Lauyoyi sun buƙaci a hukunta wanda ake zargi da ya yi wa ƴar shekara 9 fyaɗe a Jigawa

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya wasu ƙungiyoyin lauyoyi da masu kare haƙƙin dan-adam sun yi kira da a kama tare da hukunta wanda ake zargi da hannu a yi wa wata ƙaramar yarinya ƴar shekara 9 fyaɗe a jihar Jigawa.
A yanzu haka ana ci gaba da jinyar yarinyar a asibiti sakamakon munanan raunukan da aka ji mata.
Barista Aisha Ali Tijjani, lauya ce mai zaman kanta malama a kwalejin nazarin aikin shari’a ta Aminu Kano da ke jihar Kano, ta yi wa BBC ƙarin bayani kan yadda suke kallon wannan batu ta fuskar shari’a, inda ta ce za su bi kadin lamari.