Mutum huɗu sun mutu bayan hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Turkiyya
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza da Awwal Janyau
Mutumin da ya yi tafiyar kilomita 13,000 a ƙafa don yaƙi da wariyar launin fata
Asalin hoton, Twitter
Wani ɗan asalin ƙasar Uganda mazauni London ya kammala tafiyar sama da kilomita 13,000 a ƙafa domin nuna adawa da wariyar launin fata.
Deo Kato ya yi gudu ko tafiya daga Cape Town a Afrika ta Kudu zuwa London.
Ya kaucewa bin wasu hanyoyi inda dole sai da ya ratsa ta teku domin kaucewa yaƙi a Sudan.
A kan hanyarsa ya ci karo wariyar launin fata a Turai. Deo ya shaida wa BBC cewa yana son tattara tarihin masu yin ƙaura daga Afrika domin nuna cewa duka wuri ɗaya ne tushenmu.
Shugaban Syria ya ce za su karɓe ikon makaman ƙasar
Sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa, ya ce za a sanya ido a kan dukan makaman da ke ƙasar, ciki har da waɗanda ke hannun mayaƙan Kurdawa.
Bai bayyana hanyoyin da za a bi wajen cimma nasarar hakan ba, amma ya ce nan ba da jimawa ba za a rusa dukkan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, da kuma kafa sabuwar rundunar sojin Syria.
Ya ce ba za mu taɓa barin makamai a hannun wasu da ba dakarun gwamnati ba.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki domin bayar da kariya ga tsiraru marasa rinjaye, kuma za ta mayar da Syria ƙasa ta kowa da kowa, ba tare da la'akari da ƙabila ko addini ba.
Isra'ila ta kai hari a makaranta da mutane suka fake a Gaza
Asalin hoton, EPA
Hukumomi a Gaza sun ce sabbin hare-haren Isra'ila sun faɗa kan wata makaranta da mutane ke fakewa a ciki, da kuma wani asibiti a arewaci.
Sun ce mutane 28 aka kashe, ciki har da ƙananan yara.
Dakarun Isra'ila sun ce mayaƙan Hamas na amfani da makarantar wajen gudanar da ayyukan su.
Jami'ar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Juliette Touma ta shaidawa BBC cewa akwai buƙatar duniya ta tashi tsaye don kawo ƙarshen luguden wutar da Isra'ila ke yi a yankin.
Ta ce babu wanda ya kamata ya yi shiru a kan waɗannan hare-hare saboda abin tashin hankali ne kuma sun saɓawa dokar ƙasa da ƙasa.
Sojojin Najeriya sun kama ƴantawayen Ambazonia a Taraba
Asalin hoton, @HQNigerianArmy
Troops of the 6 Brigade, Nigerian Army/Sector 3, Operation Whirl Stroke (OPWS), have arrested four of the Ambazonian rebel group from the Republic of Cameroon in Taraba State.
Rundunar sojin Najeriya ta shida ta kama wasu da take zargi ƴantawayen Ambazonia ne masu fafutikar ɓallewa daga Kamaru.
Rundunar ta ce ta kama ƴantawayen guda hudu a yankin Takun na jihar Taraba.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce mutanen sun amsa cewa fataucin makamai zuwa Najeriya.
Rundunar ta ce tana tsare da su kuma tana gudanar da bincike.
Gwamnatin tarayya ta ɗage haramcin haƙar ma'adinai a Zamfara
Gwamnatin Najeriya ta ɗage haramcin haƙar ma'adinai a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Sanarwar da ma'aikatar ma'adinan ƙasa ta fitar ta ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan nazari kan yanayin tsaro a sassan jihar mai arzikin zinari.
Sanarwar ta ce ta ce shugaban ƙasa da mai ba shi shawara kan sha'anin tsaro suka bayar da umarnin ɗage haramcin. Hakan na nufin masu haƙar zinari a jihar za su ci gaba da aikinsu.
Tun a 2019 gwamnatin shugaba Buhari ta sanar da haramta hakar ma'adinai a Zamfara saboda dalilai na tsaro.
An daɗe ana alaƙanta harakar haƙar zinari a Zamfara da matsalar ƴanbindiga da suka addabi jihar.
Gwamnatin Najeriya ta taɓa saka haramcin shawagin jirage a yankin Zamfara saboda matsalar ƴanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa.
Sai dai rahotanni daga Zamfara sun ce haramcin bai hana ci gaba da haƙar zinari ba.
NDLEA ta kama ɗankasuwar da ke fataucin hodar iblis a Kano
Asalin hoton, NDLEA
Hukumar NDLEA mai yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ce ta kama wani ɗankasuwa mai suna Olisaka Chibuzo da ke ƙoƙarin fataucin hodar iblis a filin saukar jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Hukumar ta ce ta kama mutumin ɗauke da horar iblis da dunkulenta ya kai 256 kuma nauyinta ya kai kilo shida.
An kama mutumin ne bayan binciken jikinsa a lokacin da ya sauka daga jirgin Ethiopia a Kano wanda ya fito daga birnin Abidjan.
Mace ta farko da ta tuƙa jirgin sama a Iran ta ɗauki fasinjoji mata fiye da 100
Wani jirgi ɗauke da mata zalla ya sauka a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, ɗaya daga cikin manyan ƙasashen mabiya shia a duniya.
Direbar jirgin mai suna Shahrzad Shams, ta kasance mace ta farko da ta tuƙa jirgin sama a tarihin ƙasar, inda ta ɗauki fasinjoji fiye da 100 mata da kafofin yaɗa labaran ƙasar suka bayyana a matsayin fitattun mata.
Tawagar matan na kan hanyarsu ta zuwa wurin bauta na Imam Reza.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar ba su bayyana wanda ya ɗauki nauyin bulaguron ba ko daga inda jirgin matan ya tashi.
'Yansanda sun musanta rahoton Amnesty kan zargin muzguna wa masu zanga-zanga
Asalin hoton, Nigeria Police/X
Rundunar sojin Najeriya ta musanta zarge-zargen da ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International Amnesty ta yi mata kan muzgunawa masu zanga-zangar tsadar rayuwa.
'Yansanda sun bayyana zarge-zargen da cewa ƙarairayi ne marasa tushe da ke ƙoƙarin ɓata wa rundurar suna.
Cikin rahoton da ƙungiyar Amnesty International ta fitar ranar, 28 ga watan Nuwamba ya zargi 'yansandan da kisan fararen hula masu zanga-zanga, tana mai cewa 'yansanda sun kashe mutum 24 a jihohin shida da ke arewacin ƙasar.
To sai dai 'yansandan sun ce abin da bincikensu ya gano ya saɓa da rahoton na Amnesty International.
Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi, kakakin rundunar 'yansandan, Muyiwa Adejobi ya ce tun bayan rahoton na Amnesty rundunar 'yansandan ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike.
Ya ƙara da cewa, kwamitin tare da haɗin gwiwa kwamishinonin 'yansanda daga jihohin da alamarin ya shafa sun gudanar da zuzzurfan bincike kan rahoton, inda ya gano kura-kurai a zarge-zargen da Amnesty ya yi.
RSF ta sake ƙwace iko da sansanin soji sa'o'i bayan karɓe shi daga hannunta
Asalin hoton, AFP
Rahotonni daga Sudan na cewa dakarun RSF sun sake ƙwace iko da wani muhimmin sansanin soji da ke jihar North Dafur, sa'o'i bayan mayaƙan wata ƙungiya da ke mara wa sojojin gwamnati bayan sun ƙwace shi a ranar Asabar.
Sansanin - wanda ke ƙauyen Al-Zurq da ke kusa da kan iyakar Sudan da Chadi da kuma Libya - shi ne babban sansanin da RSF ta fi ƙarfi a jihar ta North Darfur.
A baya sojojin Sudan sun taɓa kai masa hari, bayan da suka zargi ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kai wa mayaƙan RSF makamai a sansanin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum 700 aka kashe a tsawon lokacin da RSF ta shafe tana yi wa El-Fasher, babban binin jihar North Darfur ƙawanya.
Putin ya sha alwashin ƙara ruguza Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya sha alwashin ƙara ruguza Ukraine a wani mataki na mayar da martani kan harin jirgi maras matuƙi da aka kai birnin Kazan da ke tsakiyar Rasha.
Yayin da yake jawabi a ganawa da gwamnatinsa da aka yaɗa a talbijin, Mista Putin ya zargi Ukriane da ƙaddamar da hare-haren jirgi maras matuƙi, waɗanda suka faɗa kan wani ginin alfarma a birnin ranar Asabar.
Ya gargaɗi Ukraine da abin da ya kira ''ɗanɗana kuɗarta'' ta hanyar manyan hare-hare da ɓarna mai yawa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Rasha suka ce sojojinta sun ƙwace wani ƙauye da ke kusa da garin Kurakhove inda ake fafatawa a gabashin Ukraine, kodayake Ukraien ba ta ce komai ba kan iƙirarin.
Dangote zai haɗa kai da kamfanin MRS don sayar da litar fetur naira 935
Asalin hoton, Getty Images
Matatar mai ta Dangote a Najeriya ta ce za ta haɗa hannu da kamfanin mai na MRS domin sayar da litar man fetur a kan kuɗi naira 935 a gidajen mansa da ke faɗin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da kamfanin Dangoten ya fitar ranar Asabar, ya ce shugaban kamfanin Aliko Dangote ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Tinbu kan matakin da ya ɗauka na sayar wa matatarsa ɗanyen mai da kuɗin naira, wanda ya ce ya yi tasiri kan tattalin arzikin ƙasar.
Dangote ya ce hakan ya kuma taimaka wajen samun raguwar kuɗin man fetur a cikin ƙasar.
“Domin kawo wa 'yan Najeriya sauƙi, a baya Dangote ya rage farashin mai daga 970 zuwa 899.50 ga masu sarin man a matatarsa, kuma domin tabbatar da ragin ya isa kan masu amfani da man, mun cimma yarjejeniya da kamfanin MRS domin sayar da man kan naira 935 a gidanjen mansa,'' kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Matakin na zuwa ne bayan da babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya sanar da rage farashin man zuwa ƙasa da naira 1,000.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
A cikin shirin namu na wannan mako mun kawo muku tarihin tsohon ma'aikacinmu, Elhadji Diori Coulibaly wanda ya shafe shekara shekara 25 yana aiki da sashen Hausa na BBC.
Mun kuma amsa tabbaya game da tarihin Masarautar Borno da arewa maso gabashn Najeriya.
Haka kuma a cikin shirin - wanda Abdou Halilou ya gabatar - ya kuma binciko muku bayanan wata cutar dabbobi da ke kama mutane.
An kama wasu bokaye bisa zargin asirce shugaban ƙasar Zambiya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An zaɓi Hakainde Hichilema a matsayin shugaban Zambia a 2021
Hukumomin Zambiya sun kama wasu mutum biyu da ake zargi ''matsafa'' ne da aka bai wa aikin asirce shugaban ƙasar.
'Yansanda sun ce sun kama Jasten Mabulesse Candunde da Leonard Phiri a Lusaka, babban birnin ƙasar.
"Aikin da suka ƙudiri aniyar yi shi ne amfani da layu wajen cutar da shugaba Hakainde Hichilema'', kamar yadda sanarwar 'yansandan ta bayyana.
Mutane da dama a ƙasar da ke kudancin Afirka sun yi amanna da bokaye, inda a lokuta da dama mutane kan rayu da fargabar tsoron asiri.
'Yansanda sun yi zargin cewa Nelson Banda - ƙanin wani ɗan majalisa Emmanuel Banda, da aka fi sani da "Jay Jay" Banda - ne ya bai wa bokayen aikin sabauta shugaban ƙasar.
A watan da ya gabata ne aka kama ɗan majalisar a makwabciyar ƙasar Zimbabwe kan zargin laifin fashi, zargin da ya musanta.
Sanarwar 'yansanda ta ce wanda ake zargi da bai wa bokayen aikin ya tsere, inda suka alƙawarta farauto shi.
An dai kama bokayen ƙarƙashin dokokin tsafi na ƙasar, inda ake zarginsu da aikata tsafi da zaluntar dabbobin, bayan da ka same su da tarin guraye da layu da kuma hawainiya da ranta, kamar yadda 'yansanda suka yi bayani.
Bokayen sun kuma bayyana wa 'yansanda cewa an yi musu alƙawarin kuɗin ƙasar fiye da kwaca miliyan biyu kimanin dala 73,000, idan suka kammala aikin sabauta shugaban ƙasar.
Mutum huɗu sun mutu bayan hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Turkiyya
Asalin hoton, Getty Images
Mutum huɗu sun mutu bayan hatsarin wani jirgin ɗaukar marasa lafiya mai saukar ungulu kudu maso yammcin Turkiyya.
Ma'aikata lafiyar ƙasar ta ce jirgin ya tashi ne daga asibitin horaswa da bincike, inda kuma ya ci karo da wani gini kafin ya faɗo ƙasa.
Ba a samu rahoton rasa rai daga cikin ginin da jirgin ya yi karo da shi ba.
Tuni dai aka ƙaddamar da bincike domin gano musabbain faruwar hatsarin jirgin, wanda rahotonni suka ce ya tashi a tsakiyar hazo.
Hikayata: Labarin Magaribar Jaki
Bayan kammala kawo muku labarai ukun farko da suka yi nasara a gasar Hikayata ta 2024 da BBC Hausa ta shirya, a yanzu kuma za mu fara kawo muku labarai 12 da alƙalan gasar suka ce sun cancanci yabo.
Kuma a yaun mun fara ne da labarin Magaribar Jaki, wanda Safiyya Mukhtar Garba daga jihar Kano ta rubuta, kuma Rabi'atu Kabir Runka ta karanta.
Marubuciyar ta gina labarin Magaribar Jaki ne kan wata budurwa da ta bijire wa umarnin iyayenta, ta kuma biye wa makauniyar soyayyar da take yi wa saurayinta, inda shi kuma daga ƙarshe ya kai ta ya kuma baro ta.
Yarinyar mai suna Ramatun Nabuta a cikin labarin ta bar gidan iyayenta ta bi saurayinta zuwa Legas, ƙarshe saurayin ya mutu a can ya barta, ita kuma ta faɗa bariki, daga ƙarshe kuma ta yi fargar jaji bayan da lokaci ya ƙure mata.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron labarin
'Yansandan Indiya sun kama fiye da mutum 400 saboda halartar auren ƙananan yara
Asalin hoton, Getty Images
'Yansandan Indiya sun kama fiye da mutum 400 bayan sun kai samame kan wani bikin haramtaccen auren ƙananan yara a jihar Assam da ke ƙasar
Babban ministan jihar, Himanta Biswa Sarma, ya ce za a gurfanar da mutanen yau a gaban kotu, sannan ya ce hukumomin jihar za su ci gaba da yaƙi kan abin da ya kira 'gurɓata tarbiya'.
Ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa ne kan alƙawarin kawo ƙarshen auren ƙananna yara a jihar Assam nan da shekarar 2026.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Indiya na da ƙananan yara amare fiye da miliyan 200, kodayake adadin na raguwa a shekarun baya-bayan nan.
Adadin mutanen da suka mutu a turmutsutsun Abuja da Anambara ya kai 32
Asalin hoton, FCT Police
Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce mutum 22 ne suka mutu a turmutsutsun da ya faru a garin Okija na jihar Anambara da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, lokacin da wata gidauniya ke rabon tallafin abincin bukukuwan Kirsimeti da suka haɗa da shinkafa da man girki ga masu ƙaramin ƙarfi a yankin.
Haka ma a Abuja baban birin ƙasar mutum 10 ne suka mutu sakamakon makamancin wannan bala'i a ranar ta Asabar a wani coci da ke unguwar Maitama a tsakiyar birnin.
Waɗannan bala'o'i na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wasu ƙananan yara 35 sun mutu a wani turmutsutsun a wajen wani biki a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Rundunar 'yansan ƙasar ta kuma gargaɗi duka masu shirya rabon tallafin da su sanar da ita kafin aiwatar da rabon, domin kare aukuwar irin hakan a nan gaba.
Tuni dai shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu.
Likitoci a wani asibitin arewacin Gaza na neman ɗauki bayan harin Isra'ila
Jami'an kiwon lafiya a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza sun yi kiran kai musu ɗauki, bayan da suka zargi sojojin Isra'ila da nananata hari kan asibitin.
Wani likita guda da majinya takwas ne ke cikin hatsari.
Idsar'ila dai ta bayar vda umarnin ɗauke asibitin daga yankin, lamarin da ya janyo suka daga hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, wadda ta bayyana umarnin a matsayin ''abin damuwa''.
A wani labarin kuma, wasu hare-hare ta sama da Isra'ilar ta kai tsakiyar Gaza a ranar Asabar ya kashe aƙalla Falasɗinawa 10 a sansanin 'yangudun hijira na Nuseirat da kuma a birnin Deir Al-Balah.
An tsare ɗan ƙasar Saudiyya kan zargin harin kasuwar Kirsimeti
Asalin hoton, Getty Images
Wani alƙali a birnin Magdeburg na ƙasar Jamus ya bayar da umarnin tsare wani ɗan ƙasar Saudiyyan da aka kama bisa zargin kai mummunan hari kan wata kasuwar Kirsimeti a birnin.
An gabatar da mutumin mai shekara 50 a gaban alƙali da maraicen ranar Asabar, bisa zargin tuƙo mota tare da kutsawa cikin kasuwar mai cike da cunkoson jama'a.
A wani taron manema labarai, mai gabatar da ƙara a birnin na Magdeburg, Horst Walter Nopens ya ce maharin shi kaɗai ya kitsa ya kuma kai harin.
Ya ce saɓanin rahotannin da ke ta yawo a shafukan sada zumunta a jiya, mai laifin mutum guda ne, kuma babu alamun akwai wani da ke aiki tare da shi.
Aƙalla mutum biyar ne suka mutu, da suka haɗa da mata uku da wani yaro mai shekara tara, yayin da sama da 200 suka jikkata a harin da aka kai da yammacin ranar Juma'a
Maraba lale
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarashen mako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Haka kuma kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.