Me ayyana Hausa a matsayin harshen al'umma a Nijar ke nufi?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin harshen al'umma a hukumance.
Wannan dai na ɗauke ne a cikin wani kundi da aka saki a ranar 31 ga watan Maris na 2025 da ke ƙunshe a cikin wani kundin tsare-tsaren gwamnatin ƙasar na 2025.
Bisa kundin dai "Hausa ce harshen al'ummar," kuma "harsunan aiki su ne Ingilishi da Faransanci."
Kundin ya kuma kawo jerin wasu ƙarin harasan cikin gida ƙari a kan harshen na Hausa da suka haɗa da Zarma-Songhay, Fula, Kanuri, Gourmanche, da Larabci a matsayin "harsunan da ake magana da su a Nijar."
Wannan dai ya biyo bayan wani taron ƙasa da aka gudanar a ƙasar a watan Fabrairu wanda ya samar da shawarwari ciki har da wanda ya bai wa Abdourahamane Tchiani damar ci gaba da mulkin ƙasar har zuwa shekarar 2030.
Ma'anar Hausa a matsayin harshen al'umma

Asalin hoton, Getty Images
Tun dai kafin sanarwar ta baya-bayan nan, harshen Hausa ya zamo wanda kusan kowa na yinsa a ƙasar musamman a yankunan Zinder da Maradi da Tahou.
"Fiye da kaso 90 na al'ummar ƙasar miliyan 26 suna magana da harshen Hausa. Saboda haka ba za ka kwatanta shi da harshen Faransanci ba wanda mutum miliyan uku ne kawai suke iya amfani da shi," in ji Tahir Guimba, jami'in gwamnati a Nijar wanda yake da masaniyar tsarin.
Ya kuma ƙara da cewa "bambanci kawai yanzu shi ne Hausa ta zama harshen al'umma a hukumance saɓanin a baya - yanzu ke nan Hausa ce harshen kasuwanci da cinakayya da kuma addini.
Ƴan jamhuriyar Nijar za su iya gudanar da harkokinsu da ba na ofis ba cikin harshen Hausa bisa doka. Amma Ingilishi da Faransanci ne harshen aiki na hukuma," in ji Guimba.
Shi ma Farfesa Abdou Majingini wanda masanin harsuna ne da ke zaune a birnin Yamai na jamhuriyar ta Nijar, ya ce "ayyanawar ta ƙara tabbatar da matsayin Hausa ne a matsayin harshen al'umma ko kuma harshen haɗin kai a Nijar. Da ma can Hausa harshen al'umma ce domin kusan kowa yana yi."
Ya kuma ƙara da cewa "yanzu ne aka tabbatar da wani yunƙuri da magabatanmu suka yi a 1979 inda suka yi yunƙurin samar da harshen haɗin kai a ƙasar amma hakan bai yiwu ba a lokacin sai yanzu."
Sai dai kuma Farfesan wanda ya rubuta ƙamus na Faransanci zuwa Hausa ya ce "harshen Hausa ya kamata ma ya zama ɗaya daga cikin harsuna biyu da aka ayyana a matsayin harsunan aiki - wato Hausa ta zama ƙari a kan Ingilishi da Faransanci."
Me ya janyo ayyanawar a yanzu?
Gwamnatin sojin ta jamhuriyar Nijar dai ta ce ta ɗauki matakin ayyana harsunan Ingilishi da Faransaci a matsayin na aiki da kuma Hausa a matsayin harshen al'umma ne a ƙoƙarinta na raba kanta da tsohuwar uwar gijiyarta - Faransa, tun bayan juyin mulkin 2023 da ya janyo tumɓuke zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum.
Baya ga batun ƙarin harsuna, Nijar ta kuma ɗauki wasu matakai da suka haɗa da korar rundunar tsaron Faransa daga Nijar da yanke alaƙa da ita da sauya sunayen tituna da wuraren tarihi da ke ɗauke da sunayen Turawan Faransa.
Bugu da ƙari, jamhuriyar ta Nijar tare da sabbin ƙawayenta - Mali da Burkina Faso sun fice daga ƙungiyar ƙasashe renon Faransa.