Rufewa
A nan muka kawo muku ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye. Sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwanta lafiya.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/05/2025
Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Zubairu Ahmad
A nan muka kawo muku ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye. Sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwanta lafiya.
Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin ƙasashen Birtaniya da Faransa da Canada sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa inda suka yi Allah wadai da matakin da Isra'ila ta ɗauka na faɗaɗa ayyukan sojin da take gudanarwa a zirin Gaza, inda suka ce hakan bai dace ba.
Sun ce idan har ba a dakatar da hare-haren tare kuma da ɗage haramci da aka yi na shigar da kayayyakin agaji cikin yankin gaba ɗaya ba za su fara nazarin irin matakan da za su ɗauka kan Isra'ilar.
Ƙasashen uku da suka bayyana goyon bayansu ga yunƙurin tsagaita wuta da Amurka ke yi, sun yi kira ga Hamas da ta gaggauta sakin dukkan sauran mutanen da suka yi garkuwa da su.
Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje NiDCOM, ta karɓi wasu ƴan ƙasar 13 da akayi safararsu zuwa ƙasashen Ghana da Mali.
Hukumar a cikin wata sanarwar da ta fitar, ta ce shugabar hukumar Abike Dabiri-Erewa ce ta tarbi waɗanda abin ya shafa da suka haɗa da ƴan mata 12 da yaro 1 ɗan shekara biyar.
Ƴan matan da aka ceto sun ce an yi musu wayo ne tare da tilasta musu shiga karuwanci bayan an yaudare su da cewa za a samo musu aiki a Ghana da Mali.
Ƴan matan sun kara da cewa waɗanda suka yi safararsu sun kuma ci zarafin su.
Matsalar safarar alumma ta hanyar yaudarar su da cewa za a samo musu aiki a ƙasashen waje ya daɗe yana addabar ƙasar, inda ko a ƴan watannin baya an sami nasarar dawo da wasu matasa daga Ghana waɗanda aka tilastawa yin laifuka ta intanet.
Asalin hoton, Daily Nigerian
Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da a ba wakilin jaridar Daily Nigerian ta intanet a Najeriya, Umar Audu tsaro na shekara goma saboda binciken ƙwaƙwaf da ya yi, wanda a ciki ya bankaɗo yadda ake amfani da kuɗi wajen mallakar digirin bogi daga Jamhuriyar Benin.
Binciken Mr Audu ne ya bankaɗo harƙallar mallakar kwalin digirin ta bayan fage, da kuma yadda ake amincewa da su a Najeriya a hukumance.
A zaman majalisar a ranar Litinin, ɗanmajalisa Abubakar Fulata ne ya sanar da umarnin majalisar, sannan ya yi kira da Rundunar ƴansanda da ta tsaron masu farin kaya wato NSCDC da sauran jami'an tsaro da su tabbatar da tsaron Audu.
"Muna godiya tare da yaba jajircewar Audu. Muna kira ga Ministan Harkokin Cikin Gida ya tabbatar jami'an tsaron NCDC sun ba Audu tsaro da ma ƴansanda," in ji Fulata kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito daga NAN.
Asalin hoton, Umar UK
Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta amince da tsawaita wa'adin dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22.
Tun da farko hukumat ta sanar da dakatar da nuna finafinan ne sakamakon zarginsu da saɓa ƙa'idar hukumar, sannan ta ba masu finafinan mako ɗaya su cika ƙa'idojin hukumar.
Sai dai a wata sanarwa da shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Najeriya (MOPPAN) reshen jihar Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, ya ce an tattauna, kuma an fara samun mashalah.
"Bayan doguwar tattaunawa da shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha da wasu ma'aikatansa da wakilan Kannywood, an samu matsaya a kan:
Hukumar ta yarda ta ƙara mako ɗaya a cigaba da sakin finafinan da suke a layin fitowa don kada masu finafinan su yi asara
Za a sake zama ranar Alhamis domin sake tattaunawa domin a ƙarƙare maganar.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilan MOPPAN da Abdul Amart da Nazifi Asnanic da Abubakar Bashir Maishadda da sauransu.
Kotun duniya, ICJ, ta goyi bayan Eqautorial Guinea a wani rikici da aka shafe gwamman shekaru ana yi tsakaninta da Gabon kan wasu ƙananan tsibirrai guda 3.
Tsibirran ƙanana ne sosai kuma babu mutane a ciki, sai dai suna yanki ne da ake ganin akwai albarkatun mai da iskar gas.
Rikicin ya soma ne tun daga shekarun 1900 a lokacin da masu mulkin mallaka na Faransa da Sifaniya suka sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta raba iyakokin.
Gabon ta musanta cewa wata yarjejeniya da akayi daga baya ta nuna cewa ita ke da iko da tsibirran, sai dai babbar kotun majalisar ɗinkin duniyar ta yi watsi da hakan.
Ta yanke hukuncin cewa tsibirran na ƙarƙashin Sifaniya, kuma daga baya aka miƙawa Equatorial Guinea a lokacin da ta samu ƴanci a 1968.
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa a shirye ta ke ta yi aiki da Ukraine domin tsara yadda za a yi tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya nan gaba.
Shugaban ya faɗi haka ne bayan kammala tattaunawa ta waya da takwaransa na Amurka Donald Trump da suke shafe sa'oi biyu suna yi.
Kafar yaɗa labarai ta Rasha ta ruwaito shi yana cewa ''tsarin zai haɗa da mai yiwuwa tsagaita wuta na wani ɗan lokaci idan har an cimma wasu sharuɗɗa masu muhmmanci''.
Tattaunawar tsakanin shugabannin na zuwa ne bayan ƙaruwar hare-haren makamai masu linzami da jirage maras matuƙa da Rasha ta kai Ukraine a ƙarshen mako, duk da ƙasashen biyu sun yi tattaunawar sulhu a Istanbul a ranar Juma'a.
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Rasha da Ukraine za su soma tattaunawar tsagaita wuta nan take, wanda kuma zai kawo ƙashen yaƙin.
Shugaban ya faɗi hakan ne a shafinsa na Truth Social bayan kammala tattaunawa ta waya da takwaransa na Rasha Vladimir Putin wanda suka shafe sa'oi biyu suna yi.
Trump ya ce tattaunawar tasu ta tafi yadda ake so.
Tun da farko mista Trump ya ce yana kuma fatan tattaunawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky nan gaba a yau.
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ce aƙalla manyan motoci biyar ɗauke da abincin yara, da magunguna da kuma fulawa sun shiga Gaza, huɗu kuma suna kan hanya, bayan hana shigar da abinci na tsawon mako 11.
An dai ɗauki matakin kawo ƙarshen hana shigar da kayyayaki cikin Gaza, wanda ya kai su ga dab da faɗawa cikin yunwa, saboda matsin lamba daga Amurka.
Shugaban hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher, ya yi maraba da shigar da kayyayakin, sai dai ya ce wannan ƙalilan ne daga abin da ake buƙata a yankin.
Tun da farko firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta karɓe iko da zirin Gaza baki ɗaya domin hana Hamas wawushe kayan agajin.
Rahotanni dai na cewa an kashe fiye da mutane ɗari a cikin sa'o'i ashirin da huɗu da suka gabata.
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Isra'ila ta umarci mazauna yankin Khan Younis da su bar yankin baki ɗaya domin sun kusa far wa yankin da luguden wuta.
An umarci mazauna yankin ne su koma yankin al-Mawasai da ke yammacin Zirin a wani al'amari da ake ganin yana cikin umarnin gargaɗin ficewa mafi girma a cikin ƴan watannin da ake ciki.
A sanarwar gargaɗin da rundunar ta fitar da Larabci, kakakin rundunar Avichay Adraee ya ce, "yanki ne mai hatsarin zama," sannan ya ƙara da cewa, "ƙungiyoyin ƴanta'adda sun jawo muku masifa. Domin tsira da rayuwarku, zai fi kyau ku bar yankin."
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ne a Gaza a ranar Juma'a, inda asibitin Gaza ya ce an kashe sama da mutum 100 a cikin kwana 1.
Asalin hoton, Reuters
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce matakinsa na ba da kafar shigar da abinci zuwa Gaza bayan hana shigar da abincin na tsawon mako 11 na zuwa ne sakamakon matsin lambar da yake fuskanta daga ƙawayensa.
Toshe hanyoyin kai kayayyakin agaji zuwa Gaza dai ya sa ƙwararru kan harkar abinci daga ƙasashen duniya yin gargaɗi kan yanayi na faɗa wa ƙangin yunwa.
Asibitoci sun ce aƙalla mutum ashirin aka kashe a yau Litinin yayin da Isra'ila ke ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza.
A karon farko tun bayan da ak yi wa ƙasar juyin mulki a 2021 jagoran dakarun sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya naɗa sabon Firaminista.
Bugu da ƙari har yanzu babu wani cikakken bayanin irin ƙarfin ikon da tsohon jami'in Majalisar Ɗinkin Duniyar, Kamil Idris ke da shi ba a wannan sabon muƙamin da aka naɗa shi, kasancewar har yanzu ƙasar ta Sudan na fama da yaƙin da ta ke yi da dakarun RSF
Da jimawa dai janar Burham na ƙoƙarin kafa sabuwar gwamnatin tun bayan da dakarun gwamnati suka sake ƙwato babban birnin ƙasar Khartoum a watan Maris da ya gabata.
Dakarun na RSF sun kai hare-hare da dama ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa inda suka haifar da tarnaƙi ga lamurran da suka shafi ayukkan gwamnati musamman a manyan biranen ƙasar.
Sannan tun bayan soma yaƙin da aka kwashe fiye da shekaru biyu ana gwabzawa, fadar gwamnatin ƙasar na ci gaba da kasancewa a birnin Port Sudan.
Asalin hoton, Reuters
Nan gaba a yau ake sa ran cewa Vladimir Putin da Donald Trump za su tattauna ta wayar tarho.
Kakakin fadar Kremlin, Dimitry Peskov ya ce ana sa ran batun yiwuwar tsagaita wuta a yaƙin Ukraine zai mamaye tattaunawar shugabannin biyu.
Mista Trump dai ya ce yana fatan tattaunawar za ta yi tasiri inda ya ce daga baya yana sa ran zai yi magana da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
Rasha dai ta ci gaba da kai hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan yankunan Ukraine a karshen mako duk da cewa kasasshen biyu sun gudanar da tattaunawar neman zaman lafiya kai tsaye a karon farko a Istanbul ranar Juma'a.
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon suaban Amurka Joe Biden ya miƙa godiyarsa ga masoyansa da waɗanda suka yi masa fata ta gari bayan an bayyana ya kamu da cutar kansar ƙasan mafitsara.
A wani saƙon da ya wallafa a kafar X, Mista Biden ya ce kamuwa da ya yi da cutar kansar ya shafi kow, inda ya godewa mutane da suka nuna damuwar su da yi masa fatan samun lafiya.
Manyan 'yan jam'iyyar Democracts da Republican sikin su har da wanda ya gaje shi shugaba Donald Trump duka sun yi ma tshon shugaban na Amurka mai shekara tamanin da biyu adu'a.
Bayanan lafiyar shugaban da aka fiyar dai sun ce cutar ta yaɗu zuwa ƙasusuwansa, sa dai likitocinsa sun ce ana ci gaba da duba lafiyarsa.
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar lafiya ta duniyar a ranar Litinin ta buƙaci ƙasashen duniya da su rungumi sabuwar yarjejniyar da ta shafi yaƙi da annobar korona domin kaucewa maimaita abin da aka fuskanta a baya game da cutar.
Membobin hukumar ta WHO na gudana da taron shekara-shekara a helkwatar hukumar da ke birnin Geneva na ƙasar Switzerland.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, " a wannan taro a bana muna fatan membobin hukumar lafya ta duniya za su rungumi wannan sabuwar yarjejeniya".
Ƙasar Amurka dai ta janye a matsayin memba daga hukumar na tsawon shekara ɗaya, matakin da ta ɗauka tun bayan da shugaban ƙasar Donald Trump ya kama aiki.
Wannan yarjejeniya da hukumar lafya ta duniya ta fito da ita na neman tsarin haɗin kai ne tsakanin ƙasashen duniya wanda hakan zai taimaka wajen shirya wa tunkarar kowace annoba mai zuwa tare da gano muhmman ɓangarorin da ya dace a mayar wa hankali musamman wajen samar wa da isar da magungunna da alluran riga-kafi a wuraren da aka samu sake ɓullar annobar .
Kuma a ciki an fito da manufofin samar da daidaito tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da masu tasowa a wurin rabon rigakafin domin kauce wa abin da ya faru a lokacin ɓarkewar annobar COVID-19 a shekarun baya.
'Yan bindigar da suka mamaye garin Sabon Gari a ƙaramar hukumar Ƙaurar Namoda sun kashe aƙalla mutum uku tare da yin garkuwa da 26 da suka haɗa da mata da yara ƙanana.
Maharan da jaridar Daily Trusta ruwaito cewa magoya bayan ɗan bindigar nan ne Bello Ƙaura da aka fi sani da Ɗan Sade, da ake ta'allaƙawa da munanan hare-haren da suka addabi ƙananan hukumomin Ƙaurar Namoda da Maradun.
Rahotannin sun tabbatar da cewa mazauna garuruwan Kungurki da Sabon Gari da Uguwar Sarkin Musulmi da Unguwar Rogo da Yamatsiwa sun tsere daga gidajensu domin gujewa hare-haren 'yan fashin dajin.
A ranar Jumu'a ma wasu 'yan bindiga sun kashe aƙalla mutum huɗu a yankin ciki har da sakataren ƙaramar hukumar Birnin Magaji inda nan ma wasu maharan suka yi garkuwa da ƙarin wasu mutum biyu.
Majalisar dokokin jihar Zamfara dai a baya ta bayana fatan hukumomin sojojin ƙasar su kai wa ƴanfashin hari cikin sansanoninsu da ke dajin Gando da ƴarjiji da Mazaro, kamar yadda a baya a ka kai hari kan sansanonin ƴan bindigar a dazukan Zurmi da Tsafe tare kuma da sanya shingayen binciken jami'an tsaro tun daga Mayinci har zuwa garin Gummi.
Jihar Zamfara dai na sahun gaba cikin jerin jahohin arewa maso yamma da ke fama da harin 'yan bindiga waɗanda kisan jama'a da ƙona amfanin gona tare da garkuwa da mutane.
Asalin hoton, AFP via Getty Images
A karon farko an gurfanar da jagoran 'yan adawar ƙasar Tanzaniya Tundu Lissu a gaban kotu tu lokacin da aka tsare shi bisa tuhumar sa da laifin cin amanar ƙasa a watan jiya.
An dai ga Mista Lissu yana ɗaga hannu ga magoya bayansa inda ya ke sanar da su kada su karaya, yana mai sanar da su cewa, "Babu abin da zai same ku, kada ku karaya."
Akwai dai ƙarin fargaba a babban birnin ƙasar Dar es Salaam a safiyar yau, inda aka girke jami'an tsaro a harabar kotun da aka gurfanar da shi are da wasu sassan ƙasar.
A baya kotun ta yi yunƙurin gudanar da zaman ta kafar majigi, amma shi da tawagar lauyoyinsa suka ƙi amincewa da haka, inda suka nemi a yi kome ƙeƙe-da-ƙeƙe domin abbatar da gaskiya.
An kama jagoran na jam'iyar Chadema a ranar 9 ga watan Afrilun da ya gabata na wannan shekara, bayan ya gudanar da wani gangami mai taken "idan babu sauyi to babu zaɓe", yana mai sanar da magoya bayansa cewa ba za gudanar da manyan zaɓukan watan Oktoba mai zuwa ba mudduin gwamnatin ƙasar ba ta samar da muhimman sauye-sauye a dokokin zaɓen ƙasar ba.
Tun a lokacin ake tsare da shi bisa zargin sa da aikata laifuka masu alaƙa da cin amanar ƙasa, waɗanda ke neman yin tawaye tare da yin zargin jami'an 'yan sanda da aikata laifin murɗa zaɓe.
He denies the charges.
Asalin hoton, NAHCON
Ma'aikaar kula da aikin hajji ta Najeriya ta bayyana cewa an kwashe maniyyata aikin hajji daga jahohi 12 na ƙasar, waɗanda yawansu ya kai mutum 25,702.
Jihohin su ne Osun da Oyo da Adamawa da Filato da Ekiti Imo da Legas da Abiya kuma Edo.
Hukumar alhazan ta ce an kwashe wannan adadin ne bayan sawu 63 daga Najeriya zuwa Saudiyya a cikin kwana goma.
Kawo yanzu dai hukumar ta ce babu wata matsala da aka fuskanta tun bayan soma jigilar maniyyatan, inda a wannan shekarar hukumomin suka ce mutum 43,000 ne za su sauke farali a ƙasar ta Saudiyya domin gudanar da babbar ibadar ta Musulmai.
A ckin wata sanarwa da jami'in gudanarwar hukumar na ƙasa, Ibrahim Muhammad ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa matakan da hukumar ta ɗauka da ke kan tsari sun taimaka matuƙa inda jigilar maniyyatan da sauran ayukan kula da su a ƙasar ta Saudiyya ke tafiya cikin nasara.
An fara jigilar ne a ranar 9 ga wannan watan na Mayun 2025 inda kuma aka soma daga filin jirgin sama na birnin Owerri da ke jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin ƙasar Afirka ta kudu sun ce za su ci gaba da bin matakan shari'a domin tabbatar da an sake gurfanar da limamin kirastan nan mai da'awa ta kafar talabijin Timothy Omotoso wanda a watan da ya wuce wata kotu ta wanke shi daga zargin yin fyaɗe, duk kuwa da cewa ba ya cikin ƙasar a yanzu.
Mista Omotoso dai ya musanta zarge-zarge har 32 da aka yi masa ciki kuwa har da cin zarafin wata matashiya ta hanyar lalata, a wata mujami'arsa da ke birnin Port Elizabeth.
Hukumar da ta shigar da ƙara a Afirka ta kudun (NPA) ta sha alwashin ɗaukaka ƙarar, inda ta ce ko da Mista Omotoso ba ya cikin ƙasar hakan ba zai hana ɗaukar matakin ba.
Hakazalika, idan har ta samu wannan nasara, gwanatin ƙasar za ta nemi Najeriya ta mayar da Mista Omotosho ƙasar domin fuskantar hukuncin, kasancewar ƙasashen biyu na da kyakkyawar hulɗar diflomasiya tsakanin su.
Bayan da wata kotu ƙasar ta wanke shi daga zarge-zargen a watan Afrilun da ya gabata, limamin kiristan na kuma fuskantar ƙarin tuhuma bisa dalilan shiga ƙasar ba tare da izini ba, kasancewar an dakatar da shi daga shiga Afirka ta kudu har na sawon shekara biyar.
Timothy Omotoso dai na jagorantar mujami'ar Jesus Dominion ta duniya wadda ke da rassa a ƙasashen Birtaniya da Najeriya da Faransa da Isra'ila da kuma Afirka ta kudu.
Hukumar da ke bayar da agajin magungunna ga Falasɗinawa ta ƙasar Birtaniya ta ce Isra'ila ta kai wani hari da ya afkawa rumbun ajiyar magungunna na Asibitin Nasser da ke yankin Khan Younis a tsakar daren da ya gabata a kudancin Gaza .
Hukumar ta ce harin ya auku ne "lokacin da ake kwashe Falasɗinawan da aka kashe da waɗanda aka jikkata zuwa asibiti, bayan wasu jerin hare-haren da Isra'ila ke kai".
Daga cikin magungunnan da harin ya lalata sun haɗa da waɗanda hukumar ta samar wa asibitin na Nasser. "A yanzu dai muna kallo dukan magungunna da muka bayar tallafi sun ƙone ƙurmus" in ji kakakin hukumar.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da hotunan wuraren da harin ya shafa. Kafar yaɗa labaran Falasɗinawa ta bayar da rahoannin cewa hare-haren da aka kai a birnin sun yi sanadiyyar mutuwar gomman mutane.
Rundunar sojojin saman Isra'ila ta fitar da wata sanarwa cewa a cikin kwana guda kaɗai ta kai hare-hare har 160 a wurare daban-daban da ta ke hara.