Ma'aikacin jinyar da ya ɓace a watan jiya a Gaza yana Isra'ila - Red Cross
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce, ma'aikacin lafiyar nan Bafalasdɗne - wanda ya ɓace tun bayan wani hari da Isra'ila ta kai a Gaza a watan da ya wuce - wanda a lokacin ma'aikatan agaji goma sha biyar (15) suka mutu, yana tsare a hannun hukumomin Isra'ila.
Ƙungiyar ta ce, an ba ta damar ganin ma'aikacin na ƙungiyar, Assad al-Nsasrah, wanda ba a san halin da yake ciki ba kafin yanzu.
Sai dai hukumomin sojin Isra'ila ba su tabbatar da labarin ma.
An gano gawarwakin ma'aikatan agajin 15 binne a wani ƙaton kabari na bai-ɗaya a kudancin Gaza a watan Maris.
Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙungiyar ta Red Crescent sun zargi sojojin Isra'ila da kashe ma'aikatan a lokacin da suka kai ɗauki.