asarar kuɗi da ƴan Najeriya suka takfa a wani tsarin zuba jari mai suna CryptoBank Exchange wanda aka fi sani da CBEX ya ja hankali a ƙasar, musamman a kafofin sadarwa.

    Wannan matsalar ta zo ne a daidai lokacin da ƴan ƙasar suke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa da rashin kuɗi, wanda ya biyo bayan janye tallafin man fetur da karyewar darajar naira.

    Rahotanni sun ce kuɗin da ƴan Najeriya suka yi asara a tsarin na CBEX sun haura naira tiriliyan ɗaya, wanda hakan ya sa wasu suke mamakin yadda ƴan ƙasar suka iya tara maƙudan kuɗi haka cikin ƙanƙanin lokaci.

    Tuni dai Hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar ta sanar da fara gudanar da bincike kan lamarin.

  4. An sa ranar zaɓen sabon Fafaroma a Rome

    Jana'izar Fafaroma a Vatican
    Bayanan hoto, Jana'izar Fafaroma a Vatican

    Manyan Limaman cocin Katolika da ke ganawa a Fadar Vatican sun ayyana Larabar makon gobe a matsayin ranar soma shirin zaɓen magajin Fafaroma Francis.

    Manyan limamai ɗari da talatin da biyar ne suka cancanci su yi zaɓe inda za su kasance cikin cocin Sistine ba tare da sanin duk abin da ke faruwa a duniya ba.

    Limaman da suka zaɓi marigayi Francis sun shafe kwana biyu suna kaɗa ƙuri'a - amma wasu na ganin zaɓen na wannan karon zai iya ɗaukan dogon lokaci kasancewar galibin manyan limaman da Francis ne ya naɗa su sun fito ne daga ƙasashe masu tasowa sannan kuma ba su san junansu sosai ba.

  5. Ghana ta kaddamar da shirin raba wa dalibai mata Kunzugun al'ada kyauta

    bbc

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Ghana ta kaddamar da shirin rabawa dalibai mata kunzugun al'ada ko pad a turanci, kyauta.

    Shugaban ƙasar John Dramani Mahama, ya bayyana shirin a matsayin wani gagarumin mataki na mayar da martaba da kwarin gwiwa da kuma damammaki ga dalibai mata a ƙasar.

    An ware sama da miliyan 292 a cikin kasafin kudin shekarar 2025 domin samar da kunzugun ga dalibai mata a makarantun firmare da na sakandare a faɗin ƙasar baki ɗaya.

    Wani bincike da BBC ta taba gudanarwa a baya ya nuna cewa kashi 1 cikin 7 na kuɗaɗen da mata ke samu har da ma'aikata a Ghana suna kashe su ne ta hanyar sayen Kunzugun al'ada.

    Binciken da BBC ta gudanar a ƙasahen Afirka 9 ya nuna cewa galibin mata musamman matasa na fuskantar kalubale wajen iya sayen Kunzugu a lokutan al'ada.

    Ghana na ɗaya daga cikin ƙasashen da sayen kunzugu ke yi wa mata wahala a lokacin al'ada. Ana ganin wannan mataki a yanzu gwamnati saukaka ko rage wahalhalun mata musamman masu tasowa ta fannin samun kunzugu a lokacin al'ada.

  6. Falasɗinawa sun ba da bahasi kan Isra'ila a kotun duniya

    Wani babban jami'in Falasɗinu ya shaida wa kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa da ke Hague cewa Isra'ila na toshe duk wasu hanyoyin shigar da kayan agaji ga Falasɗinawa a matsayin makamin yaƙi.

    Ammar Hijazi, ya shaida wa kotun cewa kusan dukkan Falasɗinawa ba sa samun ruwan sha sannan kuma wuraren da Majalisar Dinkin Duniya ke ajiye kayan agaji yanzu babu komai a ciki.

    Daraktar sadarwa a hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ke cewa kusan wata biyu ke nan babu wani abu da ya shiga Gaza - babu ruwa, babu hatsi.

    Al'umma ce da kacokan ta dogara kan kayayyakin agaji.

    Kotun ta soma zaman sauraron bahasi na kwana biyar domin yin nazari kan nauyin da Isra'ila take da shi na samar da jin ƙai a Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

    Isra'ila ta gabatar da jawabin kare kanta a rubuce.

    Sai dai da yake magana, ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar ya ce zaman kotun wata dabara ce ta muzgunawa ƙasarsa.

  7. Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen kare rayuka da dukiyar al'ummar ƙasar lamarin da ya sanya masu aikata laifi ke kai farmaki tare da hallaka al'umma.

    Ƙungiyar ta bayyana haka ne a matsayin martani kan rahotanni kai hare-hare a jihar Zamfara, inda aka hallaka "mutane kimanin 20".

    A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi ya yi zargin cewa akwai nakasu a dabarun da Najeriyar ke amfani da su wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.

    "Dabarun da gwamnati ke amfani da su wajen kare mutane na da rauni, kuma ya kamata a sake dabara," in ji Sanusi.

    Ya kuma yi zargin cewa a yanzu ƴan siyasar ƙasar sun mayar da hankali ne wajen tunkarar zaɓen shekara ta 2027 a maimakon kare rayuwar al’umma.

    "Abin da ƴan siyasa suka mayar da hankali a kai shi ne ya za mu ci zaɓe?”

    Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta fifita kyautata rayuwar mutane a maimakon siyasa.

  8. Gwamnan Delta Oborevwori da Okowa sun koma APC a hukumance

    Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori da wanda ya gada Ifeanyi Okowa sun koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a hukumance.

    Yayin wani biki da aka gudanar a Asaba babban birnin jihar a yau Litinin, 'yansiyasar da abokan hulɗarsu da dama sun koma jam'iyyar ta Shugaban Ƙasa Tinubu bayan ficewa daga PDP mai adawa.

    Jiga-jigan APC ne suka karɓe su da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da shugaban APC na ƙasa Abdullahi Ganduje, da Sanata Adams Oshiomole, da Gwamnan Imo Hope Uzodimma.

    Gwamna Oborevwori ya ce matsawa suka yi ba sauyi ba.

    "Abin da kuke gani a yau motsi ne ba wai sauya jam'iyya ba. Mun tattauna da masu ruwa da tsaki a kowane mataki. Shugaban ƙasa ya nuna mana ƙauna," in ji gwamnan.

    Tun a makon da ya gabata gwamnan da 'yanmajalisar dokoki da kwamashinoni suka sanar da shirinsu na barin PDP.

  9. Ɗaukewar lantarki ta jefa mazauna Sifaniya da Portugal cikin duhu

    Sifaniya

    Asalin hoton, Reuters

    Miliyoyin mutane a Sifaniya da Portugal sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon katsewar lantarki a sassan ƙasashen.

    Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama.

    Asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto.

    Shugabar gwamnati a yankin Madrid ta ce "abin da za mu yi shi ne mu nemi gwamnatin tarayya ta ayyana shiri na gaggawa don sojoji su kare doka da oda".

    Kamfanin lantarki na Sifaniya ya ce an gyara matsalar a yankunan arewaci da kudancin ƙasar.

    Har yanzu dai ba a san abin da ya janyo matsalar ɗaukewar wutar ba, wadda ta shafi Portugal mai maƙwabtaka.

  10. NDLEA ta ce ta kama miyagun ƙwayoyi na naira biliyan ɗaya a Kano da Legas

    Miyagun Kwayoyi

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta sanar da kama miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi da kuɗinsu ya haura naira biliyan ɗaya.

    Hukumar ta ce ta yi kamen ne a jihohin Legas da Kano da kuma Jigawa, kuma cikin mutanen da aka kama har da wasu mata ‘yan kasar waje uku.

    Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya ta zama ruwan dare, inda masharhanta ke cewa iyaye da al'umma baki daya su hada kai wajen yakar matsalar.

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku surari rahoton Zahraddeen Lawan daga Kano:
  11. Zanga-zangar ɗalibai ta tilasta rufe kwalejin Adamawa kan rashin lantarki

    Zanga-zangar ɗalibai a Adamawa

    Asalin hoton, Social Media

    Kwalejin fasaha ta jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya ta rufe makarantar tsawon mako ɗaya sakamakon zanga-zangar da ɗalibai suka gudanar.

    Bayanai sun ce zanga-zangar ta ɓarke ne sakamakon rashin ruwa da lantarki da ɗaliban makarantar ta Adamawa State Polytechnic, Yola suke fama da shi.

    Hukumar makarantar ta ce ta rufe makaranta tsawon mako ɗaya tun daga yau Litinin.

    "An ɗauki matakin ne domin bai wa hukumomi damar gyara lantarkin," a cewar wata sanarwa da rajistran makarantar Simnawa Ayuba ya sanya wa hannu.

    "An umarci ɗalibai su fice daga kwalejin kafin ƙarfe 12:00 na rana."

  12. Labarai da dumi-dumi, Putin ya sanar da gajeriyar tsagaita wuta a yaƙin Ukraine

    Vlir Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha Vlir Putin ya sanar da tsagaita wuta ta kwana uku a yaƙin da ƙasarsa ke yi da Ukraine.

    Fadar Kremlin ta ce tsagaita wutar za ta yi aiki daga safiyar 8 zuwa 11 ga watan Mayu, wadda ta yi daidai da ranar tunawa da kawo ƙarshen Yaƙin Duniya na Biyu.

    A cewar wata sanarwa, Putin ya ɗauki matakin ne "saboda dalilai na jin ƙai".

    "Rasha ta yi imanin cewa Ukraine za ta bi sawunta," in ji sanawar.

    "Idan Ukraine ta karya tsagaita wutar, rundunar sojin Rasha za ta mayar da cikakken martani.

    "Ɓangaren Rasha ya sake nuna shirinsa na na tattaunawar zaman lafiya ba tare da wani sharaɗi ba, wanda zai kawar da tushen rikicin na Ukraine da kuma tattaunawa da ƙasashe ƙawayenmu."

  13. Boko Haram ta kashe mutum 22 a arewacin Najeriya a ƙarshen mako

    Boko Haram

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi ta kashe aƙalla mutum 22 a ƙarshen mako sakamakon hare-haren da mayaƙanta suka kai a arewa maso gabashin Najeriya.

    A jihar Borno, mayaƙan sun yi wa wasu fararen hula kwanton ɓauna tare da kashe 10 da kuma wasu jami'an tsaro biyu a ranar Asabar, kamar yadda Sarkin Gwoza Mohammed Shehu Timta ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.

    A garin Kopre na jihar Adamawa ma, mayaƙan Boko Haram sun kashe mutum 10 tare da raunata wasu da yawa, a cewar mazauna yankin.

    Harin ya auka kan mafarauta ne da kuma mayaƙan sa-kai na CJTF, inda daga baya rundunar 'yansanda a jihar ta tura ƙarin dakaru, in ji mai magana da yawunta Suleiman Yahaya a yau Litinin.

    Najeriya ta daɗe tana fama da mayaƙa masu iƙirarin jihadi, inda Boko Haram da Iswap suka fi kai hare-hare a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

    A farkon makon nan ne Gwamnan Borno Babagana Zulum ya koka cewa Boko Haram ta zafafa hare-hare, abin da ke jawo koma-baya a yaƙi da 'yanbindigar.

  14. Hare-haren Amurka sun kashe gomman 'yanciranin Afirka a Yemen

    Aƙalla 'yanciranin Afirka 68 ne suka mutu sakamakon harin da Amurka ta kai wani sansanin tsare su a arewacin Yemen da ƙungiyar 'yantawayan Houthi ke iko da shi.

    Gidan talabijin na ƙungiyar mai suna Al Masirah ya ruwaito cewa wasu 47 sun ji rmunanan aunuka tare da wani bidiyo da ta wallafa na mutanen a cikin ɓaraguzai.

    Rundunar sojin Amurka ba ta ce komai ba zuwa yanzu.

    Lamarin ya faru ne 'yan awanni bayan rundunar Central Command ta sojin Amurka ta sanar cewa dakarunta sun hari wurare 800 na 'yan Houthi bisa umarnin Shugaba Donald Trump.

    Ta ce hare-haren sun kashe "ɗaruruwan mayaƙan Houthi da shugabanninsu da dama", ciki har da manyan jagorori da ke jagorantar ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

  15. Iran ta yi tayin bai wa ƙasashen Afirka fasaharta a fannin tsaro

    Iran

    Asalin hoton, @IRIMFA_EN

    Shugaban Iran Massoud Pezeshkian ya bayyana cewa yana da fatan ƙara ƙarfafa dangantaka da ƙasashen Afirka.

    Ya shaida wa taron tattalin arziki tsakanin Iran da ƙasashen Afrika a birnin Tehran cewa ƙasarsa tana da shirin bayar da ƙwarewarta a fannin tsaro da sauran fannoni kamar yadda ofishinsa ya bayyana.

    Shugaban ya zargi wasu ƙasashe da ba a bayyana ba, waɗanda ake hasashen ƙasashen Yamma ne da aikata ayyukan tarzoma a sauran ƙasashe da kuma aikata laifuka a kan ɗan'adam.

    "Maimakon shuka ƙiyayya da gaba, ya kamata mu jajirce wajen sada zumunci da ‘yan'uwantaka da ƙauna, da kasuwanci, da kuma girmama haƙƙin juna," in ji shi.

    Ana gudanar da taron ne a Tehran daga 27 zuwa 29 ga watan Afrilu, sannan za a ci gaba da taron a Isfahan daga 30 ga watan Afrilu zuwa 1 ga watan Mayu.

    Rahoton kafar yaɗa labarai ta ISNA ya bayyana cewa wadanda suka halarci taron sun hada da ‘yankasuwa 700 daga kasashen Afirka 38, da ministoci fiye da 50 da shugabannin majalisar ƴankasuwa daga ƙasashe 29 na Afirka.

    Jaridar gwamnatin Zimbabwe, Sunday Mail, ta ruwaito jiya cewa taron yana daga cikin dabarun Iran na zurfafa dangantakar tattalin arziki da ƙasashen Afirka da kuma ƙara girman cinikayya, wadda a yanzu ta kai kusan dala biliyan 1.4 a shekara.

  16. Ba a ga watan Zulki'ida ba a Najeriya - Fadar sarkin Musulmi

    Wata

    Asalin hoton, Reuters

    Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar III ta ce ranar Talata ce 1 ga watan Zulki'ida na shekarar Hijira ta 1446.

    Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jaririn watan ba a ranar Lahadi.

    A ƙa'idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.

    Hakan na nufin yau Litinin 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.

    Fadar Sarkin Musulmi

    Asalin hoton, Fadar Sarkin Musulmi

  17. Hukumar NDIC ta fara biyan masu ajiya a bankin Heritage kuɗaɗensu

    Bankin Heritage

    Asalin hoton, Heritage Bank

    Hukumar inshorar bankuna a Najeriya ta Nigeria Deposit Insurance Corporation (NDIC) ta ce ta fara biyan mutanen da kuɗaɗensu suka maƙale a Bankin Heritage da ya durƙushe.

    Kuɗaɗen sun kai naira biliyan 46.6, kuma an fara biyan waɗanda kuɗaɗen ajiyarsu suka zarta naira miliyan biyar ne da ke da inshora.

    A watan Yunin 2024 ne Babban Bankin Najeriya CBN ya karɓe lasisin Heritage, yana mai cewa mahukuntan bankin sun karya doka.

    A cewar wata sanarwa daga NDIC, an fara biyan kuɗin ne daga ranar Juma'ar da ta gabata "domin tabbatar da cewa an biya dukkan masu kuɗin ajiya a bankin".

    "Kuɗaɗen da aka fara biya na abin da aka samu ne bayan sayar da kadarorin da bankin ya mallaka," in ji sanarwar da Hawwau Gambo ta sanya wa hannu.

    Ta ƙara da cewa "akwai yiwuwar kuma adadin kuɗin su ƙunshi har waɗanda aka biya masu bin bankin bashi bayan kammala biyan masu ajiya".

  18. 'Niyyar kisa suka yi' - BBC ta gano yadda jami'an tsaron Kenya suka harbi masu zanga-zanga

    ....

    BBC ta gano mambobin rundunar ƴansandan Kenya da suka harbe masu zanga-zangar ƙin amincewa da haraji a majalisar dokokijn ƙasar a watan Yunin da ya gabata.

    Binciken BBC na sama da hotuna 5,000 ya nuna cewa waɗanda aka kashe a wajen majalisar ba su da makamai kuma ba su nuna wata barazana ba.

    Dokar ƙundin tsarin mulkin ƙasar ta Gabashin Afirka ta bayar da damar yin zanga-zangar lumana, kuma kisan da aka yi ya haifar da fushi a tsakanin jama'a.

    Duk da cewa wani kwamiti na majalisar dokokin ƙasar ya umurci Hukumar Kula da Ayyuakan Ƴansanda mai zaman kanta (IPOA) ta binciki kashe-kashen da aka yi a titunana birnin Nairobi da kuma bayyana sakamakon bincikensu a bainar jama'a, har yanzu babu wani rahoto da aka fitar dangane da kisan da aka yi a wajen majalisar kuma babu wanda aka gurfanar.

    Tawagar BBC Service World ne tayi nazari kan bidiyoyi da hotuna da masu zanga-zanga da ƴan jarida suka ɗauka a ranar. sun gano lokacin da aka ɗauki kowanne hoto ta amfani da bayanan da ke cikin na'urorin ɗaukar hoto da sa'o'in da aka yi rikodin bidiyoyi kai tsaye da kuma agogo na jama'a da ya bayyana a cikin hotunan.

    BBC ta ce sun tsara inda aka yi kisa wusu mutum uku cikin tsarin 3

    Sun tsara inda aka yi kisan wasu uku cikin tsarin 3D na zamani na majalisar dokokin Kenya, wanda hakan ya basu damar gano bindigogin da aka harba mutanen daga hannun wani ɗan sanda da kuma soja.

  19. Koriya ta Arewa ta amince sojojinta na taya Rasha yaƙar Ukraine

    Kim Jong Un

    Asalin hoton, Reuters

    A karon farko Koriya ta Arewa ta amince cewa ta tura dakarunta domin taimaka wa Rasha yakar Ukraine.

    Kafofin yaɗa labaran gwamnati a Pyongyang sun ce an aike da sojojin ne domin daƙile harin da Ukraine ta kai yankin Kursk na Rasha a bara.

    Wakiliyar BBC ta ce Shugaba Kim Jong Un na Koriya Ta Arewa ya jinjina wa dakarunsa kan abin da ya kira jarumtar da ska nuna.

    Ukraine ta sha nanata cewa dakarunta na yin gaba da gaba da na Koriya ta Arewa a filin daga.

    Sanarwar ta Pyongyang ta ce za a gina wani muhimmin abin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu a yakin.

    Amurka ta ce dole ne Koriya ta Arewa ta dauki alhakin shiga fadan.

  20. Kotun Duniya na sauraron ƙara kan matakin Isra'ila na shigar da kaya Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau Litinin ne Kotun Duniya da ke birnin Hague za ta fara zaman sauraron ra'ayoyin jama'a kan nauyin da ke kan Isra'ila na ba da damar shigar da kayan agaji a zirin Gaza da GaƁar Yammacin Kogin Jordan.

    Kusan ƙasashe 40 ne za su shiga shari'ar.

    A shekarar da ta gabata ne Isra'ila ta haramta wa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA yin aiki a ƙasar da kuma yankunan Falasɗinawa da ta mamaye.

    Ta ce hukumar ta UNRWA, ta zama ta yan Hamas amma ba tare da bayar da wata shaida ba.

    Kusan wata biyu da suka gabata ne Isra'ila ta dakatar shigar da duk wasu kayayyakin agaji zuwa zirin da ya fada matsalar yunwa.